BARIKI NA FITO 1 & 2
Mum tashi tayi tare da nufa inda Yarima da Bariki suke ta Fara bashi hakuri tare da fad’in lallai ni uwa ce, wacce ban kasance mai fahimtar abunda d’ana yake soba, ni uwa ce Mai son kanta, tunda na nuna nafi son y’ay’ana akan na wasu, na kasa amsar kaddaran data fad’a ma matarka, Ina gudun kaci gaba da zama da ita, yau gashi nima Allah ya jarabceni y’ata d’auke da ciki ba tare da aure ba, ciki harna wata uku, lallai Allah ya nunamin ishara, kamo hannun Bariki tayi tana fad’in dan Allah ki yafemin Wlh Ina jin kunyar kaina irin munanan kalaman dana dinga fad’a miki, gashi nasa d’ana ya miki saki har uku, banyi la’akari da cewa Kece rayuwarshi, ba idona ya rufe Ina ganin kaman kin mallake min d’ana kuka yaci karfinta Sosai.
Bariki cikin kuka tace mum kiyi hakuri, nayi imani da kaddara, lallai na yarda sakin da Yarima yayi min yana cikin kaddara na, ban taba ganin laifinki ba, abunda kika aikata ko wace uwa abunda za tayi kenan, babu wata Uwar da zata so d’anta ya zauna da macen da tayi rayuwar Bariki, lallai nima na cuci kaina kuka ta saki mai sauti wanda duk wannan abunda suke idon hafsat biyu tana ji itama hawaye take, lallai tayi kuskuren mallaka ma Umar jikinta gashi yanzu baya Raye.
Mai martaba daya kasa magana sai yanzu ya iya bud’e baki, yace Zainab daka ina kika fito, Ina son ki fad’amin koke wacece dan a nemi iyayenki mu samman yanzu da kike da juna biyu ya kamata musan iyayenki
Bariki taba cikinta tayi tana mamaki dama ciki gareta? Wani hawaye mai zafi ya fito mata nan ta Fara bama Mai martaba Labarin irin abunda ya faru da ita harda irin rayuwar da tayi a bariki, ta k’arasa maganan cikin kuka mai ban tausayi .
Kowa ya tausaya mata,ciki harda hafsat dake kwance tana jinsu, jikin mum ya k’ara sanyi Sosai, tare dayin nadaman abunda ta aikata ma Bariki, lallai tayi kuskure babba, ashe itama babban kaddara ne ya fad’a mata, had’e da Sharrin matar uba, lallai wasu matan bazasu ga annabi ba, tayi sanadin lalacewan yarinya danta k’i yarda da kudirinta na aikata mad’igo, Mum jikinta yayi sanyi Sosai, gashi ta raba d’anta da ita, koya rayuwarshi zata kaya?
Mai martaba yace dama ke yarinyar Sheikh musa monguno ce? Ikon Allah, d’azu dashi muke waya kan cewa yazo Nigeria nace mishi muna asibiti, nasa aje a d’aukoshi daka airport Wanda na tabba sun kusa zuwa nan bada dad’ewa ba, Abokina ne tare mukai karatu a k’asar misra, lallai abun yaban mamaki, Yarima yasa in gayyato shi akan yana son ya gabatar da lacca, Amma Zainab kinyi kuskure babba, iyaye ai iyaye ne, komai suka miki bai kamata ki k’ara bata rayuwarki ba danki kuntata ma mahaifinki, haba zainab ina iliminki? Kin aikata babban kuskure a rayuwa.
Kallon Yarima Mai martaba yayi tare da fad’in ko kasan shine mahaifinta dama??
Yarima yace eh Abba, ranan da aka d’aura mana aure na gane tamin k’arya, inda daka baya ta fadamin gaskiya, shine na bukaci ka gayyatoshi dan nasan inka kirashi zai zo, kayi hakuri Abba Nayi maka k’arya akan ina son yazo yayi lacca, Nayi hakan ne danka kirashi yazo in dai daitashi da y’arshi, ni bamma san abokinka bane, dani dakai na zani wajansa har misra din.
Mai martaba yace lallai Aliyu kayi jahadi, Allah yayi maka albarka, karan wayar Mai martaba ne yasa ya d’auka tare da fita waje, Jim kad’an sai gashi ya shigo da sheik musa monguno da matarsa Falmata wacce tasha hijab har k’asa kamar wata mutuniyar kwarai, idon sheik musa monguno ya sauka akan na gudan y’ar tasa Aiko yana ganinta ya fara nunata da hannu lokaci d’aya kuma ya fad’i k’asa……. Hmmm muje zuwa muji maike faruwa?
~MARYAM OBAM~
BARIKI NA FITO
*BY*
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Maryam Obam)
WWW.Maryamobamnovels.com
Wattpad @maryam-obam
Instagram@maryam_obam
MARUBUCIYAR
1)FATIMA ZARAH
2)DUKIYAR MARAYA
3)BA’KIN ALJANI
4)BANDA ZABI
5)AMINIYA TACE
6)KISSA KO MAKIRCI
7)SAINA AURESHI
8)SUHAILAT
9)TAMBARIN TALAKA
10)JAWAHEER
11)MIYE ILLAR Y’AY’A MATA
AND NOW…. BARIKI NA FITO
DEDICATED THIS PAGE TO….
MY DEAR MY LOVELY FRIEND QWEEN PHAREEJAY
BOOK 2
*PAGE 27*
Bariki ihu ta saki cikin tashin hankali, nan mum ta fita da gudu kiran Dr, yayin da Falmata take ta zunduma ashar kan cewa Bariki zata kashe mata miji, Bariki kam kuka take tana manne jikin Yarima, Falmata k’okarin cafko Bariki take, Yarima kaman ya Lura da hakan yasa ya dawo da Bariki baya tare da shiga gaba.
Dr shigowa yayi inda ya bu’kaci su mum damai martaba da Falmata su fita danya samu ya duba patient din, nan Dr Ya fara duba sheik musa monguno, cikin ikon Allah ya Farfado nan ya fara kuka tare da zufa dake faman keto mishi, tashi yayi tare da nufa wajan da Bariki take inda ya fara kuka yana neman gafaranta akan abunda yayi mata, wanda yace Wlh bai San ya akai har shida kanshi ya koreta ba,
Dr fita yayi domin yaga ba wani serious ciwo bane, suma yayi and kuma ya Farfad’o, ganin Dr Ya fita yasa su mum shigowa.
Falmata ganin mijinta ya tashi yasa ta Fara rusa kuka lokaci d’aya kuma ta Fara dariya tare da fad’in Nina sa akama Zainab ciki saboda ka tsaneta Wlh nice nasa aka mata hahahaha hahahaha sai kuma ta saki kuka lokaci d’aya kuma taci gaba da fad’in
Nice nasa mata kwaya cikin juice tasha, tayi bacci Mai nauyi, Nasa driver ya mata ciki, hahahaha bayan nasashi na koreshi, daka karshe ya faramin barazana nasa aka kasheshi har lahira, wlh nice nasa aka mata ciki, saboda ta’ki yarda dani, ni kuma ina sonta Sosai ina son in lashi zumarta, Wlh Ina Sonta Sosai dan Allah ku bani ita, ko ku aura min ita, sai kuma ta k’ara fashewa da dariya taci gaba da fad’in abunda yasa nasa aka mata ciki saboda ina son Dad d’inta ya tsaneta, yace ta d’auko mishi abun kunya, kuma Nayi wannan tunanin ne saboda Kar wata rana ta tauna min asiri dan yana jin magananta, kuma in ya tabbatar tana da ciki zai daina yarda da ita, bayan nasa anyi mata ciki, nasa akaje min maiduguri wajan wani boka inda na amso mugun sihiri Wanda na rufe mishi ido da baki sai abunda nace, duk da lokacin sihirin baiyi wani tasiri Sosai ba, dan Bayan ya koreta yaita fama da ciwo tare da damuwa yana mamakin Wai shine ya Kori y’arshi da kanshi, ganin irin damuwan da yakeyi gashi ana kawo mishi hotanta da shigar banza, hakan yasa hankalinshi ya tashi Sosai, ganin irin halin daya shiga yasa na tafi maiduguri dakai na wajan boka, gashi ina takaicin ban haiyu dashi ba, yau Idan ya mutu ba wani kud’i zan samu Sosai ba, inda Nayi mishi bayani, tare da cewa Ina son a cire mishi tunanin Zainab harta danginshi kona mamanta karsu nemeta, boka yace wannan aikin akwai hatsari Sosai sannan akwai zunubi Sosai, domin raba y’a da iyayenta babban aiki ne, nan nace ma boka na d’auka, boka yace dad din Zainab yana matukar son y’arshi Sosai koda anyi aikin muddin ya ganta komai zai lalace, Indai kina son aikin yayi tasiri karki bari su had’u, nace ma boka babu damuwa
Yace an gama, za’a tura mishi Aljani, wanda zai dinga juyashi, nan na amince boka ya k’ara min kashedi Idan na Bari suka had’u komai ya faru dani Kar ince bai fad’amin ba? Nace na amince domin a lokacin idona ya rufe.
Bayan na dawo Abuja naga aiki yayi, domin a lokacin tunanin Zainab yasa dad d’inta ya rage ibada, domin yana cikin ciwo, wannan ne yasa nayi nasara akanshi, har Aljani ya shige shi, saboda ina fargaban karsu had’u nasa muka koma misra gaba d’aya inda na bu’kaci Nima Ina son inyi karatu a can, wannan ne dalilin komawarmu k’asar misra yana business dinshi ta Nigeria da kasashen da yake yi, amma maganan zuwa Nigeria gaba d’aya nasa an cire mishi a rai, kwasam sai gashi yace min zaizo Nigeria amininshi yana nemanshi zai gabatar mishi da wani lacca, a lokacin na tsorata domin kuwa harta wa’azin da yake zuwa nasa an hanashi, sai gashi ya kawo min maganan zuwa Nigeria yayi lacca, da Farko naso in hanashi sai kuma Nayi tunanin muzo dan Ina son zuwa maiduguri wajan boka inji ya akayi ko aiki ya fara sanyi ne, ashe asiri ne zai tonu.. Dariya ta saki Tana fad’in Wlh koda zan mutu saina ciki Zainab Ina sonki.