DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Batare dayace komai ba yasakko Yazauna aqasan shima, yafara kokarin zuba Abincin da kansa, cikin sauri ta riqe masa hannu tace “kabari mana, yau nice zanyi feeding dinka, Kamar yanda kamin lokacin da banda lafiya”

Yace “Am maryam dakin bar…” Dasauri katseshi, tace “shiiiii”

Nan take yayi shiru, ta matsa kusadashi tazuba masa Abincin sannan tasa spoon tafara bashi, daqyar Adam yake cin Abincin saboda gaba daya tashige jikinsa, yanajin yanda take goga masa kirjinta ajikinsa, duk yarasa yaya zaiyi da ita, shi yana ganin Ilham da Aslam suna soyaiya a asbiti ashe idan Diyana ce saide arufe ido?
Ko yaya yayi motsi saiya gogi kirjinta, gashi ita abin nata masha Allah ba kadan ba, Danya rabata da jikinsa yasa yayi dabara cikin shagaggiyar murya yace “ke bazakici bane?”

Diyana tanajin yanda yayi mata maganar tasan cewa lalle tarkon ta yakama, cikin qasa-qasa da murya tace “um um, nafison kaide kafara qoshi tukunna”

Jiyayi jijiyoyin kansa suna nema su fara aiki, haka yayi shiru yakasa cemata komai, gaba daya saiya zame mata Kamar wani dolo, haka tadinga bashi Abincin shide sai santi yake aransa, domin kuwa ba qaramin dadi yamasa ba

Saida tagama bashi, sannan taci Dan kadan, yazuba mata ido yana Kallanta yanata mamaki, gaskiya duk Wanda ba’a zauna lafiya a gidansa ba to mata basu bashi hadin kai bane, amma inde mata sun bashi hadin kai, to za’a zauna lafiya, kalli de maryam, da ya’isa yayi mata maganar girki ma, amma yanzu shine ake bashi abinci abaki, yaji dadi sosai aransa, kuma yadena fishin shi ya dade da janyewa????

Ajiyar zuciya yayi, yace “Maryam girkin yayi dadi sosai”

Ajiye spoon din hannunta tayi tace “da gaske ya Adam yamaka dadi?”

Jinjina kansa yayi alamun qwarai kuwa

Beyi aune ba yaji takai masa wata irin runguma, tace”thnk you ya Adam “

Ahankali Adam yace
” yasalammm!”

Besan cewa sarai Diyana tajishi ba, itama sai tayi fuska Kamar bataji ba, tasake shi tace, “nima naqoshi, bari nakai kayan kitchen”

Adam yana ganin shigar ta kitchen ya lallaba yashige dakinsa, Dan idan yaci gaba da zama anan, maryam zata haukatashi da salonta

Bayan tafuto daga kitchen taga baya nan tayi Murmushi tace “ko’ina yakai fishin dayake oho?” ????

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin nutsuwa take shirya musu kayansu, yau likita ya sallamesu, shikuwa Aslam yana kwance yana aikin Kallanta, har yau mamakin Ilham yakeyi, kulawar datake bashi ne yasa yaji bayason subar asbitin, duk’da gidan nasu ma su kadai ne, amma saiyake ganin Kamar idan sun koma gida zata dena, tsaf tagama shirya kayan Tajuyo ta kamashi yana Kallanta, yatsina fuska yayi alamun ciwo yace “wash Allah na”

Cikin sauri ta qaraso wajansa tace “Sannu ya Aslam, ko wani waje ne yakema ciwo?”

Yace “kad’an kad’an nakeji”

Jikinsa tafara tabawa tana cewa “ka tabbatar deko?bakajin komai”

Qirjinsa ya nuna masa yace “sai nan dina, setin zuciyata yana dan min ciwo kadan”

Wajan tasa hannunta tana shafa wa tace “Sannu ya Aslam, ze daina yima ciwon kaji”

Lumshe idonsa yayi, yanaji Kamar karta dauke hannunta awajan
Ahankali yabude idonsa yace “bafa nan baneba”

Cikin mamaki ta kalleshi tace “to’inane? Kode ma kira Doc.?”

Cikin sauri yace “um um, kinga irin nan ne fa”
Yakai hannunsa kan qirjinta yana shafa wa, wani irin zirrrr taji a jikinta, numfashinta yana sauya wa, gaba daya taji wani irin yanayi yana ziyartar ta, kuma takasa hanashi abinda yake, ganin saqon nasa yasamu karbuwa yasa ya janyota jikinsa gaba daya, babu musu ta dora kanta a Kirjinsa, shikuwa yatura hannunsa cikin rigarta, yana abinda yakeso, kansa yadora akan wuyanta yana kissing wajan, lokaci d’aya Ilham ta lumshe idonta, gaba dayansu nema suke su fita haiyacinsu Ahankali tadago kanta tace “Ya Aslam muna asbiti nefa, katashi mutafi”

Ajiyar zuciya yasauke yana Kallanta, sannan yakira number Abba, ko minti talatin basuyi ba kuwa yazo yadauke su, Ilham tana baya tanajin su suna firar kamfaninsu da zasuyi bikin budeshi gobe, ya Abba Babu wasa bayason raini, ko saka Ilham bayayi acikin maganar tasu, saide Aslam yanayi yana juyowa yana Kallanta ahaka har sukaje gida sannan ya juya, sukuma sukai ciki

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Wasa-wasa saida Fawaz yayi zarya awajan Dida harya gaji amma Dida ko kallansa batayi, gaba daya ya lalace, idan ya koma gida Babu abinda yake sai aikin tunanin ta, a yanzu kam shi kansa yasan cewa yana qaunar Dida, saide anata bangaren yanada tabbacin cewa Dida bata sonsa.
Abangaren Abba kuwa aiki yataru yayi masa yawa, ganasa aikin da yakeyi, ga kuma aikin campanynsu dasuka bude Wanda yake sarrafa kayaiyakin Furnitures, kuma Abban ne yake jagorantar komai tunda Aslam yana gida yana shan Honeymoon, shiyasa koda yaushe baya zama

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“kiyi hakuri mana, kukan ya’isa haka”

Cikin shagwaba tace “toba saida nace ma akwai zafi ba, amma kai kullum saika dinga qyaleni” ta qarasa maganar cikin kuka

Jikinsa ya janyo ta, ya bubbuga bayanta yace “Ilham, toyi shiru mana hajiya ta, kiyi hakuri insha Allah zaki daina jin zafi, Nikaina nayi mamaki ace kusan wata daya kenan amma har yanzu kinajin zafi, but kiyi hakuri zaki dainaji kinji?” ya qarasa maganar cikin sigar sigar lallashi

Daga masa kai tayi, kafin tayi magana wani irin amai yataho mata, cikin sauri tatashi da gudu tayi cikin toilet, Aslam yabita da kallan mamaki

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Idan lissafin sa yayi daidai to yau watan Dida daya kenan agida, yau kam saide ayi Wacce za’ayi, amma inde yaje Babu Inda zai dawo saida matar sa, tsaf ya shirya yatafi gidan yaje kofar part dinsu Dida Yazauna, hajiya Farida tafuto falo zatayi kallo saitaga Kamar mutum awaje, tadaga labulen falon nasu kawai sai ganin Fawaz tayi azaune, Dasauri tasaki labulen Tun kafin yaganta, juyowa tayi tadawo cikin falon jikinta asanyaye, wannan yaro yanashan zarya, amma taga alamun Dida ko’ajikinta, Tun bata tausayin yaron harda dawo tana tausaya masa, gaba daya ya lalace wannan Jan lips nasa duk sun bushe ????

Haka tayi shiru tana fatan Allah ya hade kan yaran nasu gaba daya
Tun la’asar yake wajan, har magrib baije ko’inaba, saide idan ankira sallah yaje masallacin dayake cikin gidan yayi sallah yadawo, itama Dida da magrib din tafuto falo akan idonta yadawo daga masallaci yaci gaba da zama awajan

Amma saita nuna batasan ma yana wajan ba, hajiya Farida tana hankalce da’ita, tayi shiru tana kallan ikon Allah
Har karfe goma na dare Fawaz Yana wajan, kawai jira yake babanta yadawo yaje ya sameshi suyi magana abashi matarsa, adede lokacin kuma hadari Mai yawa yahadu, sai cida akeyi da walqiya alamun ana gab da yin Ruwan sama.

Iska aka fara amma Fawaz Yana zaune, har wajan shadaya na dare sannan ne aka fara sheqa ruwa kamar da bakin qwarya, Fawaz Yana nan zaune ruwa yana dukansa sai karkarwar sanyi yake, kayan jikinsa ya jiqe jalaf
Amma tsabar taurin kai yana wajan azaune, daga qarshe ma tashi yayi tsaye ya zubawa part din nasu ido yana kallo
Dida na cikin dakinta tana karanta littafi harta sauya kaya zuwa doguwar riga ta bacci, sai dan qaramin mayafi data daure kanta dashi, cikin ranta tace su Fawaz anace, Tun la’asar anzo an zaune, ai yanzu nasan dole yatafi, danni kam bazan koma gidansa yaci gaba da dukana Kamar yasamu jaka ba, littafin ta ajiye tatashi ta zuge window din dakinta taleqa, gabanta ne yafadi ganin Fawaz Acan gefe a tsaye yana karkarwar sanyi, ruwa sai dukansa yake, cikin tsananin mamaki tace “Innalillahi… Ya Fawaz”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button