DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Babu musu tatashi, kai tsaye dakin Momy suka tafi, tayi wanka sannan taci abinci, Momy tasa ta ta kwanta, ta qara mata karfin esi sannan takashe mata wutar dakin tafita zuwa wajan Daddy

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari daqyar tasamu taci abinci, idan tatuna Diddi saitaji wani irin abu yatokare mata maqoshi, daqyar taci kadan ahakan ma saboda Momy ta tsareta ne

Cikin murna tashigo part din nasu da gudu tana kwalawa Momy kira “Momy! Momy!! Momy!!!”

Cikin sauri Momy ta kalli wadda tashigo part din nasu, kafin tayi mata magana yarinyar tace “Jiya Ummah tah tace Nihla tazo, Momy tana ina?”

Murmushi Momy tayi “ilham, Nihla tana dakina, jeki sameta”

Dasauri tashige dakin Momy, a lokacin Nihla tana kwance tana tunanin Diddi, sai jin mutum tayi a jikinta, Dasauri ta kalli wadda tashigo din, kyakykyawa ce sosai wadda ake kira da choculate beauty, ahankali tatashi zaune tana cewa “wash Allah, zaki karyani”

Cikin murna dayar tace “to murna nake ance kinzo, duk bamu sanki ba, kema baki sanmu ba, nide sunana ilham, dama ummah na tana cewa kina kama da yayata Aisha, me sunan Diddi, kuma yau nagani, wallahi kina kama sosai da ita”

Murmushi Nihla tayi “dama kece ilham? Ai duk Diddi tana bani labarin ku, ina Aishan take?”

“tana India, amma ta kusa dawowa, meyasa kika zauna a daki ke kadai bakya tsoron kiyi tunani?,”

Ajiyar zuciya tasaki “nayi karatu ne kuma nagaji, shine nake Dan hutawa, ya karatu?”

Fari ilham tayi da idonta “ai nayi candy, ke dukanmu munyi candy, saide tagaba insha Allah”

“nima nayi candy har na karbi result dina,”

Kafin ilham tayi magana Momy tashigo dakin tace “Nihla tunda ga ilham tazo kuje ta tayaki ki gyara dakin naki ko?”

Ilham tace “eh wallahi zomuje”

Dakin dayaji furnitures da Komai launin green suka fara gyara wa, ilham tafara wanke mata toilet, sannan suka goge kayan dakin, tareda yin moppinga, Nihla tanata yabon halin ilham cikin ranta, babu ruwanta faram faram

Dasuka gama gyara wa zama sukai anan kowa tadau wayarta suka hau Xender suna tura abubuwa

Sallama sukayi suka shigo dakin susu biyu, kana ganin su kasan gidansu daya saboda kama dasuke da juna, daya tana sanye da riga da wando dasuka kamata sosai, gata da uban hips masha Allah,dayar kuwa norml kayane a jikinta, kana ganinta kasan silent ce, me riga da wandon ce ta d’akawa Ilham duka abaya
Sannan tazauna

Ilham tace “haba Diyana, irin wannan daukan ai saiki budamin qirjina”

Zama sukayi suma akan gadon, wadda aka kira da Diyana ta kalli Nihla “haba haba Nihla, wannan hijabin fa, Kamar bakyajin zafin duniyar nan? Kinci wani uban hijabi Kamar matar liman haba be wise mana”

Murmushi nihila tayi tana kallanta, yanda taci wannan riga da wando aidole tayi fada akan hijabi ????
Wadda batayi maganar ba tace “Nihla sannu da zuwa kinji, kirabu da Diyana, idan kina neman mace Mai shegen son maza to Diyana ce” ????????‍♀️

Kallanta Diyana tayi “to Dida idan banso maza ba mata zanso?????

Dida tace “kide rage wallahi, ai a yimaka shedar arziki ma abu ne Mai kyau”

Tashi tayi tsaye, batama kalli yar’uwar tata datayi mata magana ba, tace “Nihla, natafi, saina sake dawowa kokuma inkin shigo, ai zaki zo ko?”

Nihla tace “Zan shigo Diyana, nagode “

Ilham ta kalleta, “sai ina kenan?”

Kai tsaye batare da tantamaba tace “wallahi unguwa zamuje nida wani cika ????????‍♀️, yanaso zaiyi birthday zamuje mufara shirin komai, danya takura ne ma wallahi banso zuwaba”

Nihla ta kalleta cikeda mamaki anya kuwa Diyana kalau take? ????

Dida tace “ke dince zakice antakuraki? Keda yawo? To idan baki bishi ba ina zakije?”

Babu alamun damuwa tacewa qanwar tata “Dida nadade kema kinsan dadade banje nigh Club ba ????, wallahi nan nakeso naje”

Wannan karan kam Nihla daria tasaka ????
Al’amarin Diyana akwai kallo, kuma duk maganar datake yi hankalin ta kwance, zuciyarta daya take magana

“Ilham tace” to saikin dawo, idan Nihla zatazo Zan rakota masha fira “

Tace musu ” ok” sannan tafice

Dida ta kalli Nihla tace “haka take wallahi, Karki yi mamaki ????, mune yaran Anty Farida, itace babba ninake binta, kuma wallahi Mom dinmu tasani amma tazuba mata ido, tana zama idan ta tsarata shikkenan sai kiji shiru”

Murmushi Nihla tayi, tace “Diyana kenan” sannan sukaci gaba sa firarsu gwanin sha’awa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari Ilham ce tasake dawowa taja Nihla zasuje ta nuna mata kowanne part na gidan, part dinsu suka fara zuwa
Hajiya Abida tana ganinta ta karbeta hannu bibiyu, tana tausayin yarinyar sosai, taso Aisha Wato Diddi, hakanne yasa ta sakawa yarta suna Aisha, kuma ganin Nihla tana kama da Aishanta saitaji dadi, sai nan nan take da ita, sun dade sannan suka futo
Ji tayi taci karo da mutum, Dasauri tadago kanta taganshi a tsaye abakin kofar part din shima zai shigo, dogo ne fari, saide bakinsa dayayi baqi, alamun yana shan wani abun????,yaraba gashin kansa biyu yasakawa Rabin colour Mai launin yallow, dayan gefen kuma yabarshi yanda yake, hatta Dan gemun daya tara irinna samari yan gayu shima yasaka masa kala,ga wani uban bluetooth daya toshe kunnuwansa dashi, da alama waqa yakeji, kana ganinsa kaga tantiri na gaske, ahankali tace masa “ina wuni?”

Yace “normal ne, Nihla ko?”

Tanajin irin Tambayar dayayi mata jikinta yayi sanyi, ahankali ta daga masa kai kawai

Yace “okey kihuta”
Yana fadar haka ya shige ciki ????

Ilham taja hannun ta suka futo ta kalleta sannan tace “wannan shine yaya fawaz, shine Babban yayanmu, dagashi sai Aisha saini, Tun suna yara yake kula abokan banza har suka koya masa shaye-shaye, babu irin qwayar da baya sha, Tun su ummah suna fada har sun gaji sunyi shiru

Nikuma kinga banaso naga abinda akeyi nayi shiru, kokuma ban shiga sabgarka ba ka shiga tawa, to Zan rama ne, shiyasa Tun muna qanana ake cewa nafi kowa rashin kunya.

Nihla tace “kai wannan gida kuna abinda kukeso wallahi” ????

Part dinsu Alhaji Baqir sukaje “hajiya na’ila ta amsa musu cikin sakin fuska, amma aboye hararar Ilham take, saboda yarinyar batayi mata ba kwata kwata ????

Daga cikin dakin hajiyan yafuto da car key ahannun sa, yana sanye da manyan kaya riga da wando na wani yadi, ya kalli hajiyan yace” mama zanje school inada lacture da yamma “

Tace” to adam saika dawo “

Ilham tace” yaya adam ina wuni”

Sai lokacin yakula dasu, cikin farin ciki yace “a a Kamar Nihlan Diddi”

Daria sukayi, Nihla tace “nice wallahi”

“A a masha Allah, sannu da zuwa”

Tace “yawwa”

Fita yayi daga falon, basu jimaba suma suka fice, Ilham tace “wannan shine yaya Adam,duk Mazawaje family shine ustazi, idan kina neman alaramma kikazo wajansa to kingama samu????, lacturer ne, yana koyarwa a yusuf maitama, Wato northwerst, yayansa yana germany shida yaya Abba Wato Aslam, su biyu ne a part dinsu

Nihla tace “Allah sarki, aikuwa Babu ruwansa bawan Allah” ????

Part din qarshe sukaje kafin su shiga Ilham tace “wannan shine part dinsu Diyana da Dida, maman su tana auren dan’uwanmu ne na family shiyasa taci gaba da zama agidan nan, basu bar family house ba, tana son yaranta sosai, batasan abinda zai tabasu
Kuma ayanda ummah take fada mana hajiya Farida Maman su Dida tana shiri da baban ki sosai”

Nihla tace “hakane kam, nima nasani Ilham”

Part din suka shiga, nanma Babu laifi sunsha fira da Dida, Dan Diyana bata nan ????, sannan suka futo kowa ya koma part dinsu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button