BARIKI NA FITO 1 & 2
Bayan kinyi zina kin had’a da mad’igo, har d’anki ya kamaki, Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, kin aikata zunubi mafi girma y…….
Cikin kuka tace dan Allah ka yafemin, ko Allah Idan mukayi laifi muka tuba yana yafe mana, dan Allah ka yafemin Wlh na tuba, sannan ni mace ce ina da bukata tare da sha’awa, yau rabon daka kulani wani abu ya shiga tsakaninmu harna manta, burina bawai Inci abinci bane ko sutura a’a ina da bukatar hakki na, tunda Nima mutum ce, da farko Ina zaune dakai saboda kana da dukiya Kar ince ka rabu dani ban San wanda zan aura ba, ganin ban son in rasaka yasa na Fara aikata zina, ganin zaka iya kamani yasa na Fara neman mata yanda koda kazo Kaga mace bazaka zargeni ba Dan Allah ka yafemin.
Jikinshi yayi sanyi lallai shima yana da laifi Sosai, ko yace shine mai laifi ma gaba d’aya, yau zai iya cewa rabon da yayi wani abu da ita yakai wajan Wata biyu ko fiye da hakan ma, lallai shine mai laifi babba, bawai kaba mace kud’i ko wani Abun jin dad’in rayuwa ba, tana da bukata, babu abunda nasa sai business da neman kud’i, bani can k’asar yau bani can, bani da lokacin iyalina Kai gaba d’aya nine ma Mai laifin, jikinshi yayi sanyi Sosai, duk da yasan shi ba wani tabuka Abun arziki yake a gado ba, amma yasan inda yana biya mata bukata koda yaushe bazatai marmarin wani ba, ko kad’an. Kallon hjy habiba yayi tare da fad’in na yafe miki duniya da lahira, sai kiyi tayin istigfari tare da neman gafaran uban giji, domin kofofin tuba a bud’e take ga wanda suka tuba, Allah mai gafara ne ga bayinsa Indai sunyi tuban tsakani da Allah.
Sannan maganan auran farhan da haulat babu fashi sai ki Fara shiri, wannan shine hukuncin Mai sabon Allah, gashi Allah ya jarabci d’anki da yarinyar da kukai lalata da ita.
Hjy habiba kuka take Sosai, lallai tasan wannan jarabta ne, da wani ido zasu dinga kallon juna ita da sirikar tata? Kai kai kai matar d’anta Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, lallai taga ishara, amma babu yanda zanyi dole In amshi kaddara domin bijire ma Abun in Allah yasa akwai rabo Zan iya rasa raina akai, bai kamata inyi jayayya da abunda uban giji ya tsara ba.
Hjy habiba ta amince Ayi auran farhan da haulat, Amma kullum tana cikin tunani irin kallon da zasu dinga yima juna
Hjy Umaima ce kwance ita da jamcy, suna ta faman cin juna, tare da tsotse tsotsen iskancin su, Bayan sun gama ta kalli jamcy, tace Kai kin tsallake Rijiya da baya, jamcy tace ai yaron hjy habiba ko dan iska, sai yasa ni yanzu inba keba bana yarda Inbi ko wace mace gida, sai dai ta Kama mana hotel, wayan hjy Umaima ne yayi k’ara d’auka tayi taga habib ne, ban San mai yace mata ba, naji tace dagaske Bariki ta koma gidan mijinta? Ban San amsan daya bata ba, naji tace ka tabbata malamin aikinshi nayi? Toh karka damu gobe da safe zan tawo kaduna.
Kaman yanda hjy Umaima ta tsara zuwa kaduna hakan ya faru, ita da jamcy suka Kama hanya, aiko sun zo wajan jere wata babban mota ta bugi nasu, nan motarsu ta Fara kifawa tana juyawa, motar ta bugi wani dutse ta tsaya a wajan, nan mutane aka taru tare da kiran police da ambulance, aka fara k’okarin ciro su hjy Umaima, amma koda aka ciro su hjy Umaima rai yayi halinshi, driver dinma shima Allah ya mishi rasuwa, jamcy ce take numfashi itama rai a hannun Allah, ko Kafin su k’arasa asibitin itama Allah yayi mata rasuwa, Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, kai rayuwa ba komai bace, hjy Umaima ta fito da niyan shairi zata wajan boka, zata ta aikata shirka, gashi Allah ya amshi rayuwarta, ba tare data nemi gafaran Allah akan laifin data aikata ba, kai duniya ba komai bace, sai dai Allah gafurul rahim ne, ba’a shiga tsakaninshi da bayinshi, Allah kasa mu cika da imani yasa muyi kyakyawan karshe.
Lokaci kad’an labarin rasuwan hjy Umaima ya bazu ko ina, hjy habiba taci kuka Sosai, koda labari ya riski habib budan bakinshi yace za’a sha kwairi domin an aikata Abun tsiya, Hmmmm Allah ya kyauta, mutuwa dai ance wa’azi ce, Amma habib ko alaman nadama babu ko tausayawa alaman yayi nisa.
An fara hidiman bikin haulat da farhan, Zainab taso taje amma Yarima ya hanata, dole ta hakura, anyi bikin farhan da haulat lafiya inda suka tare a sabon gidansu, haulat tana bama hjy habiba girma Sosai, hjy habiba tun tana d’ari d’ari harta dan saki jiki, sai dai abunda suka aikata kullum yana damunta Hmmmm Allah yasa mu dace, wannan abun kunyar har Ina
Bayan wata shida Hafsat ta haifi d’anta namiji santalele Mai kyau, wani ikon Allah Sai yaron yayi sak babanshi Umar, ranan hafsat taci kuka sanda taga yaron, iyayen umar suma sunci kuka, nan aka ma yaro huduba da Umar sunan babanshi.
Yarima Aliyu sun tare a gidansu na kaduna, Cikin Zainab yayi girma haiyuwa yau ko gobe, tana zaune a falo daka ita sai wata doguwar riga irin ta roba dinnan domin kayanta basa shigarta, irin rigan da take sawa yanzu kenan, kanta babu d’ankwali, tasa kankana a gaba tana ta sha, daka gani cikinta ya cika amma sha takeyi tana nishi kaman dole, Yarima ne ya shigo cikin falon kallonta yayi ya girgiza kai yanda take tusa kankana din, d’auke plate din yayi yana fad’in oh my princess ki barshi haka mana,
Tace Yarima plz ka bani insha, yace Nop ya isa haka, d’agota yayi tare da fad’in bari in gaisa da baby d’ina, tsugunnawa yayi tare dasa kunnenshi a cikinta, dariya ta saki Tana kallonshi
Lokaci d’aya ya fara magana hello baby, is ur Dad, wen r you coming to d world?
Bariki dariya tayi tare daja baya tana k’okarin zama, lokaci d’aya ta saki kara mai sauti tare da ri’ke cikinta, da sauri Yarima ya nufeta, ganin yanda takeyi yasa ya nufeta da sauri tare da ri’keta, kamata yayi suka fita yasa ta a mota, dai dai lokacin zinatu ta shigo gidan ganin haka itama ta fito daka mota ta bisu, direct asibitin Yarima suka nufa, suna zuwa akai labour room da ita, Yarima saboda sauri ko kayan haiyuwa ba’a d’auko ba, dole zinatu ce ta koma ta d’auko, Yarima shi kadai Ya shiga ansar haiyuwar Princess dinshi, ganin yanda take ihu da kuka ya kasa tabuka komai, dole fita yayi ya kira wata Dr akan ta amshi haiyuwar Zainab dinshi domin bazai iya juran ganinta Tana wannan halin ba,.
Cikin minti 30 da fitan Yarima bariki ta sintibo d’anta namiji kyakyawa kaman Yarima Aliyu, sai dai farin na Bariki ya d’auko, nan aka gyara yaro da Mai jego, Yarima tunda yaji ihun jariri yasan ta haiyu amma ya kasa shiga saboda tsoro, hahahaha kunji Yarima fah shida yake ansan haiyuwar wasu amma ya kasa amsar na his princess saboda tausayi .
Saida Dr ta fito tana fad’in congratulations Dr Aliyu matarka ta haifi baby boy, saboda murna da sauri zinatu ta rungume Yarima Aliyu, tare da sakinshi lokaci d’aya, tun Kafin Yarima ya shiga zintau ta shiga Tana taya Zainab murna tare da d’aukan baby tace Kai lyk father lyk son, Shigowan Yarima Aliyu yasa ta mi’ka mishi Yaron tare da fita danta basu daman magana, Yarima kallon yaron yayi tare da fad’in Masha Allah, lokaci d’aya ya nufi gadon da Bariki take kwance hannunta ya kamo tare da fad’in sannu my princess, ganin bata kulashi ba yasa ya tashi yaje ya kwantar da baby din, tare da dawowa, yace my princess talk to me, d’agota yayi tare da zaunar da ita hawaye ta Fara, ganin haka Yarima ya rud’e ya fara tambaya lafiya? Tace Yarima gaskiya bazan kara haiyuwa ba, nasha wuya, maganan da tayi yaba Yarima dariya, suna cikin haka saiga mum da hafsat Sun zo, Yarima saida Ya gansu yama tuna bai kira ya fad’a musu ba, mum tace wato saida aka haiyu shine aka kiramu koh? Hafsat d’aukan baby din tayi tare da fad’in wow kaman bros, Zinatu ce ta kira su mum, nan itama mum ta d’auki baby din, suna cikin haka saiga Fatima yayar Yarima tazo itama, Bariki kam kunya take taji, Yarima kam gashi Abu kad’an ya janyota jikinshi ga mum a wajan, ta rasa yanda zata mishi yabar tabata dariyan Ya’ke kawai takeyi,ga zinatu itama ta shigo, ganin babu wani matsala da yamma suka dawo gida, inda Mum tace a ZARIA za’ayi taron suna, dan haka suka had’a kaya suka nufi Zaria