DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Su farouq suka dawo gefenta suna bata hakuri, takalli Abba tace “duk abinda yafaru, laifin ka ne, Inda ace baka nunawa yarsa qiyayya ba, babu abinda zaisa Ibrahim yazo yatafi da ita, idan ma akan antaho da ita batare da sanin sabane to danaka laifin, na tabbatar labari yaj…j…ji” numfashi tane yafara sama

Anan maganar ta tsaya, numfashinta yana qara yin sama, cikin tashin hankali Abba yataso yacire Babbar rigar jikinsa yayi wulli da ita ????
Ya cacimeta yana kiran “Momy! Momy!!,”

Amma inaaaa, numfashinta ne kawai yake sama, qirjinta sai Dagowa yake, lokaci daya kuma, jikinta yasaki

Cak Abba yadauketa yadawo da ita kan gadon Daddy, farouq yadauko ruwa a fridge ya shafa mata, Usman kuma yafara kiran number family doctor nasu yace gashinan zuwa

Saida tadauki lokaci kafin ta farfado, tana bude idonta tafara kuka, Daddy yanaga yashiga tashin hankali ashe duk abinda yakeji Rahma tafi shi ????
Mamaki yagama kashe Abba, yanzu duk saboda Nihla suke wannan abun? Lalle ba qaramin so suke mataba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Sai yamma liss suka sauka, saboda Alhaji Isma’iel bayasan gudu, futowa sukai daga ciki motar, Yusif yasaki miqa yana fadin “wash Allah” idonsa akan Nihla

Mami tace “Yusif banasan wannan san jikin fa, to yanmata de basason rago, oya bude boot ka dauki kaya mushiga”

Yace “yanzu ni dinne rago?”

Murmushi tayi, ta kalli Nihla data shagala wajan kallan hadadden gidan, yanzu itace zatayi rayuwa acikin wannan gidan? Duniya kenan
Mami tace “Muje ciki Nihla”

Fuskarta Babu yabo ba fallasa tace “bari nadauki wata jakar mami”

Kusadashi taje ta tsaya, shi beyi mata magana ba itama haka, haushi yaqara kama Yusif, duk murnar dayake zaizo yaganta yaga yanda takoma amma shine tashareshi, ????
Cikin fishi yadauki jaka guda daya yamiqe zaiyi ciki
Dasauri ta tareshi tareda miqa hannu zata karbi jakar tace masa “kawo jakar”
Lokaci daya hannunsu yahadu dana juna, kallan hannunta yayi zanen qunshin da akayi mata yayi kyau sosai, Dasauri ya fizge jakar yace “no Barshi kawai”

Daga haka yayi ciki, sai wata tadauka acikin boot din tabiyosu ciki

Dakinda zata zauna mami ta nuna mata, sannan tashige ciki, anan taga babanta yana ciki, yana futo mata da kayaiyakinta na sakawa daga cikin jakarsa, cikin ranta tace dama de baba yagama shirya komai

Jakar yadauka yatafi Inda akayi masa masauqi daga can baya

Yana fita taga wayarsa ya mantata, Dasauri tadauka tasaka number Momy tafara kira

Acan kano kuwa gida duk ya hargitse yanmata duk sun shiga damuwa saboda labarin tafiyar Nihla, Ilham tafi kowa Baqin ciki saboda Babu abokiyar shawara antafi, Dan dole ake saka su abu su yi, yanzu ma wanka akasa ko wacce tayi domin anjima kadan za’akai kowa dakin mijinta

Apart din Momy kuwa kowa sai neman ta yake yarasa, tunda tashiga dakin Daddy bayan doctor yazo yagama dubata bata sake futowa ba, wayartace data Nihla a gefenta, adede lokacin wayarta tafara qara, Dasauri ta dauka tace “Ibrahim Dan Allah kayi hakuri, munsan munyi maka laifi amma kayi hakuri kadawo min da yarinyar nan” hawaye yazubo mata tasa hannu tashare

Kuka Nihla tafara tace “Anty kidena kuka nice”

Dasauri tace “Nihla kece? Kina ina, gida kuka koma?”

“Anty gida baba yadawo Dani, amma yanzu muna Abuja, mun tafi Abuja gaba daya da zama Anty”

Momy tace “Innalillah…Nihla banji dadi ba, banji dadin tafiyarki ba yata, kiyafemana kinji?”

Tace “Anty kidena neman yafiyata ba kiyimin komaiba, kedin Kamar mahaifiyata ce”

Momy tace “to ai kinji Nihla, kema kikace kama, ba kama nakeso nayi da mahaifiyar ki ba Nihla, sonake ki daukeni amatsayin mahaifiyar ki, ki kirani da Momy Kamar yanda ‘ya’yan cikina suke fadamin, ke dasu bakuda banbanci a wajena”

Jikin Nihla yayi sanyi sosai, bata taba sanin cewa Momy batasan Antyn datake fada mataba sai yau, ashe haka Momy take kaunarta? Wannan wacce irin soyaiya ce? Kasa magana tayi sai kuka datake sosai abaiyane

Alokacin baba yashigo yadawo daga masallaci kenan, tana ganinsa takwashe wayar, idonta jajir, tana share hawaye

Zama yayi agefenta ransa abace yafara magana “ke saboda rashin hankali, da hauka dayake damunki zaki zauna kinawa mutumin dabai damu dake ba kuka,? idan akayi muku auren waye zai wahala bayan ke?
Anayi wa mace auren dole kuma tayi hakuri tazauna din, amma namiji karkiyi tunanin lokaci daya zai hakura Yazauna dake amatsayin matar sa, yaron yafuto yace bayasonki to kema ki cireshi aranki, sannan daga yau ko awaya ne ban yarda ki nemesuba, “

Yana fadin haka yafice yabar mata dakin

Innalillahi… Baba bai taba fishi irin wannan ba, dama ance ka kiyayi fishin mutum Mai hakuri
Wai ita ta d’orawa kanta soyaiyar yaya Abba ne? Yaya zatayi da Rayuwar ta? Yanzu yaya Yusif yadawo amma ta gagara yimasa magana, ba kuma komai ne yasa hakanba sai tunanin datayi akan Abba, yadawo daga wata qasa tabi ta shishshige masa, daga qarshe ya Wulaqantata, tana tsoron shima tayi masa magana daga qarshe yayi mata Wulaqanci, itada shigewa maza har abada, ya Abba ya koya mata Hankali ????

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Shadaya da rabi kowa ya watse daga gidan amare anbarsu su kadai, mayafin da’aka lullube mata kai dashi ta cire tayi wulli dashi tafara fada “ina dalili Zan takura kaina akan wannan malamin, kun wani rufeni da mayafi ai zafi sai yamin illa” ????

Saukowa tayi daga gadon, tafara cire kayan ta, daga ita sai under wear a jikinta, tadauki towel tashige wanka, da ruwa Mai Dan dumi tayi wankan saboda gajiyar biki

Tana futowa daga wanka tadawo gaban mirrow tafara shafe jikinta da turare, ko kayan bacci bata nemaba ta kashe wutar dakin ta kwanta bacci
????
Shikuwa Ango Adam sai wajan sha biyu yashigo gidan, hakanan gabansa yake faduwa saboda baisan mezai tarar ba
Falon yashigo da sallama, yaga Babu kowa, wucewa yayi zai shige dakinsa amma wata zuciyar tace yakamata kaje kaduba yarinyar nan, haqqinta yana kanka

Dan qaramin tsaki yaja Kamar anyi masa dole, yakoma baya sannan yabude dakin nata yaga duhu, zuciyarsa daya yakunna wutar dakin, lokaci daya yayi arba da santala santalan cinyoyinta, baccinta take hankali kwance, magana yafara cikin ransa, to yanzu wannan tayaya zakai tunanin yimata maganar sallar da akeyi raka’a biyu ga sababbin aure? ????
Kallanta yasakeyi sosai, Diyana tanada komai da d’anamiji yakeso awajan mace but ba yarinyar kirki bace, kuma may be hakanne yasa take tallar jikinta awajan sauran maza

Bata son haske inde tana bacci, ko yaya taga haske tofa zata farka, yanzu ma cikin magagin bacci tabude idonta taganshi a tsaye yana qare mata kallo ????
Cikin ranta tace jikinnan dai haka za’a ganshi abarmin kayana
Tashi tayi zaune, har towel din yana kwance wa kana iya hango nashanunta takalleshi tace “Yawwa nace ba, idan kagama kallon ka kashe min wutar dakin please, banasan haske idan ina bacci” ????

Tana fadar haka tayi juyi ta rufe idonta, Adam kuwa kunya ce ta kamashi, karfa yarinyar nan tayi tunanin neman wani abu yazo wajan ta, tsaki yaja, yafice daga dakin ko kashe wutar baiyi ba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Ilham kuwa tunanin Nihla take tayi, tayi shiru ita kadai agidan, gashi kowa yatafi Babu kowa, tashi tayi tarage kayan jikinta tafuto falo ta kunna kallo ko Allah zaisa ta daina tunanin, gashi tabar wayarta agida bare ta kirata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button