DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Hararar wasa ta watsa masa tana shafa abin hannun nata

Murmushi yayi yace “yanzu ya za’ayi? Nayi hakuri fa maryam” ya qarasa maganar yana kashe mata ido daya

Cikin shagwaba tace “ya Adam Allah ni gaskiya bazan iyaba, duk wahalar daka bani haka bai isaba”

Daria yayi yace “a a, nide bai isaba, please maryam”

Shiru tayi masa, hakan yasa yafara aika mata da saqonni, amma yanda taji na farko wannan ma haka taji, banbancin kadanne, domin kuwa yauma taci wahala

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke afalo shida Aslam, takardu ne ahannun su suna cikewa, sun baje a kafet din falon, yayinda sautin tv din falon yake tashi Ahankali

Cikin sauri tafuto daga dakinta tana saka wayarta acikin jaka, sanye take da riga da wando na kayan bautar qasa, kayan anyi masa shape sosai, wandon nan tacika abinta Dam, rigar ma tabi jikinta, sai jacket din kayan data dora asama, tasaka Dan qaramin hijabi daya tsaya mata iya qirji, idonta sanye da glass

Qamshin turaren dasukaji ya bigesu ne yasa dukansu suka daga kansu suka kalleta
Itama kallansu tayi tace “ya Aslam ina kwana”

Murmushi yayi yace “lafiya Nihla, ya service”

Tace “Alhamdulillah” sannan takama hanya zata fice

“ke koma kicire wannan kayan”
Ta tsinci muryar Abba yana mata magana

Cak ta tsaya awajan, Sanna Tajuyo ta kalleshi fuskarta Babu yabo Babu fallasa “makaranta fa zanje, kuma kowa da uniform dinsa yake zuwa”

“nace kikoma kicire wannan kayan bazaki fita dasu ki janyo mana magana ba”

Aslam daya ga za’ayi drama agabansa saiyayi gyaran murya yace “haba Abba”

Sannan yadubi Nihla yace “Nihla jeki”

Babu musu kuwa tajuya tafice daga falon

Aslam ya kalleshi yaga fuskar nan ahade tace “meyasa zakayi mata magana Abba? Bayan kasan waje dayawa doka ne coppers suje batare da uniform ba”

“kalli shigar ta mana Aslam, tayaya yarinya ‘yar musulmai zata fita da wannan kayan ana ganin komai nata”

Murmushi Aslam yayi yadubi abokin nasa “Abba kana kishin Nihla, kode sonta kakeyi ne?”

Cikin sauri yace “Babu wani so”

Aslam yace “Abba banason rainin wayo, baka sonta tayaya zaka dinga wannan masifar akan zata fita da wannan kayan? Ni nayi mata magana ne? Malam ko kanaso ko bakaso, ina tabbatar ma kakamu dason Nihla”

Hannunsa yadaga masa “dakata Aslam, Dan Allah kadena min wannan maganar, meyasa bazaka fahimce niba ne?”

Haushi yakama Aslam yace “Ok fahimta ko? Nafahimceka”

Daga nan ya tattara takardun gabansa yafice daga part din, aikin da ba’a qarasaba kenan ????

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin farin-ciki ya kalleta, yana goge jikinsa da dan qaramin towel, “Baby Dida Tun dazu kike wannan kukan, bayan kuma kece kikace nayi, cemin kikai kinajin dadi nayi”

Hawayen idonta ta goge tace “to aiba wannan nace kayi ba, kuma saida nacema kabari amma tsabar mugun ta ka qyaleni”

Murmushi yayi, yau Babu Wanda yakai shi murna ya angonce, gaskiya masu aure sunji dadinsu, yasan hakane ai da tuni an wuce wajan yace “toki hakuri, ai daga yau nadena, wajan yadena ciwo?”

Jan zuciya tayi tace “akwai zafi sosai, rad’ad’i nakeji sosai, kuma zazzabi ma nakeji”

Yace “subhanallah, bari nagani”

Batayi masa musu ba, haka tabarshi yabude kafarta yaga wajan, yasa bakinsa yahura mata iska kadan aciki, jiyayi Kamar ya qara, amma dole hakura zaiyi Tun kafin ya ballowa kansa ruwa, tasa shi agaba tana kuka

Rufewa yayi yace “shikkenan to kiyi hakuri, zai daina insha Allah”

Ahankali ta daga masa kanta, yasaka hannu yana shafa kanta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari da yamma yana kwance a dakinsa, tunanin maganar Aslam yakeyi, yanzu idan maganar Aslam ta tabbata gaskiya yaya zaiyi? Gabansa yafara faduwa, idan hakane kuwa ai yashiga ukunsa, tayaya zai iya fuskantar yarinyar dayace bayaso cikin bainar jama’ah yace yana sonta yanzu? Anya kuwa su Momy zasu bashi goyon baya akan hakan? Innalillah…

Sumar kansa ya hargitsa, yana tuno lokacin da Momy take ce masa tana gujemasa ranar dazaiyi DANA SANI (my first novel)

Kai, bazai iyu bama, tayaya zai fara son Nihla? To amma meyasa yakejin kishinta aransa? Meyasa ranar sunan takwaransa yakasa kwantar da hankalin sa akan dadewa datayi bata dawo gida ba? Meyasa yakejin haushi idon yaga tana wa yan’uwansa Fara’ah bashi ba? Meyasa? Meyasa duk yakejin hakan?

Wannan alamomin duk sun nuna cewa tabbas yanason Nihla, Innalillahi wa inna ilaihir raju’un…, Idanunsa ne suka cika da qwallah, yasan cewa Babu me fuskantarsa

To amma yasan Nihla, yasan cewa Nihla tana sonsa, yasan cewa koda kowa zai juya masa baya banda ita, amma yanda yake ganin tsanarsa a’idonta yasan cewa abinda wahala, amma tayaya zai gane cewa tana sonsa? Ta wacce hanya?

Wata dabara ce tafado masa, lokaci daya yadanji sanyi aransa, haka yatashi yashiga toilet yayi wanka, wata shadda yadauko yasaka Mai launin Ash, yasaka hula tareda Agogon sa qirar gucci, yayi masifar yin kyau, idan ka kalleshi Babu qarya saiya birgeka

Falon yafuto yanata zuba qamshi, Nihla tana kwance da waya a hannunta tana chatting, Momy tana zaune agefe, gaba dayansu kallansa sukayi, yayi mutuqar kyau Kamar bashi ba

Momy takasa yin shiru tace “Masha Allah, Abba wannan wankan sai ina?”

Murmushi yayi Wanda yaqara wa fuskarsa kyau, yasaci kallan Nihla, Sanna yace “Momy zanje wajan zance”

Momy tayi dariya tace “Alhamdulillah, gara da kayiwa kanka fada ai”

Haushi yakama Nihla, tayi shiru batace komai ba, Abba kuwa ya juya zai fita daga falon

yaje dede kofar falon ya tsinci maganarta tace “ya Abba”

Cak yaja ya tsaya awajan, shi yasan cewa Nihla tana sonsa, wani farin-ciki ya kamashi, finally yau de takira sunansa, cikin murmushin da yaqara masa kyau ya juya yana Kallanta yace “na’am”

Budar bakinta saitace “idan kaje ka gaishe ta” ????

Be’iya cemata komai ba saide Jinjina kansa dayayi kawai tareda ficewa daga falon

Yana fita itama tatashi tashige cikin dakinta, Momy tabita da kallo amma bataga komai akan fuskarta ba
Tana zuwa dakin tafada kan gadon ta tasaki wani irin kuka Mai cin rai, ita kanta tarasa dalilin yin kukan, haushin ta daya, yanda tadage ta gyara kanta, take Jan ajinta, duk Dan yaso ta tayi amfani da wannan damar wajan nuna masa kuskuren daya aikata abaya, yanzu komai yatashi abanza kenan, ashe duk wannan dauke kan datake abanza, ashe hankalinsa yanacan kan wata daban, Wato harda yimata Fara’ah yana amsawa Dan zaije wajan wata, to tunda hankalinsa yana kan wata, tayaya zata iya rama abinda yamata?

Haka tasha kukanta sannan tashige toilet ta wanke fuskarta tadawo falon tazauna

Yana futowa daga falon nasu yake ganin duhu-duhu a’idonsa, duk hasken dayake wajan Abba baya gani, duhu kawai yake gani, baisan Inda yake saka qafarsa ba,lokaci daya Idanunsa Yarufe ruf yadena ganin komai sai jinsa yayi yafada jikin mutum Wanda baisan ko waye ba

Daqyar Aslam da Allah yakawo shi gidan yanzu, yakawo Abba cikin falon

Momy da Nihla cikin tashin hankali sukai kansu, Momy tana cewa “subhanallah, Aslam lafiya? Menene ya sameshi? Yanzu yanzu fa yafita”

“Momy wallahi shigowa ta kenan nima naci karo dashi”

Momy ta kamashi suka qarasa cikin dakin Abban, akan gado suka kwantar dashi, Nihla tabude fridge din dakin tabawa Momy ruwa tace “Momy ga ruwa” jikinta sai rawa yake

Momy ta kalleta taga yanda duk ta rude, ta karbi Ruwan aka shafa masa a fuska, Allah ya temakesu yafarka, yana bude idonsa yasauke su akanta, kallo daya tayi masa tace “Sannu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button