DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Dasauri tafuto daga dakin zuwa falo, hajiya Farida taji alamun gudu, tace to Dida ko lafiya?

Dida kuwa kofar falon tabude tafuto wajansa tace “mekake yi hakane eh? Sai mura takamaka ko?, kawuce katafi gida”

Fawaz yanajinta yayi shiru, kuma still yana tsaye awajan bai motsa ba, Kamar marar gaskiya haka ta kalli gabas ta kalli yamma taga Babu kowa awajan saisu kadai, Sannan tafuto cikin Ruwan itama ta nufeshi, jikinsa tashiga girgizawa tana cewa “ya Fawaz katafi gida, kar zazzabi ya kamaka”

Wani irin dadi ne yakama Fawaz, ko banza yau Dida ta kula dashi, cikin sauri ya fusgota jikinsa ya rungumeta tareda hade bakinsu waje daya, tureshi tafarayi amma saiyasa dayan hannunsa yariqe waist dinta, dayan kuma yariqe kanta yana kissing lips dinta sosai

Hajiya Farida tafuto falo taga Babu kowa, cikin mamaki tace to waye kuwa yashigo naji Kamar ana gudu
Labulen falon ta janye tabude window anan idonta yasauka akan Dida da Fawaz da ruwa yagama jiqesu suna kiss, cikin sauri tarufe window din tana salati, da mema yakai ta dube dube? ????

Saida yagaji Dan kansa sannan yasaki bakinta yace “I’m sorry Dida, please forgive me, nayi miki alqawarin nadena komai, Allah da gaske”

Shiru tayi, takasa cemasa komai, ganin haka yasa yaja hannunta yace “zomu tafi gidanmu”

Hannunta ta fizge tajuya zata koma ciki, ganin abinda take shirin yi yasa yadauketa cak yayi wajanda motarsa take yasakata aciki sannan yashiga yatada motar, megadi yabude masa, yafice daga gidan

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Books ne agabansu masu yawa, duk na addini ne, yanayi mata bayanin su dalla dalla, littafin hannunsa na iziyya har sun danyi nisa aciki, yana sake yimata bayani dangane da hukunce-hukuncen tsarki da kuma abinda ya wajabta ayi tsarki, dagashi sai jallabiya amma tsabar yanda yadage yanayi mata bayani yasa jallabiyar ta tattare daga qasa kana ganin gajeren wandon dake jikinsa ????

Ita kanta dalibar tasa, wani shegun riga da wando ne a jikinta, gaban rigar abude kana iya hango albarkatun qirjinta awaje
Kallanta yayi yace “maryam kina ganewa kuwa?”

Matsowa tayi jikinsa ta leqa cikin littafin tace “eh ina ganewa”

Idonsa ne yasauka akan qirjinta yazuba musu ido yakasa daukewa, tana ganin haka tayi Murmushi cikin ranta
Afili tace “ya Adam!”

Firgigit yayi, yadawo haiyacinsa, yana sakin ajiyar zuciya yace “yawwa kina ganewa ko?”

Murmushi tayi tadan kwanta ajikinsa cikin dabara, tasaka hannunta akan littafin dake hannunsa tace “Amma nan wajan bangane fassarar saba ya Adam, kasake min bayani kaji”

Kallanta yayi yaga yanda ta kwanta ajikinsa, gashi ta dora masa qirjinta agefen nasa qirjin, yanaso yayi magana amma yakasa, hakanne yasa yayi shiru tare da lumshe idonsa, baiqi ace sun tabbata ahaka ba shida Maryam, tanada tarin baiwa dayawa yarinyar, dukda yasan cewa wasu gayun sun rigashi

Kallansa Diyana tayi cikin rada tace “ya Adam kawai ni nagaji ma abar karatun sai gobe, yanzu dare yayi sosai”

Idanunsa a lumshe bai iya bata amsa ba, sai kansa daya daga mata kawai

Mamaki yagama kashe Diyana, tarasa gane kan ya Adam, har yanzu Yaqi futowa fili ya nuna mata yanda yakejinta aransa, to kode har yanzu duk wannan Jan hankalin nasa datake yana nufin yace bai fara sonta ba?, ko yaya idan tahada jikinsu baida aiki saide ya lumshe ido amma har yau yakasa baiyana mata yanda yake sonta, aikuwa inde hakane tadinga gasa masa aya a hannunsa kenan harsai ya furta mata kalmar so, bazai iyu tadinga yin abu da jikinta da kalaman ta amma yanata basarwa ba, zataga qarshen basarwar tasa.

idonta abude suke tana tunani tana kuma kallansa yanda ya lumshe ido, tana dariya qasa-qasa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda suka shigo gida take ta masa kuka ita yamaidata gida

Kujerar datake kai yazo ya tsugunna a gabanta, yadora hannunsa akan cinyarta yace “Baby Dida, rigima kikeji ko? Kinga fa ruwa ake, kibari gobe saina maida ke gidan kinji?”

Cikin kuka tace “ai nasan ba maidani zakayi ba”

Yace “a a, zan maida ke, bakisan banason abinda zaisa ranki yabaci ba?”

Dago kanta tayi tace “kuma shine kakeyi ba” sannan ta maida kanta qasa tana kuka

Murmushi yayi yace “to naji, kuma nadauki laifi na, inde shan kayan maye ne yakesa ranki yabaci ni wallahi nadena”

Tace “ai rannan ma haka kace”

Girgiza kansa yayi yace “Dida! Wallahi da gaske nake, idan kika sake kamani inasha nayarda ki dauki kowanne irin hukunci ne akaina amma banda yin nesa Dani, kinji?”

Daga masa kai tayi batare datayi magana ba

Yace “yawwa, to kokefa, tashi Muje kiyi wanka, kicire wannan kayan, kinga duk sun jiqe”

Tashi tayi batare da tace masa komai ba tashige dakinta, shikuma yabi bayanta da kallo yana ganin yanda surar jikinta tafuto acikin kayan sakamakon jiqewa dasukai, haqiqa ya yarda cewa a yanxu kam yanason Dida, tunda haryakejin yanayin jikinsa yana sauya wa akanta

Washe gari dasafe dakansa yadauki Dida suka tafi asbiti wajan wani doctor yayi masa bayanin matsalar sa

Likitan yabashi shawarwari akan yanda zaiyi Yaqi da shan miyagun qwayoyi, Sannan kuma ya dorashi akan wasu magungunan, Wanda zai dinga sha koda shaye-shayen dayayi abaya sunyi masa wata illar batare daya saniba

Haka suka dawo gida cikeda farin ciki, babu wanda yakai Dida murna, yau ya Fawaz yadena shaye-shaye, haka al’amarin yaci gaba da kasancewa, Inda kwanaki suka qara ja, lokaci yana qara wucewa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Takardu ne a gabanta na handout, banda books manya manya dake jere a gabanta

Karatu take sosai, hankalinta kwance, dinkin doguwar riga ne a jikinta na atamfa, kanta Babu dankwali, hakan yasa dogon gashinta kwanciya agaban qirjinta kasancewar gaba tawatso shi

Turo dakin nata akayi a kashigo, amma bata daga kai ta kalli kofar ba, saboda tasan cewa Babu me shigo mata daki inba mamy ba

Saide kuka qamshin turaren dataji ne yasa tadago kanta Dasauri, Idanunsu ne suka hadu, lokaci daya murna ta baiyana a fuskarta

Tace “ya Yusif!, Dan Allah kaine? Yaushe kadawo?”

Murmushi yayi Yazauna agefen gadon, daga wajan qafafunta, yace “zanyi miki Surprice ne shiyasa nace kada afada miki yau zanzo qasar, but Dafarko dai ki sanar Dani me kikeci kika koma haka?, Nihla idan na ganki ahanya fa daqyar Zan iya gane ki, anya kece kuwa?”

Murmushi tayi tace “Allah ya Yusif kaganka ko? Nide bari na kawo ma ruwa”

Tana fadar haka tatashi daga kan gadon ta nufi fridge din dakin domin kawo masa ruwa, Yusif yabi bayanta da kallo yaga yanda hips dinta yake rawa acikin kayan, gaba daya Nihla ta sauya masa, acikin wannan ‘yan shekarun takoma haka, kokuma danya dade baiganta bane? ????
Komai yaqaru ajikin yarinyar Kamar ba itaba, lalle dole yadinga kaffa-kaffa da’ita Tun kafin wani gayen yayi masa qafa ????

Yana wannan tunanin takawo masa ruwa da lemo ta ajiye masa, shide sai binta yake da kallo harta farajin kunyar kanta, zama tayi tace “ya Yusif ya hanya, Yaya kabaro china?”

“china tanacan Nihla, na kawo miki tsaraba Mai yawa harda kaya, but nasan may be suyi miki kadan, dannaga yanzu masha Allah, kinzama Babbar yarinya”

Murmushi tayi tace “a a fa ya Yusif, bawata Babbar yarinya nide”

Yace “kina zaune adaki ke kadai, ko tunani nama bakyayi ko”

Tace “ya Yusif kenan, tayaya Zan kasa tunaninka, kawai de karatu ne yamin yawa shiyasa, kaga munata shirye-shiryen rubuta exam din qarshe, yakamata na maida hankali akan karatu kozan samu sakamako Mai kyau, shiyasa duk nashiga damuwa ina zama adaki ina karatu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button