BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Mutumin direct asibiti yakai Bariki, itama din de emergency aka kaita, nan aka fara bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah numfashinta ya daidaita, bata ko 30mnt ba ta farka tare da fara bud’e idonta, ganinta a kwance yasa ta gane a asibiti take, gefenta ta kalla da sauri ta tashi domin ganin Yarima Aliyu a kwance, tsige Abun drive din da aka saka mata tayi, jini ya fara zuba da sauri tasa hannunta ta toshe, tare da nufa wajan da Yarima Aliyu yake kwance rai a hannun Allah, da sauri ta ri’ke Mai hannu tana kuka tare da fad’in Yarima maiya sameka? Kuka take Sosai cikin tashin hankali, Yarima Aliyu dake kwance lokaci d’aya ya fara numfashi da karfi alaman numfashin shi yana son dai daituwa, ta dad’e a ri’ke da hannunshi tana kuka kanta na k’asa,

Ji tayi yasa hannunshi akanta, Tsagaitawa tayi da kukan, domin tana son ta tabbatar shi dinne yasa mata hannu akai, lokaci d’aya ta d’ago dakai a hankali, cikin mamaki taga yana sakar mata murmushi, itama murmushin ta sakar mishi tare da rungumeshi tana kuka, Tana fad’in Yarima maiya sameka? Bai bata amsa ba, sannan bata damu ba ita tunda taga ya farka hakan yafi mata komai, tana kwance jikinshi abunda ya faru ya fara dawo mata, yanzu ita ba Matar Yarima bace?

Da sauri ta tashi daka kan jikinshi tana hawaye Mai zafi, idon Yarima na kanta yana mamakin irin Tashin da tayi cikin razana tare dayin baya dashi, gaba d’aya ya kasa magana, domin bakinshi yayi mishi nauyi yana son yi mata magana ya kasa, sai hannunshi da yake mi’ka mata alaman tazo, ga jinin daya gani a hannunta yana zuba, duk da shima ta bata shi da jinin, Bariki kam ganin yana mi’ka mata hannu alaman tazo yasa ta Fara fad’in Yarima kayi hakuri na haramta a gareka, Yarima Nasan bazan iya juran rasaka ba, Yarima Ina ro’kan ka dan Allah kaima ka tashi kaci gaba da rayuwa kaman kowa, Yarima Sonka a jini na yake, amma an yake duk wata jijiya da zai had’ani dakai, na tabbata Yarima Sonka shine ajali bar, amma ya zanyi kaddara ta riga fata, Yarima Indai dagaske kana sona ka tashi daka wannan yanayin da kake ka koma kaman da, Nasan Yarima namiji ne mai cikar lafiya, namiji ne mai kwazo, karka bari wannan ciwon y….. Kuka yaci karfinta lokaci d’aya kuma tace Yarima ka yarda dani a matsayin kaddara lokacin da kasan koni wacece, yanzu Ina son ka yarda da rabuwa na dakai shima a matsayin kaddara S…. Kuka take Sosai ga Yarima dake kwance hawaye na zubar mai hannunshi yana tsaye yana kiranta tazo amma ta’ki,gashi ya kasa magana.

Bariki da sauri tabar d’akin ganin fadawa a waje damai martaba yasa ta dawo da sauri, tare da hawa window ta dirka….. Tana dirka cikinta ya murd’a mata alaman ciwo.

Yarima kam gaba d’aya kasa tashi yayi domin jin kafarshi yake kaman an d’aureshi da igiya, sai hawayen takaici yake, yana son magana da Zainab ya kasa lai. … Shigowan Dr ne yasa Yarima Aliyu kallon kofar Dr ne da mutumin daya kawo Zainab din, Dr yace Ina tayi kuma??

Mutumin yace ikon Allah, nan Dr yace May be ta farka ne ta tashi ta nufeta, ganin jikin Yarima da jini, itama gadon da take da jini yasa Dr saurin ‘karasawa wajan Yarima, lokaci d’aya kuma ya saki murmushi Dr din ganin oxygen din yana tafiya dai dai alaman numfashin Yarima ya koma dai dai, duk da idon Yarima a lumshe yake,

Dr Ya kalli mutumin daya kawo Bariki, yace lallai ka tabbatar ka nemota, domin tana bukatar bed rest, cikinta sati uku da kwanaki, in bata huta ba zai iya zubewa gaskiya.

Mutumin yace Dr nima a hanya naga ta fad’i n…..

Yarima Aliyu da tunda yaji ance ciki Zainab take dashi ya bud’e ido, lokaci d’aya wani karfi yazo mishi, jinshi sukayi yana fad’in Dr kana nufin Zainab Tana da ciki??

Su duka suka bishi da ido alaman mamaki, tashi Yarima Aliyu yayi zaune, yace Dr she is my wife plz tell me is she pregnant??..

Dr yace yes she is pregnant, but where is she??

Yarima Aliyu cire oxygen din dake hanncinshi yayi tare da tsige Abun drive din dake hannunshi, da sauri Dr yace Aliyu ka tsaya, da sauri Dr din ya nufeshi tare da ri’ke Mai hannun dake zubar da jini, Yarima Aliyu yace Dr leave me I will handle it, am a Dr too..

Dr yace I know but plz ka tsaya kasan yanayin da kake ciki, bai kamata ka fita haka ba, u need to rest

Yarima Aliyu yace how will I sit hare and rest matata da unborn child d’ina suna cikin had’ari bayan kace cikin zai iya fita, I have to go and find her.

Babu yanda Dr ya iya dole yabar Yarima ya fita, inda yana fita yaga mai martaba da mum da fadawa.

Mum ganin d’an nata ya fito yasa ta saki wani murmushi Tare da furta Alhmdlh, nufanshi tayi tare da rungumeshi tana kuka, mai martaba shima tashi yayi yana fad’in Aliyu ya jikin naka, amsawa yayi da Alhmdlh Abba, mum sakinshi tayi tana fad’in ya jikin naka ya amsa da Alhmdlh mum, tare dayin gaba da sauri.

Mum damai martaba binshi sukayi da ido, ganin Dr yasa suka nufeshi suna fad’in ina zashi, nan Dr Ya fara basu Labarin Yarinyar da aka shigar da ita d’azu matarshi ce, and tana da ciki Yadai basu Labarin komai, tare da fad’in abunda na Lura is lyk kaman itace wacce lokacin da yayi irin wannan tayi mishi magana ya tashi koh??

Mai martaba yace eh Dr itace, nan Dr yace gskiya yana mata son so, dukansu bazasu iya rayuwa babu dayansu ba, dan haka ku tabbata Yarima duk inda zashi ko ince kar’ayi abunda zasu rabu da juna, ban taba ganin irin wannan son ba sai a Fina finai ko a littafai, ashe yana faruwa da gaske, duk da Muma a karatun mu anyi mana wajan, but ban taba d’aukan abun serious ba dan Banyi tunanin zai faru ba, sai gashi na gani yanzu, and shawaran da zan k’ara baku shine ku tayashi dubata, domin Indai bai ganta ba gaskiya I don’t know wat will happen, nan Mai martaba yace mun gode Dr, Dr yace babu komai ganin matar tashi shine lafiyanshi.

Mum kam gaba d’aya duk abunda Dr yake fad’a babu wanda ya shiga kunnenta, ita tunda d’anta ya tashi Alhmdlh, sannan maganan a nemo matarshi bai taso ba, tunda ya Mata saki uku, and kuma cikin dake gareta ta tabbata bana d’anta bane, sai dai in wani ya Mata ciki y’an iskan samarint…. Mai martaba ya Katseta da fad’in Kinga ikon Allah koh? Kina tunanin kin rabasu amma Akwai ajiyar jikanki a jikinta, Kinga har yanzu ala’ka bai ‘kareba tsakaninsu, Idan babu ala’kan aure Akwai na abunda zata haifa, lallai ki godema Allah da yasa sai da akayi auren kika san ko wacece, domin na tabbata inda kin San ko wacece b4 suyi auren Nasan bazaki amince ba, not even you Nima da kaina bazan amince ba, Kinga Ashe Akwai rabon wannan cikin, kuma rabo na kisa, and inma baiyi kisa ba za’a kawo mana jika babu aure shi kuma wannan sai muce me??

Duk abunda kikaga Allah yayi, karkiyi jayayya akan abun, yanzu kina murna kin raba d’anki da matar da kike kira karuwa, gashi a karo na biyu ta k’ara taimaka mishi, lallai Khadija keda kanki kike son kashe d’anki, yanda d’anki yake Sonta itama take sonshi in bakiyi wasa ba za kiji suna zaman dadiro ko kiji yasa tayi auren kissan wuta, daka k’in gaskiya sai bata yana fad’in haka ya tafi ya barta domin yaga wani hali d’an nashi ke ciki

Hmmm Tashin hankali mum duk maganan da mijinta ya fad’a mata, babu wanda ta d’auka domin idonta ya rufe, lallai Asirin bariki yayi tasiri har akan mijinta, domin gaba d’aya taga baya ganin laifin kowa sai Nata, wacce take ganin abunda tayi shine dai dai, lallai dole ta nemi maganin karya sihiri taba d’anta da mijinta, itama binsu tayi domin taja d’anta suyi gida, dan tasa a Fara mishi addu’a,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button