BARIKI NA FITO 1 & 2
Kowa dake wajan salati yake cikin takaici tare da jimami, da Allah wadai da halin Falmata
Dad d’in Bariki nan take yace Falmata na sakeki saki uku, kuma insha Allah sai Kinga abunda kika aikata, kin cuceni kin batamin rayuwar y’ata, lallai Falmata sai nasa an hukunta ki W…..
Mai martaba yace kayi hakuri, baka ga halinda take ciki ba, Mai martaba ya lura da Falmata kaman ta haukace.
Falmata tace saime cikin ihu, ni dama ba Sonka nake ba, saboda kud’i na aureka, da naga y’arka sai naji Ina Sonta, tunda naga irin suranta kuma Wlh sai na cita,hahahha Kaga koda ka mutu nida ita zamu zauna muci kud’inka, sannan ta dinga biya min bukata, Hahahahahaha sai kuma ta saki kuka tare da fara k’okarin cire hijab d’inta, nan mum ta k’ara fita ta kira Dr.
Koda Dr yazo dakyar aka ri’keta tana ta fusge fusge, andai samu an d’aureta dakyar inda sheik musa monguno yace zai sa a maidata maiduguri domin wlh ko sisi bazai bada ba wajan yi mata magani ba.
An ro’ki Dr akan su Fara dubata inda Mai martaba ya bada umarni tare da fad’in ba’a saka sharri da sharri, Dr yace gskiya wannan asibitin mahaukata za’a kaita, mai martaba yace babu damuwa a kaita, zai biya ko nawa ne, nan akai Gaba da Falmata. Kai rayuwa kenan wannan shi ake cema sakayya, lallai Allah ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya cuci kanshi, duk irin abunda Falmata tayi gashi ya koma kanta, kai Mata mata Wlh muji tsoran Allah.
Sheik musa monguno kuka yake tare da ri’ke hannun Zainab yana tambayanta akan ta yafe mishi
Cikin kuka tace babu abunda yayi mata, tace Dad niya kamata in nemi gafaranka, dana biye ma shairin zuciya, tare da kokarin San in kuntata maka, ta wajan aikata aikin sabon Allah, Dad na cuci kaina da yawa, dan Allah ka yafe min dad ta k’arasa maganan cikin kuka
Janyo y’ar tashi yayi tare da rungumeta su duka suna kuka abun tausayi.
Yarima Aliyu jin kukan hafsat din yake har cikin ranshi.
Hafsat da tun ihun da Falmata ke zabgawa yasa ta tashi ta zauna, nan itama ta fad’o daka kan gadon d’akin ta zube a gaban iyayenta tana kuka akan su taimaka mata su yafe mata.
Mai martaba yace duka su tashi suyi gida, acan za’ayi magana, hafsat jikinta yayi sanyi ganin mahaifin nata ko kallonta baiyi ba, lallai ta aikata babban kuskure na yarda da Umar wajan bashi jikinta, kuka take Sosai, inda gaba d’aya suka fita Bayan an tambayi Dr ko akwai wani damuwa, Dr yasa anba ma Hafsat magani sannan yace Bariki tana bukatar hutu Sosai, inda so samu ne ma a bata bed rest, da Farko Yarima Aliyu yace ta koma a bata gado, amma tace a’a a gida zata fi samun hutu, babu yanda ya iya dole ya biye mata itama aka bata maganin suka nufi Gida, duka a babban falon Mai martaba suka zauna inda Mai martaba ya kira waziri akan yazo, domin yana son yin magana yau wanda tun tuni yake son yi.
Kowa ya hallara, inda Mum tace ina zinatu ya kamata tazo itama, mai martaba yace Aliyu yaje ya kirata.
Yarima Aliyu fita yayi amma bai soba, domin duk zuwa asibiti da yayi bata tako k’afa tazo ba, and yanzu kuma maganan daya shafi Zainab za’ayi sai yake ganin kaman bai kamata tazo wajan ba, tunda kishiyar Zainab dince ita.
Direct gefenta ya shiga tun Kafin ya k’arasa d’akinta yake jiyo maganansu ita da gimbiya Amina, wanda yama manta tazo, gimbiya zinatu tana fad’in ai Wlh inda badan wannan maganin dana sama Yarima yayi mishi karfi ba, toh da Wlh zai gane niba virgin bace, ki duba fah ki gani baya cikin hayyacinshi har Ya iya gane niba virgin bace, dariya gimbiya Amina ta saki tare da fad’in hmmm ai tunda yaga wannan jinin na tabbata dole ya yarda ke budurwa ce.
Gimbiya zinatu tace yauwa wai jinin miye kika Aiko min dashi?
Gimbiya Amina tace Wlh fadawa naba kud’i suka kawo min, nace musu kona dabba ne kona mutum suje asibiti su siya, bayan sun dawo suka cemin Sun yanka raguna uku, shine suka kawo min jinin
Dariya gimbiya zinatu ta saki tare da fad’in ashe jinin rago ne, Yarima ya d’auka jini nane, kai gskya anyi bidiri, dariya suka saki.
Gimbiya Amina tace shidai duka baiyi dace ba, ita wancan amaryan tashi ba budurwa ba, Kema gaki, yatsa da ayabar roba yasa kin rasa budurci.
Gimbiya zinatu tace uhm Kedai bari, ni bada sanin namiji ba budurci ya gudu, hmm inda Yarima bai saki matarshi ba Aida tasha gori wajena Wlh da habaici
Gimbiya Amina tace toh Kema dai Kibi sannu a hankali, domin wlh idan Yarima ya gane kin mishi wannan yaudaran kashinki ya bushe, shi yanzu yana miki kallon budurwa ne
Yarima Aliyu dake tsaye yana jinsu cikin tashin hankali, gaba d’aya jikinshi yayi sanyi, ji yayi kaman ya juya amma wata zuciyar tace ka shiga ka nuna musu kaji komai, dan haka ya kutsa Kai kalman Innalillahi’wa inna ilaihirajiun ya iya furtawa, ganin gimbiya zinatu da gimbiya Amina zindir haiyuwar uwarsu jikinsu manne dana juna.
Yarima Aliyu tunda ya furta wannan Kalman na Innalillahi wa inna’ilaihira jiun bai k’ara cewa komai ba, sai hawayen dake idonshi dake zuba, tare da fad’in wannan wace irin jarabawa ce cikin ranshi, juyawa yayi ya fita jim kad’an sai gashi da mum d’inshi itama Abun ya bata mamaki, gimbiya zinatu da gimbiya Amina, Sun kasa koda motsi ne
Yarima Aliyu kuka yake yana fad’ama mum dinshi abunda yaji, suna fad’a tare da fad’in mum ban kasance mazinaci ba, amma Allah ya bani Mata fasikai,mum.. Kuka ya hanashi k’arasa abunda yayi niyan fad’a.
Mum rarrashinshi take tare da fad’in yayi hakuri ya d’auka wannan shine jarabawanshi na rayuwa, uhm su mum kenan yanzu an gane kaddara da jarabawa uhm.
Yarima yace mum bazan zauna da macen dana Kama tana aikata mad’igo ba, na tabbata duk macen dake aikata lesbians kallon hoto take ma mijinta, tana mishi kallon sakarai, mum bazan iya zama da itaba, lallai laifinta yafi na kowa muni, mum kice ta tafi bana son ganinta,
Zinatu da sauri ta taso tana kuka tare da ri’ke kafan Yarima tana bashi hakuri akan bata dad’e da fara aikata wannan aikin ba, dan Allah Yarima ka yafe min Wlh yi kawai nakeyi, amma bawai Ina jin dad’inshi ba, kuka take Sosai tana bashi hakuri
Mum tace tashi kisa kaya ki samemu falon Mai martaba, tare da kallon gimbiya Amina tace ke kuma ki shirya ki koma Gida, abunda kuka aikata dakai na zan fad’ama iyayenku, tana fad’in haka taja Yarima suka fita, tana fad’a mishi karya sake yace zai rabu da matarshi, tare da fad’in a farko tayi kuskuren raba shi da wacce yake mutuwar so, bazan k’ara Bari ka saki matarka ba, itama Zainab Ina neman hanyar da zaku dawo tare ne.
Koda suka je cikin falon idon Yarima Mai martaba ya kalla, yace maiya faru? Mum shuru tayi haka shima, yarima, muryan Gimbiya zinatu suka ji Tana fad’in dan Allah Abba kuyi min rai Nasan na aikata mummunan laifi, wlh shairin shaidan ne, dan Allah Abba kaba Yarima hakuri karya rabu dani Ina sonshi, wlh ban taba aikata mad’igo ba sai shekaran jiya, duka salati suka saki kowa kallonta yake cikin jimami da Tashin hankali .
Jin kowa na salati yasa gimbiya zinatu kallon mutanan dake d’akin, wanda idonta ya rufe bata ko Lura dasu ba, sai yanzu cikin jin kunya tare da tsanar kanta da kuma gimbiya Amina da tasa ta Fara aikata wannan abun.
Mai martaba ne yayi gyaran murya tare da fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, kai duniya kai duniya Mai take son zama ne, da farko dai zan fara da Zainab yanzu Zainab zaki bi dad d’inki ne ko zaki zauna a nan har sai kin haiyu?