DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Momy tayi Murmushi tace “tana wajan Yayan ta”

Abba ya kalli Nihla yace “to kinji tana wajan Daddy kije kiyi sauri ki karbota mutafi”

Momy ta girgiza kanta tana murmushi, sai sauri yake Kamar Wanda zasu je wata qasa akace jirgi zai tafi Babu su ????

Daddy yafuto daga dakinsa hannunsa dauke da yarinyar yace “hajiya wannan qanwar tawa tacika kuka”

Momy tace “haka take Alhaji, da rana tasha baccinta da daddare kuma mu ta hanamu sakat”

Daddy ya kalli idon yarinyar yace “toki daina, danni ba haka Aisha na take ba”

Gaba dayansu sukai dariya, Nihla ta karbeta, su kayiwa su Momy sallama suka tafi gidansu

Awannan dare Nihla tasha baqar wahala awajan ya Abba, domin kuwa Tun ana abu na marmari saida ya Abba yasa tafara kuka, sannan ya’iya hakura, amma badon yasoba

BAYAN SHEKARA TAKWAS

Zaune suke afalo suna yin game atv, gaba dayansu hankalin su yanakan game din, Acan gefe kuwa wani Yaro ne yana zaune yana kallan abinda sauran yaran suke

Little Diddi na gefensu tana wasa da teddy ahannun ta

Remote din lil Fawaz yayar aqasa yace “natafi wajan mata ta” ????

Yayi wajan Little Diddi

Yanbiyu ma dasuka ga haka sukai wajansa da gudu kowa yana cewa matar sa ce

Lil Adam yaron Dida yace “ai gidanmu zaki dawo ma ko?”

Tajuya ta kalleshi kafin tayi magana lil Fawaz yaron Diyana yace “a a gidanmu zata koma”

Shima tajuya ta kalleshi, duk sai kallansu take tarasa wazata yiwa magana duk sun sata agaba

Wancan na zaune agefe shi kadai shine yataso yazo wajan su yace “duk ba Inda zataje, gidanmu zata tafi” ????
Ya kalleta yace “ke Little Diddi gidanmu zaki tafi gaba daya, kuma nine Zan aureki, kinga nine takwaran Daddynki” ????

Abba da Nihla dake zaune akujera suna kallan yaran sukai murmushi, hijabi ne a jikinta ya Abba yatura hannunsa cikin hijabin ya shafa qirjinta

Kallansa tayi tace “ya Abba kayi ahankali fa ga yara nan”

Murmushi yayi yace “bakiji abinda suke fada bane? Kitashi Muje daga ciki anema musu wata Ayshan shikkenan kin raba fada” ????

Tace “um um, sutafi Abuja wajan ya Yusuf yabasu Mai sunan Mamy”

Yace “a a, gara de kema ki haifo musu wata yar budurwar Karki hadasu fada” ????

Hannunsa ta cire daga kan qirjinta cikin shagwaba tace

“ya Abba Allah zakasa yaran nan sugane fa”

Murmushi yayi yace “to Muje nakoya miki wani abu” ????

Murmushi tayi ta rungume mijinta, shima yasaki daria cikeda farin-ciki

Tammat Bi Hamdullah

Anan na kawo qarshan wannan labari Mai taken DANGI DAYA

Gaskiya tunda nake rubuta labari bantaba shan wahala ba Kamar yanda nasha acikin wannan littafin, saboda soyaiya ce data rabu gida gida kuma kowanne gida da irin nasa salon,dakuma irin nasa soyaiyar, babu wanda yaci karo da irin soyaiyar wani

Haka kuma duk cikin books dina Babu Wanda nasamu qarancin Comments Kamar sa, bantaba rubuta littafi nace Zan ajiye shiba sai akan DANGI DAYA saboda qarancin Comments
But Babu damuwa kowanne labari da irin nasa farin jinin

Amma abin mamaki shine bantaba tunanin inada masoya ba sai akan novel din DANGI DAYA ta yanda ina bude page a facebook masoyana suke ta ruruwar Like din page dina, Alhamdulillah mun fara labarin DANGI DAYA da mutum dari da hamsin mungama shi da mutum dubu biyu dawani abu, gaskiya naji dadi Babu abinda zance da masoyana sai godia,domin kuwa nagane ni akeso ba novel dina ba.

Dangane da al’amarin rayuwa nayau da kullum shima mun tabo matsalolin da ake fama dasu Awannan yanayin kuma mun fadi maganin su, misali magungunan da aka fada acikin labarin

Idan kuma labarin Rayuwar ki yayi daidai da irinna wannan ma’auratan, to ina fatan zaki samu solution acikin littafin DANGI DAYA.

Idan akwai wanda na batawa Sanadin wannan labari, yayi hakuri yayafemin, nikam na yafewa kowa,daga qarshe ina fatan duk masoyan Amnah El Yaqoub su kasance DANGI DAYA ????????

Amina Muhammad El Yaqoub jigawa state ✍????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81

Leave a Reply

Back to top button