BABU SO HAUSA NOVEL

BARIKI NA FITO 1 & 2

Bariki cikin sanyin jiki tare da zubar da hawaye tasan ta rasa Yarima har abada tace Abba zanbi Dad Dina

Da sauri Yarima yace ban amince ba, wanda bai San maganan ta fito ba

Kowa kallonshi yayi,

Mum kam kuka take k’asa k’asa domin tasan d’anta bazai jure rashin Zainab ba, kai ta cuci d’anta, ta rabashi da farin cikin shi

Mai martaba yace Aliyu karka manta yanzu Zainab ba matarka bace.

Yace Abba Zainab har gobe tana matsayin matata

Mum da sauri ta d’ago tana kallonshi, bama mum ba duk wa inda ke falon, yace Abba sanda mum tace in saketa na rubuta mata saki biyu Naji bazan iyayi mata uku ba, bayan na bata takardan naga mum bata damu data duba takardan ba hakan yayi min dad’i amma ganin yanda mum ta korata yasa naji a jikina kaman mum bazata taba Bari in dawo da ita ba, lokacin dana Fara ciwo nan take na dawo da ita, Zainab yanzu tana matsayin matata, takardan dana bata yana hannunta

Mum wani irin ajiyan zuciya ta sauke tare da furta Alhmdlh, Allah na godema.

Bariki tace Yarima Wlh sanda kaban takardan ban duba ba, harna yaga shi saboda ba Abun kallo bane, ashe saki biyu ne sai kuma ta saki kuka.

Mum ta tashi taje kusa da ita tana fad’in kiyi shuru zainab, wlh nafi kowa murna, inda Yarima saki uku yayi miki, dana shiga uku, kai Allah na gode ma, naso in aikata kuskure a rayuwa, naso bata rayuwar d’ana da kaina, sai yasa akace ba’a yanke hukunci cikin fushi, yau gashi naga yanda naso jefa yarana halaka sai kuma itama ta saki kuka, Bariki ganin haka sai ta dena Nata kukan ta Fara rarrashin mum.

Mai martaba yace yanke hukunci cikin fushi babu abunda yake haifar wa, sai dana sani, A kullum ana son Kafin ka yanke hukunci ka Fara bincike inka tabbatar, saika zauna kayi tunani akan maiya kamata, inko kace zaka yanke hukunci cikin fushi lallai zakai dana sani, Allan yasa kun fahimta.

Mai martaba ya kalli sheik musa monguno, ya fara bashi irin rayuwar da y’arshi ta shiga, bayan ya koreta har zuwa auran Yarima da tayi.

Sheik musa monguno kuka ya fara tare da fad’in Falmata ta cuceni, ta batamin rayuwa data y’ata, kallon Zainab yayi tare da fad’in ki yafe min inda ban aureta da hakan bai faru ba.

Mai martaba yace ka daina fad’in haka, sheik ko ka manta Idan Allah yasa abu zai zo gareka dole sai yazo, sannan sheik asiri yana bin hali ne, na tabbata koda Falmata bata maka asiri ba, zaka iya Koran Zainab, domin lokacin kana cikin fushi, zaka yanke hukunci cikin fushi, domin zaka ga a matsayinka na babban Malami y’arka ta kwaso cikin shege na tabbata koda babu asiri zaka iya koranta, daka baya kayi dana sani, sai yasa akace ba’a yanke hukunci cikin fushi, a lokacin duk da akwai sihiri a kanka Bayan ta tafi aika nuna kayi nadama, tare dason ganinta.

Sheik musa monguno yace hakane, tabbas asiri yana bin hali, asiri yana tafiya ne da halin mutum, Allah ka k’ara tsare mana imanin mu, kallon Yarima yayi tare da fad’in lallai Aliyu ban San da wani baki zan gode maka ba, domin kayi babban jahadi na ceto rayuwar Zainab, duk da kasan irin rayuwar da tayi daka baya, bayan tayi maka k’arya kaci gaba da zama da ita, lallai ban tunanin duk irin sonda nake mata cewa nawa yafi maka, lallai ka fini son Zainab, tunda harka iya zama da ita, sa’banin nida nake mahaifinta sanda take bukatar kulawata Sosai lokacin na juya mata baya, duk saboda fushi tare da kunyar duniya, kai kaico na, Yarima Allah yayi maka albarka.

Yarima ya amsa da Ameen tare da kallon zainab wacce itama shi take kallo, Yarima ido ya kashe mata, da sauri tayi k’asa dakai tana murmushi tare da tsoran Allah yasa wani baiga sanda ya kashe mata idon ba.

Mai martaba kallon waziri yayi tare da fad’in, Ina son aje a sauke sarkin u/k daka kan kujeranshi, domin bai kamata a barshi yana shugabantan al’umma ba, a sami wani kamili Dattijon arziki a saka, amma yau nake son a bashi takardan murabus, domin duk mutumin da zaiyi Abu saboda kud’i ciki harda yaudara ba mutumin arziki bane, bai kamata ya dinga shugabantan al’umma ba, nan take waziri yace an gama ranka ya dad’e

Mai martaba kallon hafsat yayi tare da kiran sunanta da sauri ta d’ago cikin faduwan gaba tace na’am Abba, tana hawaye

Yace hafsat Mai kika rasa? Mai kika nema kika rasa? Hafsat wani irin tarbiya ne bamu baki ba? Dama kin San kina da ciki shine kike k’okarin yin aure da cikin wani? Hafsat kin bani mamaki matuka.

Cikin kuka tace Abba ka yafemin Wlh cikin Umar ne

Mai martaba shuru yayi cikin jimami da takaici, Amma babu yanda ya iya, wannan abunda ya sameshi kaddara ce.

Yace hafsat gashi Umar ya rasu, yanzu kina tunanin zaki sami wanda zai aureki, Bayan kin bata rayuwarki?

Sheik musa monguno yace mai martaba, yanzu ka gama bayani akan hakuri da dangana, da kuma d’aukan kaddara, kayi hakuri, ka cinye wannan kaddaran taka kaima.

Mai martaba yace hakane, Allah yasa mu dace, zan nemi iyayen umar din muyi magana dasu

Kallon gimbiya zinatu yayi sannan yace zinatu kinyi matukar bani mamaki, kin San bala’in dake cikin aikata mad’igo kuwa? Bariki kiji daka aikata mad’igo gara kayi zina duk da shima babban bala’i har gwara mai aikata zina akan mad’igo Bari kiji illar dake cikin zina kawai Kafin muzo wajan mad’igo

Mai zina mace da namiji akace ayi musu bulala d’ari, kuma kada aji tausayinsu akan bin hukuncin Allah, Indai kayi imani da Allah da Ranar lahira, sannan ana son jama’a mumunai su halarci azabar da za’ayi musu, wannan in saurayi da budurwa ne wanda basu da aure.

Masu aure kuma mace kona miji jifa ne.

Manzon Allah (S A W) Yace:
Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina sai an cire mishi imani… Wa’iyazubillah yanzu Idan kana aikatawa Allah ya d’auki rayuwar mutum kunga ya mutu a kafiri Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, yarima yasa mu dace .

Yace zina ta had’a dukkan sharri gaba d’aya, zina bala’i ce babba, tana haifar da bala’i Mai girma, Tana sa rashin tsoran Allah, tare da haifar da cututtuka da mutuwar zuciya, Tana sa zuciyar mutum tayi ba’ki da tsatsa ,tana sa mutum kullum ya jishi cikin damuwa da rashin kwanciyan hankali, sannan tana haifar da talauci, da zubewar mutunci, mazinaci dukiyarshi bata albarka, saboda kullum yana neman mata yana basu, Suma matan basa iya tara dukiyar saboda suna ganin wani zai basu, a haka za suyi ta zama har su daina samu, kowa ya’ki taimakon su.

Manzon Allah ( S A W) Yace mutum bakwai Allah ya tsine musu, kuma bazai kallesu da rahma ba ranan Al’Qiyama zaice musu ku shiga wuta Innalillahi’wa inna ilaihirajiun..

Mai yin zina da dabbobi
Mai yin luwadi da mad’igo
Wanda akeyi dashi
Mai yin zina da uwa
Sannan kuma yayi da y’arta
Mai yin wasa da al’aurarta
Ko maiyin wasa da gabansa
Masturbation kenan

Zinatu cikin kuka ta Fara fad’in Wlh shekaran jiya na fara wannan mummunan abun, da masturbation nakeyi Ashe shima babban laifi ne, wayyo Allah na tuba

Mai martaba yace
Yana d’aya daka cikin laifukan da mutanan Annabi LUD suka aikata, sannan an ruwaita duk maiyin haka Indai harya mutu bai tuba ba zai tashi ranan alkiyama hannayenshi d’auke da ciki

Yarima Aliyu yace Abba sannan duk maniyin da aka fitar dashi da gangan baya fita gaba d’aya wanda ya rage saiya daskare ma mutum cikin mara, sannan yana sa rashin haiyuwa wannan daskareren maniyin yana kashe kwayoyin hallita daga jikin namiji ko mace, sannan likitoci sun k’ara fadada bincike akan hakan yana haifar da mugayen cutuka kamar haka
Saurin yin realising mutum nan da nan yaji ya Kawo, Yana saka raunin ido, mutum Idan yanayi zai iya rasa idonshi har abada, yana sa mutum yawan mantuwa, raunin al’aura, wannan y’ana d’aya daka cikin abunda masu wasa da yatsa ko masu aikata mad’igo yake haifar wa, bance duka ba sai yasa yanzu mata yawanci suke fama da rashin haiyuwa, wata ita lokaci ne baiyi ba, wata kuma tana aikata mad’igo Wanda maniyin daya fita sauran ya daskare mata a jiki, Abba tunda na Fara aiki a asibiti Ina had’uwa da abubuwan al’ajabi da dama sai dai muce Allah ya shirya ya ganar damu hanyar gaskiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button