DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Takardar ya ajiye, saboda jiri-jiri dayake gani ????

Cikin fishi hajiya Na’ila ta miqe tsaye tace “wallahi bazata sa’buba, kowa yasan kaf family dinan yarana sunada hankali, babu wanda yakai Adam sanin Allah yace, annabi yace, ????
amma arasa yarinyar da za’a liqa masa sai Diyana, yarinyar dakowa yasan tagama tambad’ewa atiti, shikuma Aslam wai Ilham, da rashin kunyar ta zaiji koda aikin gabansa “

Hajiya Farida cikin sauri itama tatashi tsaye ta maida wa hajiya Na’ila martani,
” ke saurara hajiya Na’ila, dakike cewa ‘yata tagama tambadewa ambawa danki jinake yata Dida aka hada da qungurumin Mashayi ????????‍♀️, ni nace wani abu ne? Saike me bakin magana?”

Hajiya abia tayi shiru, tabbas taji haushin furucinsu akan yayanta, sai yau take dana sani akan halin Fawaz na shaye shaye, ta kalli hajiya Farida tace
” Farida Karki sake danganta min dana da sunan shaye shaye, “

Hajiya Farida tace ” besha bane? Jinake Tun yana yaro kika gama lalata masa tarbiya, antashi an Auro mana baragurbi cikin family”

Gaba daya hall din ya kaure da surutu, da hayania, Aslam yayi shiru yana tunani, tayaya zai iya Rayuwar aure da qanwar Aysha? Yanzu kenan da ace tana raye ma Abba zata aura? Innalillah…wannan wacce mahaukaciyar wasiyya ce?

Momy kuwa hamdala take cikin ranta, shikkenan Abbanta zai auri nihila

Adam kuwa me karanta wasiyya yana ganin Ance Diyana zai aura yatuna lokacin data futo daga motar wani qato

Shikuwa Fawaz tunani yafara wai A’ina yakejin Dida ne? ???? Wacece Dida ne acikin yaran?

Daddy yayi shiru yana kallan kowa, matan sai hayaniya suke, Alhaji Baqir ne yatashi yadaka musu tsawa sannan suka nutsu kowa takoma wajan zamanta tazauna

Cikin ransa yafara magana, mata biyu!! amma wad’annan tsofaffin sunfi kowa cimasa mutunci, to aishi guda d’ayanma bayajin zai iya zama da ita, Dan haka yadago kansa Ahankali ya kalli Daddy yace

” I’am sorry Daddy, amma i can’t marry her, Daddy bazan iya auren taba, inada wadda nakeso”

Gaban Nihla yayanke yafadi, ita yaya Abba yake cewa bazai aura ba agaban jama’a?
Lokaci daya hawaye suka wanke mata fuska, babu wanda yafado mata sai Diddi, tabbas sai kayi rashin uwa zakasan wani bangaren na rayuwa

Momy ta kalli Abba da sauri tanaso ta gaskata abinda kunnanta sukaji, ba ita kadai ba hatta Usman, Aliyu, farouq, shi suke kallo cikin tsananin mamaki

Daddy kansa maganar Abba tadaki ransa, amma saiya basar bai nuna ba ya kalli Abban yace “Amma kasan cewa yanda ‘ya’yan wasu sukabi umarni bazai iyu d’anda nahaifa acikina yaqibiba ko? Tunda kace baka sonta tokaje kanemo son aduk inda yake, idan kuma kanakan bakanka har yanzu to kasa aranka cewa, qin auren Nihla dede yake da fitarka daga cikin Mazawaje family,sannan ni kaina nacireka acikin ‘ya’yana, Zabi na gareka, koka amince kokuma daga nan katashi kafita baka cikin Mazawaje family “

Hall yasakeyin tsit, maganar Daddy ta daki kowa, tabbas yanda yayanke wannan hukunci akan d’ansa nacikin sa tofa bazaiji kunyar yankewa Dan wani ba

Babu musu Abba yamiqe, yafuto daga cikin Hall din

Momy tafara kuka wiwi, tace” Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, meyake shirin faruwa damune?”

Ta kalli Abba dayake dab dabarin cikin hall din ta qwala masa kira tace “Abba!!!”

Amma ko juyowa baiyiba

(wai ina labarin yusif ne,?????Yaje China ya maqale)

(tab bari na fece kar masu dukan Abba sudawo kaina ????}

Mutara zuwa gobe????????

Kada ku Manta da sharhi, Comments, dakuma share, please

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 10:55 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

15&16

Baqin ciki yakama Momy, batasan lokacin data rungume Nihla ba suna kuka tare, Nihla kukan abu uku takeyi, na farko yanda ta dauki Abba aranta, take jinsa na daban acikin zuciyarta Tun tana qarama, amma karshe ga irin abinda yamata, na biyu Diddi, ta tabbatar da ace tana raye, zataji Dan sauqi acikin zuciyarta, na uku mafi munin yanda yafadi kalmar baya sonta acikin bainar jama’ah

Momy kam Baqin ciki yahanata magana tama kasa Dagowa ta kalli idon kowa saboda abin kunyar da d’ansu ya aikata

Hajiya Farida bataji dadin abinda akaiwa Nihla ba, yanda take shiri da Mai Hakuri bataso wannan abu yafaru akan yarsa ba, kowa yasan cewa yaran Babu Wanda yakeso, amma dukda haka ai basuyi magana ba

Hajiya Abida mahaifiyar Ilham tayi shiru abun duniya yayi mata yawa, wannan abin takaici da yanzu harda Ayshanta za’ace baza’a iya aura ba

Ran Daddy yayi mutuqar baci akan abinda Abba yayi, haqiqa ya kunya tasu agaban mutane, ya nuna musu cewa ba’a isa dashi ba

Ahankali yadago kansa ya kalli al’umar dake gabansa yace “amatsayina na babba acikin wannan family daga ranar yau, na yankewa wannan yara ranar aure, nanda wata daya Mai zuwa”

Ahankali Momy tatashi taja hannun Nihla suka futo daga cikon hall din, qafar Nihla sai hard’ewa take saboda yanda ake Kallanta
Suna fita shima Usman yatashi yayi gaba ransa abace, Aliyu ma ya biyo bayansa, yayinda farouq shima yaga to zaman me zaiyi? Yatashi yabiyo bayan ‘yan uwansa

Sai ajiyar zuciya Nihla take ja saboda yanda taci kuka, ta kalli Momy tace “Anty inajin zazzabi” daga haka tashige cikin dakinta tafada kan gado tana sakin sabon kuka

Momy ma ta doru abayanta,tana zuwa taganta tana kuka, tasa hannu tadagota ta rungumeta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida taji ta rage kukan sannan tadagota tana kallan idonta tace “Nihla, zaki iya rabuwa da Abba? Ki cireshi gaba daya daga cikin zuciyarki?”

Hawaye ne yazubo mata tace “Anty inason ya Abba sosai, bazan iyaba Anty”

Momy tace “zaki iya Nihla”

Girgizakai tayi alamun a a, sannan ta koma kan gado tarufe idonta da fillo tana kuka
Jikin Momy yayi sanyi, taso ace Nihla zata iya rabuwa da Abba, dasai ta nunawa Abba Dan hakin daka raina Shike tsone maka ido, to amma yaya zatayi tunda yarinyar ta dage akan tana sonshi? Dole shi zatayi wa dole akan saiya amince da wannan auren
Tana gama wannan tunanin tafuto daga dakin domin zuwa wajan Abba, dasu Usman tafara cin karo afalon azaune, kowa ransa Babu dadi

Batace dasu komai ba tashige dakin Abba, suma sukabi bayanta dukansu

Suna shiga dakin suka sameshi yana zuba kayansa acikin jaka, Momy ta kalleshi tace “ina zakaje?”

Fuskarsa atamke yace “Momy already hutu na yaqare Zan koma bakin aikina”

Usman yace “Abba kanada hankali kuwa? Kasan abinda ka aikata zakayi dana sanin sa agaba ko?”

“bana tunanin haka yaya Usman, wai meyasa kuka kasa fahimta tane? Saboda me Zan boye mata gaskiyar abinda yake raina?”

Cikin zafi Aliyu yace “to Dan uwarka baka isaba, wacce yarinya kakeso dazaka Wulaqanta Nihla akanta? Wacece?”

Kai tsaye yace “sunanta Nadiya, tana Abuja, tare mukai karatu da ita a germany”

Momy tace “Abba,yarinyar nanfa marainiya ce, agabanka mahaifiyar ta tace idan ka girma da kanta zata samo maka matar aure, kana tunanin tanada wadda zata samo makane bayan Nihla? Ashe yanzu da ace Aisha tana raye a gabanta zaka watsawa yarta barkono a’ido? Banasan abinda zakazo kana dana Dani akansa nan gaba “

Shiru yayi Bece komai ba, farouq kam me raguwar zuciya hawaye yake sharewa yakasa cewa komai tunda suka shigo dakin, sai yanzu yadago kansa cikin hawaye yace ” Momy nizan aure ta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button