BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Yarima Aliyu tafiya yake cikin haraban asibitin jiki babu kwari sai waige waige yake, kallo d’aya zaka mishi kasan yana cikin Tashin hankali tare dajin zafin ciwo, gaba d’aya cikin asibitin baiga mai kama da Zainab ba, dan haka ya fita waje, nan mutane suka fara tareshi ana fad’in Yarima Aliyu, mai jiran gado, gaba d’aya mutane sun hanashi yin gaba suna k’okarin gaisawa dashi, ganin haka fadawan dake binshi a baya suka zo suka fitar dashi suka sashi a mota, koda Mai martaba ya fito ganin abunda ke faruwa shima motar ya shiga yace su nufi Gida, Yarima idonshi nakan titi ko zaiga Zainab amma baiga koda Mai kama da ita ba, haka har suka k’arasa gida, Yarima Aliyu hannunshi ri’ke dana Mai martaba suka shiga gefen mahaifin nashi, suna shiga Yarima ya fad’a kan kujeran falon ya fara hawaye tare da ri’ke kirjinshi dake faman mishi zugi da rad’adi, ganin haka Mai martaba ya fita tare da kiran waziri akan suje su duba gidan iyayen yarinyar na k’arya may be tana can, nan su waziri suka amsa da angama ranka ya dad’e suka tafi.

Bariki kam tunda ta fita daka asibitin cikinta na Mata ciwo Sosai, samun wani waje tayi akwai rumfa ta kwanta, domin babu komai a hannunta, harta wayarta bata hannunta, gashi yanzu babu bank sun tashi da taje ta cira kud’i ta check book, haka ta kwanta a wajan domin ciwon cikin yana damunta Sosai, ita bata ma San tana da ciki ba, Hmmm Bariki babu riba, lallai rayuwar mace kalilan ce, zakiyi iskanci lokaci kad’an kiyi sanyi a daina yi dake, in kinso shiriya mutane su dinga nuna miki kyama da hantara, tare da goranta miki, inma kin samu mijin aure kin haiyu aita miki gori ana ma y’ay’anki gori, daka fad’a ya had’asu da wani aita musu gori, y’ar uwa Mai yafi wannan ciwo da zafi? Gashi kullum in kika fita miji yaita zargin ki, kai Wlh Mata iskanci da fitsari bashi bane wayewa, babu abunda yakai kame Kai da tsare mutunci dad’i, Idan ke ta’kamarki bin maza kina bud’e musu k’afa suyi lalata dake, daka ranan da kikace d’aya daka cikinsu ya fito ya aureki, zaki ga yace shi dan iska ne da zai aureki? Bayan kin gama bin maza ai inada kishin kaina, daka ranan ma in bakiyi wasa ba yabar kulaki, mai wayau kuma zaiyi ta miki Karya tare da alkawarin zai aureki, inya gama cin moriyarki ya gudu, ke koda shine ya fara saninki kuma shi d’aya kike bi, wlh bazai iya auranki ba, domin shifa a kullum tunani yake kina bin wasu mazan, zaki ce ai maza nawa sukayi lalata da Mata suka auresu Toh Bari kiji Wlh Mata da yawa y’an duniya wanda suka amsa sunansu y’an Bariki, akwai namijin da suke nunamawa su ustazai ne basu taba sanin namiji ba, daka anyi aure yaji kofar a bud’e take sai kuji ya saketa, aure kuga ko sati baiyi ba Ya mutu, wasu kuma asiri suke ma mazan su auresu, Hmmm kuma duk abunda aka had’a da asiri baya ‘karko domin asiri dai yana karyewa daka ranan daya karye ranan zaki gane shayi ruwa ne, y’ar uwa komai zakiyi ki yishi akan gaskiya, da yawa zaki ga y’an duniya suna hulda da malamai, amma daka karshe ya rayuwarsu take k’arewa? Idan har kin San miye rayuwa kuma kina nazari kina kallon abunda ke faruwa, wlh zaki ji tsoran duniya da rayuwa kiga ba komai bace, yanzu maza yawancin su babu abunda suka iya sai soyayyar shan minti, daka sunje wajan Yarinya zasu Fara mata maganan banza da rashin kunya, daka nan sai a fara tabe tabe, wani ma so yake ya aureki, amma yana gwadaki daka ya taba yaga kin biye mishi, sai yace y’ar hannu ce shida yazo da niyan aure sai ya nemi kwanciya dake daka kin bashi ya gudu, ke kina ganin hakan shine wayewa, lol

Wlh mata ku kiyaye, sai yasa yanzu y’an mata sukai yawa, babu mazajan aure, domin mazan suna mana kallo a d’age, suna ganin kaman duka d’aya muke, yau Idan namiji yazo Wajanki yayi k’okarin tabaki kika rufe ido kika ci mishi mutunci kika tafi kika barshi, wlh Indai aurenki zaiyi gobe zai dawo, domin zaice kinci jarabawan shi, amma daka ya tabaki saiki bada Kai bori yahau, kai Wlh Mata masu irin wannan halin aji tsoran Allah, domin duk iskancin namiji so yake ya auri nitsatsa ba ballagaza ba, wacce kowa ya Santa, Allah ya kyauta.

Koda su waziri suka isa gidan iyayen Bariki na k’arya, mamanta tace ai tunda tayi aure bata zoba.

Koda su waziri suka koma suka fad’ama sarki, Yarima babu abunda yake sai kukan zuci, domin yanzu hawayen dake fuskanshi Ya’ki fita, saboda yana cikin Tashin hankali da damuwa, fiye da tunanin mai karatu, Yarima Aliyu yasan rashin matarshi kaman barazana ne ga rayuwanshi, gashi ba ita d’aya ba, tana d’auke da cikin shi, lallai Mum ta gama dashi da tasa ya saki matarshi, inda tasan irin son da yake mata da bata ce ya saketa ba, mai yasa mutane basa d’aukan kaddara Indai ba’a kansu ya fad’a ba?? Mai yasa mutane basa ma wasu uzuri Indai basu bane suka aikata?? Mai yasa duk abunda ba damuwarka bane mutane basa d’auka da muhimmanci?? Shin Mum tasan zan iya rasa raina akan Zainab tayi k’okarin rabani da ita? Shin tasan Sonta a jini na yake? Lallai Indai banga Zainab ba komai zai iya faruwa domin yanzu dauriya kawai nake, Yarima Aliyu lokaci d’aya ya fara girgiza kai domin tunawa da yayi Karta koma irin rayuwarta ta da, tashi yayi da sauri.

Mai martaba yace Aliyu Ina zaka?

Yace Abba neman Zainab, zani in dubata, Abba Ina tsoran ta nanata irin rayuwar da tayi baya, Abba ban son ta k’ara bata rayuwarta S….

Mai martaba yace Aliyu zoka zauna, nasa a nemota, Aliyu zama yyi tare da fad’in Abba Kirjina tare da ri’ke wajan ya kasa magana, da sauri mai martaba yayi kansa….


Habib ne zaune gaban hjy Umaima yana fad’in, na samu Labarin Yarima ya saki bariki, dama sai yasa na fad’a miki iyayenshi basu sani ba, gwara da kika turama uwarshi, Kinga yanzu aiya saketa,

Hjy Umaima dariya tayi cikin jin dad’i tare da fad’in yanzu sai a nemo min ita

Habib yace hjy aiki kwantar da hankalinki ita da kanta zata kawo kanta, tunda Yarima ya saketa ai dole ta dawo gidan jiya, dama saboda shi ta shiryu, yanzu Kinga tunda ya korota ai dole a dawo gidan jiya, ko dan a sami na rufin asiri.

Hjy Umaima tace hakane yanzu abunda ya kamata shine, ka koma kaduna nasan for sure zata koma gidan barikin da take tana zuwa call me, Zanzo kaduna din.

Habib yace an gama, ai hjy Wlh bariki komai kika ce mata yanzu zata yarda domin bata da wani zabi, saina abunda kikace, tunda komai ya cabe Mata, yace hjy inada y’ar tambaya?

Hjy Umaima tace inaji

Yace hjy Idan kuna wannan lesbians din dad’i kukeji?

Hjy Umaima tace Kai Idan ana cinka ta baya dad’i kake ji?

Habib yace na shiga uku, Nayi gamo amma gaskiya banji dad’in wannan zancen ba, wlh har kinsa naji kunya, wai anyi da mutum yaji

Hjy Umaima tace Aiba k’arya Nayi ba, ni kaga ko Kinga zance dan Allah kama hanya zan maka transfer yanzu dan banda cash, koya ake ciki call me, inma bata zo ba make sure ka nemo min ita zuwa gobe, Yarinya sai shegen kafiya, Nayi Asirin amma shuru, aiki ya’ki kamata, ni Allah yasa tana da ruwa ma,koda yake ko bata dashi yanda na kwallafa rai sai naci ko ana ha maza ha mata saina d’ana, tunda na Kwadaita

Habib yace ah wannan zance yafi karfina, Kinga Nayi gaba, inji alert , domin komai danshi nakeyi.

Hjy habiba iya tashin hankali ta shiga, farhan tunda yabar gidan sai cikin dare ya dawo, a falo yaga mum din tashi, wani irin kallon tsana ya Mata tare da d’auke idonshi daka kanta, dan baya bukatar yana ganinta ko kallonta, domin abunda ya gani shine yake dawo mishi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button