BARIKI NA FITO 1 & 2
Bariki dake kwance cikin mota bata san inda kanta yake ba, hafsat kiran Mai martaba tayi tare da shaida mishi Anga Zainab a halin yanzu ga sunan suna tafe, amma kaman ta suma.
Mai martaba yace ma Hafsat ta kaita asibiti, shima yanzu zaizo shida Aliyu, domin ga shinan kwance bai San inda kanshi yake ba.
Hafsat tace toh Abba.
Asibiti takai Bariki inda akai emergency da ita domin bata ko motsi, nan aka fara bata taimakon gaggawa.
Basu dad’e da zuwa ba saiga Mai martaba da Yarima an kawo an sashi akan Keken d’aukan marasa lafiya, nan shima aka shigar dashi emergency, likitoci dai suna nan tsaye kan masoya biyu, suna iya bakin k’okarin su.
Yarima ne ya fara sauke numfashi sama sama, alaman yana jin jiki Sosai, sannan sanda aka kawo shi ko numfashin baya iyayi da kyau, irin haka inda an k’ara bata lokaci a gida, sai mutum ya rasa ranshi gaba d’aya, Yarima yana kwance yana nishi sama sama, d’aya daka cikin Dr din ya fara mishi magana tunda yana d’aya daka cikin wanda suka duba Yarima lokacin da abun Farko ya faru, a kunne tare da fad’in Yarima wake up ga matarka kusa dakai, kallon abokanan aikinshi yayi tare da fad’in su matso da gadon da bariki take kusa.
Nan aka matso da gadon sauran Dr din suna son suga Mai d’ayan Dr din zaiyi, idan kuka duba in za’a ma mutum operation tiyata, za kuga likitoci fiye da d’aya ne suke aikin, domin ko wanne zai bada nashi gudun mawan, wani yana da experience fiye da wani, so wannan shine dalilin da yasa suke kallon d’ayan Dr din suga Mai zaiyi.
Kamo hannun Yarima yayi dana Bariki ya had’a waje d’aya, tare da k’ara yima Yarima Aliyu magana a kunne ka tashi matarka na bukatar taimakon ka, Plz wake up.
Yarima tun sanda aka sa mishi hannun Zainab a nashi, zuciyarshi ta Fara harbawa da sauri, suda kansu sauran Dr din sunyi mamaki, lallai soyayya ba k’arya bane and basu taba ganin irin wannan son ba, ashe hakan na faruwa, ikon Allah.
Yarima Aliyu a hankali ya fara bud’e ido, wanda suka sauka akan selling d’in d’akin, lokaci d’aya ya waiga ganin Zainab kwance kusa dashi ya fara k’okarin tashi, da sauri Dr ya rik’eshi tare da fad’in plz Aliyu ka kwanta matarka Tana kusa dakai babu inda zata.
Yarima Aliyu hannun Dr yake k’okarin cirewa daka jikinshi amma ya kasa saboda jiki babu ‘kwari.
A hankali yace plz leave me, I want to see my wife.
D’aya daka cikin Dr din yace ka d’agashi ya ganta.
D’ago Yarima Aliyu yayi tare da matso dashi gadon da Zainab take, k’ara matse hannunta yayi yana hawaye tare da fad’in my princess I will never ever let you go from me again, I can’t live without you, my princess why r you go far away from me?….. Lokaci d’aya kuma yayi shuru komai ya tuna kuma oho, yayi wajan minti biyu yana kallon Zainab, lokaci d’aya kuma ya rungumeta duk da tana kwance, sun dad’e a haka Kafin Bariki ta farka tare da bud’e idonta itama kukan ta Fara, tare da matse mijinta a jikinta tana fadin Yarima zan mutu , mai yasa mum bazata duba irin sonda nake maka ba, Yarima plz kaba mum hakuri ta hakura ta barmu tare, bazan iya rayuwa ba tare dakai ba, plz Yarima kazo mu gudu muyi rayuwa a wani waje wanda babu wanda zai gammu….
Muryan mum sukaji Tana fad’in Sai dai ke ki gudu ba d’ana ba, y’ar iska, har abada d’ana bazai taba barin iyayenshi ba, kaman yanda ke kika bar naki, y’ar iska karuwa hafsat dake Bayan mum tana takaicin abunda mum din ke fad’a tare da tausaya ma d’an uwan nata da matarshi, k’okarin fita tayi domin kiran Mai martaba dake waya a waje Aiko jiri ya d’ibeta lokaci d’aya tayi k’asa, nan mum ta waiga jin kaman mutum ya fad’i, ganin hafsat ce yasa ta saki ihu tare da fad’in na shiga uku, da gudu ta fita ta kira Dr inda aka fara duba hafsat din itama.
Nan mum ta fita ta kira Mai martaba take fad’a mishi hafsat ta fad’i Tana ciki ana dubata, hankalin Mai martaba ya tashi Sosai, yara uku ba lafiya, Yarima da matarshi ga hafsat, mai martaba ko zama ya kasayi saboda tashin hankalin da yake ciki, tare da fargaban maike damun hafsat itama
Sunyi wajan 30mnt suna jira Dr ya fito wanda tun a ciki Dr ya fad’ama Yarima Aliyu abunda ke damun hafsat, ya shiga mugun damuwa wanda ko magana ya kasayi, Bariki ce tayi karfin halin ro’kan Dr akan karya gayama mum da Abba a waje saboda Akwai fadawa, ya shigo dasu nan ne Kafin ya Sanar musu, hakan ko akayi aka kira mum da Mai martaba, inda Mum ta Fara fad’in Dr dan Allah fad’amin abunda ke damunta?
Hafsat na kwance tana bacci abunta, ansa Mata drive.
Dr yace hjy tana d’auke da ciki na wata uku, abunda yasa ta fad’i saboda jikinta yayi weak, is lyk Tana cikin damuwa so….. AI tuni mum tayi k’asa sumamma, shiko Mai martaba kasa magana yayi sai Innalillahi’wa inna ilaihirajiun da yake ta faman furtawa cikin ranshi, ganin mum tayi k’asa yasa ya d’agota da sauri inda Dr ya d’auko ruwa aka yayyafa Mata ta Farko .
Kuka tasa tare da fad’in Hafsat kin cuceni, kin gama dani, yanzu irin tarbiyan dana baki kenan? Kin d’auko mana Abun kunyar da ban taba jiba ko a zamanin baya ba, ace y’ar gidan sarauta tayi cikin shege, kuka Mum take Sosai cikin ‘kunan rai, tare da ba’kin cikin abunda y’arta ta d’auko, shiko Mai martaba kukan zuci yake lallai basai kayi abuba Allah yake jarabtanka, koda baka kasance mazinaci ba, Allah yakan jarabceka da samun mata mazinaciya ko kuma cikin y’ay’anka, lallai babu yanda Allah bayayi akan wannan al’amarin, Allah yakan jarabci bayinshi tako Ina, yaga ya za suyi.
Zainab dai itama tana zaune tana hawaye, lallai abunda ciwo, ganin yanda mum take kuka saita tuna da dad d’inta, irin halin daya shiga sanda yace tana da ciki, Wanda ita bata san Wanda yayi mata ba, sai yanzu Bariki take k’ara ganin laifin kanta wanda komai dad d’inta zai Mata bai kamata ta fad’a Bariki ba, danta kuntata ma mahaifinta ba, gashi yanzu abunda tayi shi take girba,tayi aure amma saboda rayuwar da tayi baya ya bata mata rayuwar auranta, kuka ta saki mai sauti wanda hankalin kowa yayi kanta.
Mum kallon Bariki take irin yanda take kuka, jikin mum yayi sanyi, lallai abunda mijinta yake fad’a mata gaskiya ne, kaddara tana kan kowa, gashi yanzu ya fad’a kan y’arta, Innalillahi’wa inna ilaihirajiun. Hmmmm Allah sarki rayuwa kenan, kowa baya yarda da kaddara saiya fad’a kanshi, sannan zai san kaddara ne, Abu Indai ba’a kanka ya fad’a ba to wajan kowa ba kaddara bane wasu sai su dinga fad’in dagangan mutum yayi ko kuma ace shiya sa kanshi, Hmmm mutane suna bani mamaki, wlh baki shi yake Kai mutum ga halaka, sai kuji mutum yana fad’in Wlh ni ai duk wacce take karuwanci ita taso maganganu dai irin haka, toh Wlh y’an uwa ku iya bakinku, Domin kuwa Allah zai iya jarabtanku ku fad’a cikin harkan karuwancin sai yaga yanda za kuyi, sai yasa a kullum ake son mutum ya dinga fad’in Alheri, kaman dai irin abunda mum ta dinga fad’i akan Bariki ita bata haifi karuwa ba, sai gashi y’arta da cikin shege, lallai dubaranka ko wayanka bashi bane zai sa Allah ya’ki jarabtanka, Allah yana jarabtan bayinshi ta hanyoyi da dama domin ya gwada imaninsu, wasu ta dukiya, wasu ta ciwo, wasu na talauci babu yanda Allah bayayi, sai dai muyi fatan Allah yasa mu cinye ko wace jarabawa da zata zo mana a rayuwa.