DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Suna zuwa bakin titi yatare musu adedeta suka shiga, gaba daya tarasa gane kan baban nata, tashar Mota sukaje, daga nan suka wuce jigawa

Awa biyu ce ta kaisu gida, kuma har lokacin Bece da’ita uffan ba, suna zuwa kofar gida sukaci karo da motar Alhaji Isma’eeil qirar Range rover

Alhaji Isma’eeil yace “Mai hakuri ina ka shiga Tun dazu angama zuba kaya amota kai muke jira?”

Baba yace “Alhaji wallahi kano naje Tun safe, yarinya ta za’ayi wa aure batare da iznina ba, shine naje nadauko ta”

Adede lokacin yafuto daga gidansu shida mami, karaf maganar tasauka acikin kunnansa, Dasauri yakai kallansa kan yarinyar da ake magana akai
“Nihla my friend” yafadi sunan cikin ransa, fuskarta ya qarewa kallo har yanzu kyanta yana nan saima qaruwa dayayi

Cikin mamaki yakalli baba yace “Baba wai wannan yarinyar za’ayi wa aure?”

Ko a mafarki taji wannan muryar bazata taba mantawa da ita ba, kallansa tayi tafara magana cikin ranta “yaya Yusif! Innalillah.. Yaushe yadawo? ????

Alhaji isma’iel yayi Murmushi yace” Mai hakuri, hakuri yaqare kenan “????

Mami da baba sukai daria, Nihla tayi shiru, ga tashin hankalin rabuwarta da yan kano ga kuma mamakin ganin yaya Yusif

Handbag din mami ce a hannunsa, ahankali ya matsa ya wullawa Nihla jakar yace “ke riqe wannan “

Dasauri ta cafe jakar, saboda karta fadi qasa

Alhaji isma’eeil yakalli Yusif yace “nasa Mai gadi yadauko kayan Mai hakuri ansaka amota, bani key naja motar da kaina, ban yarda da driving dinka ba na ganganci, idan kuka samu titi kuna gudu Kamar bakwa son ranku” ????

Sumar kansa ya sosa,sannan yabashi car key din

Sai a lokacin Nihla tagaidasu, mami da Alhaji Isma’eeil suka amsa mata cikeda kulawa

Alhaji ne yabude motar yashiga, shima baba yashiga gaba, mamy da Nihla suka shiga baya, sannan shima Yusif yashiga bayan daga daya bangaren, Yazauna agefen mamy

Mamy ta kalli Nihla cikin kulawa tace “Nihla kinsha hanya sosai ko ‘yata, nasan kin gaji, zoki kwanta kihuta” ????

Taja Nihla jikinta sannan ta dora kanta akan cinyarta tana bubbuga bayanta Kamar wata qaramar yarinya

Shikuwa Kallanta yake, Wato bazatayi masa magana bako? It means batayi missing dinsa ba,koda yake yaushe zatayi masa magana tunda ta Manta dashi harta samu wani zata Aura (tofa????)

Ahankali Alhaji isma’eeil yatada motar, suka dauki hanyar Abuja.

To Alhamdulillah anan na kawo qarshen labarin DANGI DAYA, zan Dakatar da typing dinsa badan komai ba saidon Comments din readers da ban gamsu dashi ba, sharhi yayi qaranci, idan akwai wadda na batawa rai Sanadin wannan labari to tayi Hakuri ????????

WhatsApp readers banida bakin dazan gode muku, kunyi min komai akan wannan littafi
masu yimin sharhi daga cikinku nayi saving number dinsu insha Allah zansakaku asabon group dina, mudinga gaisawa

Yaya labarin Mazawaje family?

Wanne hali Momy zata shiga dangane da tafiyar Nihla?

Yaya Rayuwar Nihla zata kasance a Abuja?

Ina labarin amare masu shirin shiga daka ciki?????

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/21, 1:40 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️

{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

Tabbas hakane, laifin wani baya shafar wani, amma kuma Babu dadi kayi rubutu a karanta ma bayan ansan kanason Comments a share ka, danku nake wannan rubutun, be kamata agani ayi shiru ba, masu kirana, masu min private text, masuyi min magana ta group, da Wanda suka min ta page d’ina, duk naji maganganunku, nagode da soyaiyar dakuke nunamin, insha Allah zanci gaba da typing, daga qarshe wannan page din na sadaukar dashi ga dukkanin masoyan Amnah El Yaqoub ????

‘yan labe ina kuke? ???? To Allah yasa ku d’ore dayin Comments ehe????????

17&18

Liman ya kalli Alhaji Abubakar kozaice wani abu tunda shi ne babba, amma tashin hankalin da Alhaji Baqir ya hango a fuskar Daddy ne yasa shi yayi magana dasu yace “ala gafarta Malam mungode, mungode sosai,”
Yadauko kudi a aljihunsa masu yawa ya ajiye musu, Sannan yakama hannun Daddy suka futo daga masallacin, Alhaji Kabeer kuma shine yake sanarwa da mutane ansoke daya daurin auren, daga nan yaci gaba da godia ga jama’ar dasuka gayyata

Uban gayya kuwa fuskarsa Babu yabo Babu fallasa Wato Abba
Angwaye dukda dama can suna cikin bacin rai, sai abin yasake qaruwa
Usman yadafe kansa, meyasa baba Ibrahim zai musu haka? Amma aida yayi hakuri anbi komai Ahankali ko, amma abu acikin taron mutanen da sukazo daurin aure

Dan haka yayiwa su Aliyu alama da ido, nan danan suka futo gaba dayansu sukabi bayan Daddy

Su Daddy kuwa saida sukaje bakin get sannan Alhaji Baqir yasaki hannunsa yace “Alhaji kayi hakuri, nasan yanda kake ji acikin ranka, kayi hakuri” ya qarasa maganar yana bubbuga kafadarsa

Su Usman ne suka qaraso, Aliyu yajashi hannun Daddy yace “Daddy Muje ciki”

Alhaji Baqir yawuce part dinsa jiki a sanyaye

Suma sukaja hannun Daddy suka tafi, mutane baqi anata hidima, dasuka shigo kowa sai gaida su yake amma su Usman ne masu amsawa, suna shiga dakin Daddy gaba dayansu suka zauna Babu me magana acikinsu, farouq yafuto daga dakin yayi wajan Momy

Yana zuwa yakama hannun yace “Momy zokiji”

Kallansa tayi tace “jarababbe, farouq Dan Allah kabarni nahuta yau ana bikinma bazaka rabu Dani kaima kaje wajan mutanan ku ba”

Yace “Momy kitaho please”

Fuskarsa ta kalla taga Babu wani wasa ko Fara’ah, mamaki ya kamata, Dan haka kai tsaye tabishi zuwa dakin Daddy

Kujera ta nema tazauna, tace “yanaganku haka jiki a sanyaye? Meyake faruwa ne?”

Daddy yayi shiru har lokacin Bece komai ba, Aliyu ne yafara magana “Momy Wallahi fa ansamu matsala, anfasa auren Nihla da Abba”

Cikin mamaki tace “me kace Aliyu?”

Usman yace “hakane Momy, baba Ibrahim yazo yadauketa, suntafi”

Adede lokacin Abba yashigo dakin, yanemi waje Yazauna, duk Babu Wanda ya kulashi

Momy ta kalli Daddy tace “to Alhaji meyasa zakayi shiru? Yanzu de ka kirashi kafada masa Dan Allah ni yadawo min da yarinya” ????

Ajiyar zuciya Daddy yayi, sai a lokacin yayi magana “Ibrahim ya nunamin yafini iko akan Nihla ne, yanda na nuna masa iko da farko, shine yazo har gida ya nunamin yafini iko akanta”

Tace “mekake nufi Alhaji, bangane maganganun ka ba”

Yace “Rahma bayan rasuwar Aisha nashiga tashin hankalin da ban taba fuskantaba, Nihla kadai Zan gani naji dadi, ita kadai Zan gani yarinyar inji Kamar Aisha tace akusa Dani, hakan yasa lokacin dazamu dawo gida kai tsaye nace ku fito mutafi, saboda ina tsoron inyiwa Mai hakuri magana yace bazai ban itaba, nasan shima yaji mutuwar Aysha, Awannan lokacin bazai taba yarda yarabu da ‘yarsa ba, nikuma Rahma bazan iya tahowa nabar jinin Aisha Awannan wajan ba, shiyasa nadauko ta muka Taho batare da iznin mahaifin ta ba “

Momy tace “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un,”

Dukda taji gaskiyar magana a bakinsu, wani bangaren na zuciyarta bai yardaba, wayarta tadauka takira layin Nihla, Adayan bangaren wayar tana hannun Dida tana ganin sunan Anty tasan cewa Momy ce, saboda ita kadai Nihla take cewa Anty

Ta daga wayar tace “Momy Nihla tafita bakin get, wai babanta yazo”

Kashe wayar Momy tayi tace “Innalillah… Yanzu Alhaji shikkenan Nihla tatafi? Inaji ina gani anrabani da ‘yata…” Sai kuka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button