DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Momy tace “Nihla ga yayanki yashigo fa, shima baya qasar yanzu yanzu yadawo, yaude ina cikin farin-ciki yarana duk sun dawo gabana”

Hankalin Nihla yana kan cup din gabanta, ko dago kanta batayi ba, bare yasaka ran zata kalleshi, kanta aqasa Kamar anyi mata dole tace “ina yini”

Ataqaice yace “lafiya”

Sannan yayi gaba, yajuyo yasake kallanta waiko zaiga ta kalleshi amma yaga gaba daya hankalinta ma baya kansa, shi wannan yarinyar zata gaisar asheqe Kamar ta samu sa’anta?

Momy kuwa tayi mamaki guda daya, mamakin daya kamata shine yanda Nihla taqi ambatar ko sunan Abba, da tasaba tanaji yarinyar tana ya Abba kaza, ya Abba kaza, duk da yana shareta bata fasa fadar sunansa ba, Kamar a bakinta aka rada mata sunan ya Abba, amma yau taga gaisuwar ma daqyar tayi ????

Dakinsa yashige yafada kan gado yana tunani, inaaa! Bazai iyuba, Sam bayason raini, Dan haka bazai dauki wannan ba, lumshe Idanunsa yayi, meyasa yake jin farin-ciki ne awani bangare na zuciyarsa?

(ko a film fad’an boss shine qarshe ????dafatan za’a min Comments ????????)

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/3, 12:43 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

33&34

Nihla ta kalli Momy “Momy kibani wayarki nakira su Ilham, banda number kowa acikinsu”

Momy tace “wayarki tada tana nan a dakin naki, ki kunna saiki dauka, ai Babu wadda ta sauya number acikinsu, nima Bari nakira Daddynku dasu Usman nafada musu zuwanki”

Tace “to Momy” sannan tashige dakinta

Da daddare kuwa su ya Usman sukazo dukansu, dama Momy tasa Adala ta shirya musu abinci Mai kyau

Alokacin Nihla tasake wanka tasaka riga da siket na atamfa Mai launin Jan duhu, dinkin yayi mutuqar yimata kyau, siket din kuwa hips dinta yacikashi dam, daurin dankwali nede tayishi simple amma gashinta awaje yake daga baya

Babu Wanda bai rude ba, lokacin dasuka ganta, gaba dayansu suna zaune acikin qayatattun kujerun dakin, Adala kuma tana dauko abinci daga kitchen zuwa kan dining, firarsu suke cikeda farin-ciki but Abba kam baya saka musu baki, baya cewa um bare um um, asali ma waya ce ahannun sa yana danne-danne, yayinda yadora kafa daya kan daya

Farouq yace “Momy, yarki fa tagama rikicewa, gaba daya ta sauya kamar ba ita ba, ni sai yanzu nema nakejin naqara matowa, inba itaba sai rijiya” ????

Ahankali yadago kansa ya kalli farouq, amma Bece masa komai ba

Murmushi Nihla tayi, har dimple dinta yana lotsawa, tace “ya farouq bakada dama, aina fadama dakai za’ayi, tunda kaji sharadin”

Wannan karon ma tana fara magana Abba yadauke idonsa daga kan farouq yadawo dashi kanta, har yanzu de wannan dimple din nata yana nan, yayi tunanin zata kalleshi amma kwata kwata saiyaga ko kujerar dayake kai bata kalla ba

Aliyu yace “ai farouq, bazan baka qanwata ba, mijinda Nihla zata aura ai sai Wanda duniya tasan dashi”

Usman yace “Kamar ni kenan” ????

Gaba dayansu sukasa daria, Momy tace “Dinner is ready kutashi Muje kowa yaci abinci”

Usman da farouq da Aliyu gaba dayansu ajere suka zauna, Momy ma tazauna akusa da Usman, kujeru biyun dasukai saura kuwa na Abba ne da Nihla, hankalin ta kwance taja kujerar tazauna sannan tafara cin Abincin ta, shima Abba daya qaraso wajan yaga saura kujera daya ta kusa da Nihla, haka yaja Yazauna, idonsa akan wayarta data ajiye a gabanta, yana zama wani irin sihirtaccen qamshi yabugeshi, baisan lokacin daya lumshe idonsa ba yabude, kowa shiru yayi yana cin abinci, wayar Nihla tafara qara, kowa yazuba mata ido yana Kallanta, Abba yakai dubansa kan screen din wayar yaga ansa
❤my Yusif❤ harda alamar hert ajikin sunan, Nihla tasa hannu tasaka wayar a silent, idonsa ne yasauka akan kyawawan yatsun hannunta, dogaye gwanin sha’awa, janye idonsa yayi, Nihla kuwa ko a jikinta taci gaba dacin Abincin ta, ana jimawa ya Yusif yasake kira, tasake sakata a silent, akaro na uku ma yasake kira, ahankali ta miqe tsaye tace “Excuse me, zan amsa waya”

Tana fadar haka ta nufi hanyar dakinta, Hips dinta Abba yabi da kallo, anya kuwa yarinyar nan itace bawani abu take sakawa a jikinta ba? gashi sai yawo take tana fitarda gashinta waje kowa yana kallo, amma Momy tana gani ko magana bata taba yiba

Har suka gama cin Abincin Nihla tanacan tana waya, da dade tana shan wayarta dashi sannan tafuto sukai sallama dasu ya Aliyu

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“ku shikkenan idan akace anyi muku aure, ankai muku amarya daki saiku rasa control dinku gaba daya, tayaya za’ayi daren farko kace zaka shigi mace gaba daya, shiyasa mutanan da sukafi mazan yanzu iya zama da mata, da kanku kukesa matanku suna tsoron ku, yanzu saboda Allah wannan dame yayi kama? Kaja anyiwa yarinya dinki, tayaya kake tunanin zata sake yarda dakai akaro na biyu? “

Adam yayi shiru kansa aqasa, ko yayiwa doctor bayani bazata ganeba, gara yayi shiru tagama fadanta kawai, ahankali yadago kansa ya kalleta, matar kam babba ce zata iya haifansa, shiyasa Babu kunya baro baro take masa fada, yace” insha Allah Zan kiyaye gaba likita “

Fuska a cukune tace” to dade yafi muku, narubuta muku magunguna kasata agaba tadinga sha, sannan karka sake zuwa wajanta sai nanda yan kwanaki “

Kansa aqasa yace” to insha Allah “

Daga nan yafuto daga office din nata yaje wajan Diyana daya tarar tana bacci, baiyi kokarin tashinta ba, yabarta tagama baccinta sannan tatashi Dan kanta, yakamo hannunta da kafadarta suka futo daga asbitin, saida yasai magungunan da aka rubuta musu sannan suka wuce gida

Dakinta tashige ta kwanta tana tunani, dama haka daren farko yake? Ahakan wasu suke cewa sunason daren farko? Wannan aiba abin dadi bane abin wahala ne kawai, har akan wannan abun wasu matan suke fada? Har wasu sukai kansu ga aikata zina, tabdi, ita kam, itada ya Adam danba qara

Dakin yaturo yashigo yakalli fuskarta tayi fayau, zama yayi agefenta yace “maryam kiyi hakuri, insha Allah hakan bazata sake faruwa ba”

Shiru tayi masa batare datayi magana ba, ahankali ya miqe yafara cire kayan jikinsa, gaban Diyana yafadi, me kuma zai sake yi? ????

Tsaf ya cire komai dagashi da boxer yahau kan gadon, cikin faduwa gaba tace “dan Allah kayi hakuri ya Adam,”hawaye ya silalo daga idonta

” ohhh Diyana, niba wani abu Zan miki ba, kawai inaso najiki ajikina ne “
Yana fadar haka yasa hannu yadaga mata hannayenta ya cire rigar jikinta, daga ita sai breziya ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsam, sannan cikin rarrashi yace “muyi bacci ko?”

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda suka dawo normal shida ita yakasa yimata komai, yasan cewa Dida mace ce Mai matuqar kunya bazata taba kawo kanta gareshi ba, to shi kuma kunya yakeji da girman sa yaje gun yarinyar mutane da sunan neman haqqin sa, amma azahiri yana matuqar buqatar matar sa, saide zaici gaba da haquri kawai har Allah ya yaye masa abinda yakeji, saboda yakusa sati kullum da ciwon mara yake kwana, amma be nuna mata cewa yanayi bama bare ta daga hankalinta

Magun gunansa suna hannunta, kullum itace take bashi saboda tana tsoro karta je Yaqi sha, idan lokacin shan maganin yayi saiyaje tabashi yasha

Yauma da azahar yashigo gidan, kai tsaye dakinta yashiga, a lokacin tafuto daga wanka tana zaune gaban mirrow tana kwalliya daga ita sai Dan qaramin towel

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button