BARIKI NA FITO 1 & 2
Ganin yana k’okarin wucewa yasa ta tashi ta nufeshi tare da fad’in farhan plz ina bukatar magana dakai, dan Allah ka saurareni.
Yace plz matsa min a hanya, I hate to see ur face, bana bukatar koda muryanki inji, sai kuma ya saki kuka.
Hjy habiba tace farhan Nasan dole zaka tsaneni amma Kafin nan ina son kaji dalili na, kayi min uzuri kuma tare da adalci n….
Yace babu abunda zan saurara daka gareki Wlh inda kin San hukuncin abunda kika aikata da bakiyi ba, lallai mum shaidan ya gama dake, kiyi gaggawan tuba tare da ro’kan gafaran Allah, karki bari mutuwa ta riskeki kina Mai aikata wannan mummunan aikin zunubin, wlh mum da kin San irin bala’in dake cikin wannan abun da baki aikata ba, mad’igo wai Uwar data haifeni ita take aikata wannan mummunan abun, amma babu damuwa Allah zai hukunta ki, sannan tun a duniya zaki gani, ko ince kin Fara gani, domin Allah ya jarabci d’anki da son wacce kuke aikata wannan mummunan aikin, kuma Wlh Indai Kinga ban auri haulat ba Allah yasa ba matata bace, ko kuma ni na mutu ko ita ta mutu, saiki shirya amsan abokiyar lalatanki a matsayin surukar ki matar tilon d’anki yana fad’in haka yayi gaba, Tashin hankali ……..
NOT EDITED
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO
BOOK 2
*PAGE 26*
Yarima Aliyu sai nishi yake sama sama, mai martaba ya cire mishi rigan jikinshi ya rage daka shi sai singlet, sai zufa yake ta keto ma Aliyu, duk da kuwa akwai AC a d’akin, mum shigowa tayi cikin tashi hankali ganin halin da Aliyu ke ciki,
Kuka ta Fara tana fad’in Aliyu sannu, tare da kallon mijin Nata tace mu maidashi asibiti.
Mai martaba yace ai kinfi kowa sanin maganinshi, dan haka ki barshi kawai, babu abunda asibiti zasu iya mishi.
Mum fita tayi Jim kad’an sai gata da limam, tana fad’in dan Allah kayi mishi addu’a, nasan wannan Asirin Nata BA’KIN AJANI Ta tura mai, dan Allah mlm dubashi Karta kashe min yaro, tana maganan tana kuka
Mai martaba yace Khadija ina tunanin Kece kike bukatar ruki’a bashi ba, kallon limam Mai martaba yayi tare da fad’in limam kaje abunka.
Limam fita yayi
Mum tace na shiga uku, haba Kai baka ga halinda yake ciki ba, yanzu Inba asiri ba taya danya saki matarshi zai shiga irin wannan halin, wannan wani irin sone haka? Wannan aikin sihiri ne ba komai ba, ban tunanin koni na mutu Yarima zai shiga wannan halin, amma akan y’ar iskan karuwar yarinyar can duk ya d’aga hankalinsa W….
Mai martaba ya daka mata tsawa tare da fad’in Yimin shuru, Khadija zan saba miki, naga alaman kina son wuce gona da iri, ki barshi yaji da abunda yake ji, kinsa ya rabu da matarshi ki barshi haka karki k’arasa shi, komai ya sami Aliyu Kece sila.
Mai martaba kallon Aliyu yayi da yake faman jin jiki tare da fad’in Aliyu Ina son kayi hakuri ka d’auki komai ya faru da bawa kaddara ne, sannan zansa a nemo maka matarka duk da kun rabu zata zauna a nan har sai ta haiyu.
Mum dai fita tayi tana kuka ita an gama da d’anta da mijinta
Koda labari ya iske gimbiya zinatu da gimbiya Amina, zo kuga murna, inda sukai ta fad’in Ashe y’ar iska ce amaryan daya aura, nan suka tashi suna cashewa, inda daka nan magana ta canza ana cikin rawa gimbiya Amina ta kamo kugun gimbiya zinatu tare da fad’in yau zaki cika min Burina tare da alkawarin da kikamin in Kinyi aure zamu fara soyayy…..
Gimbiya zinatu tace dole In cika miki wannan burin naki my love domin Ina cikin nishad’i, sannan bani da wata fargaba K….. Kafin ta k’arasa magana gimbiya Amina takai bakinta cikin na gimbiya zinatu ta Fara kissing dinta…..
Washe gari da safe Bariki ta tashi,kuma Alhmdlh ciwon cikinta ya warke bata jin komai, direct bank ta nufa inda ta tsaya tana jira 8 tayi, lokaci nayi ta shiga ta amsa check book ta rubuta adadin kud’in da take bukata, sannan ta bu’kaci a bata ATM, nan dai ta gama komai cikin awa d’aya, tun tana bank din take jin kaman hanjin cikinta zai fita, dan haka tana barin bank din taga inda ake siyar da waina Aiko nan taji ranta ya biya, zuwa tayi ta siya gashi ba’a cikin shago bane, akan benci kowa yake ci, babu yanda ta iya haka ta zauna tana ci, ita dai burinta taji wainar cikin bakinta, tana ci tana mamaki Wai itace take cin abinci a irin wajannan ga maza, gashi akan titi, Yarima ya fad’o mata a rai tare da tunanin ko wani hali yake ciki yanzu oho, wani hawaye taji ya zubo mata Mai zafi Sosai, lokaci d’aya taji wainar ya fitan Mata a rai, gashi tana jin tashin zuciya, da sauri ta tashi taje gefe ta Fara kwarara amai kaman zata fitar da hanjin cikinta, wani irin jiri taji tana ji, Wanda yasa dole ta zauna a wajan tare da lumshe ido, tana sauke numfashi dakyar, duk wannan abunda take ledan kud’in data ciro yana hannunta, mutanan dake wajan wasu sun tausaya mata, yayin da wasu suke fad’in hala tayi cikin shege ne aka korota har suke fad’in tir da ita, Bariki dai ita burinta jiran ya saketa ta tashi ta shiga cikin kaduna.
Tana nan zaune kaman daga sama taji ana mata magana, da sauri ta bud’e ido, wanda ya sauka a kanshi sukai ido biyu, gabanta taji ya fad’i, ba kowa bane sai Mai kid’a , duk da tana jin jiri saida ta tashi tare dayin baya.
Yace Bariki Kece a yashe a nan haka? Murmushi yayi tare da fad’in daka gani kina neman taimako, yanzu abunda za’ayi kizo muje inada d’aki a nan saiki huta.
Bariki ido ta bishi dashi Wanda jikinshi ga kurajen HIV nan duk sun feso mishi a jiki duk Wanda yasan Kalan kurajen yana kallo zai gane yana da cutar, mai karya garkuwan jikin d’an Adam.
Yace taimakon ki zanyi, kin tsaya kin kafeni da ido, naji ance kinyi aure? Ko dama k’arya ne? Muje in baki masauki ki huta, ko ince Mu huta.
Bariki kai ta girgiza tare dayin gaba dan bata tunanin zata iya furta wani kalma a yanda take jin jikinta.
Binta yayi yana fad’in nan ba maraban jos bane, gwara ki bini in taimaka miki, in bani bama Waye zai kalleki, kalli yanda duk kayanki suka baci, m…. Motar data tsaya a gaban Bariki ne yasa Mai kid’a yin shuru
Wata mota ce ‘kiran Prado ta tsaya gaban Bariki, da sauri aka bud’e motar hafsat ce ta fito daga cikin motar tare da ri’ke Bariki tana fad’in Zainab Ina zaki haka? Usman shima faka tashi motar yayi Bayan ta hafsat, tare da fitowa, tun sanda bariki take cin waina ya ganta shine ya kira hafsat dama jiya da suke waya da hafsat take fad’a mishi halinda Yarima yake ciki, da Kuma neman da Mai martaba yasa ayi mata.
Hafsat tace Zainab maza kizo muje Gida, Yarima yana bu’katarki.
Bariki tace a’ah hafsat tare dayin gaba lokaci d’aya jiri ya kwasheta ta Fara k’okarin yin k’asa hafsat ta kamata tare da sata a mota, suka wuce.
Usman kallon mai kid’a yayi tare da fad’in mai kake binta kayi Mata?? Mai kake nema wajanta? Bud’e Mai ido usman yayi
Mai kid’a ya fara bashi hakuri tare da fad’in taimako nake nema wajanta yana fad’in haka ya ruga da gudu, dan ya tsorata da usman yana tsoran Kar yasa a kamashi.