DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Ilham tace “to nide abinda idona yagani aishi Zan fada”

Haka sukaci gaba da firarsu har hudu da rabi tayi, hajiya Na’ila takira wayar Ilham din tace tazo kafin tatafi gida, tashi tayi tafara shirya wa, Momy takawo mata wani turaren wuta Dan Sudan Mai qamshi, ta karba tana godia

Momy ta kalleta tace “Nihla karbo mata yaronta awajan Abba, zasu tafi”

Tashi tayi ta nufi dakin nasa, Ilham tanayi mata dariya qasa-qasa, ahankali ta tura dakin tashiga, taganshi yana kwance yadora yaron akansa yana masa wasa

Cikin ranta tace ashe yana yiwa yara wasa, sallama tayi ta qaraso, tunda tashigo idonsa akanta Ahankali shima ya amsa sallamar tata

Gabansa ta qarasa, ganinsa dagashi sai ita yasa taji duk yayi mata kwarjini, tana jan yatsun hannunta tace “Momy tace akawo shi zasu tafi”

Da idonsa ya nuna mata yaron yace “gashi nan daukeshi mana”

Wai yaro akan qirjinsa bazai bata shiba saide tasa hannu tadauka, zuciyarta daya kuwa tasaka hannu tadauki yaron
Jin hannunta yadan taba Kirjinsa hakan yasa ya lumshe idonsa, gaskiya yanzu kam yaqara tabbatar wa kansa cewa soyaiyar yarinyar tayi masa mugun kamu

Nihla bata lura da yanayin sa ba tafuto daga dakin, bayansu yabi da kallo itada Babyn, sai yaji dama basu tafiba, dama tazauna yasaka su agaba yana kallansu itada babyn

Bayan sun futo daga part din Momy Nihla tawuce part din umman Ilham itada Yaron, ita kuma Ilham tawuce part din hajiya Na’ila

Ta dade a part din hajiya Na’ila kome take bata oho ???? sannan tataho part din ummanta wajan Nihla, takira ya Aslam yazo yadauketa suka tafi, Nihla taji dadin ziyarar da Ilham takawo musu, Ilham tana sonta sosai, tazo gida amma bata wuni awajan sirikarta da ummanta ba, sai awajanta tawuni

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Wanka yashiga ita kuma tana gyara masa dakin nasa, wayarsa ce tafara qara, tanufi wayar taduba taga number ce take kira

Zuciyarta daya tadaga wayar, sai taji muryar mace tace “Malam Adam yau zaka shigo makaranta kuwa?”

Gaban Diyana yafadi, cikin masifa tace “Wacece ke? Menene hadin ki da mijina?”

Alokacin yafuto daga wanka yayi gaban mirrow zai shirya, yana ganin wayarsa ahannun Diyana sai masifa take amma ko Kallanta beyiba, shide yasan yanada gaskiya, kuma Babu wata mace daza dauke hankalinsa daga kan Diyana a yanzu,yanda yakeji da amarcin nan ai Babu me rabashi da maryam

Diyana kuwa sai masifa take, amma wadda takira wayar bata qara cewa komai ba Tun maganar ta ta farko, daga qarshe ma saita yanke wayar

Diyana Tajuyo ta kalleshi tace “ashe yanmatan university har kiranka suke kuna waya bansani ba”

Kayansa yake sakawa cikin sauri saboda yayi latti dayawa, yace “to menene abin damuwa maryam, tunda kece Mai ni”

“wata yar’iska takira ka awaya da wannan safiyar kacemin menene abin damuwa? Amma yanzu idan nice wani yakirani da yanzu kafara fada ko”

Hularsa yasaka yajuyo yana Kallanta, kishi qarara yagani akan fuskarta, Bece da ita komai ba yadauki key din motarsa yana kokarin fita

Itama cikin haushi tafice daga dakin, da wayar tasa a hannunta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Wayar Dida ce a hannunsa yana sending pictures dinta zuwa tashi wayar, gyaran falo take, yana ganinta tagama ta goge sauran kayan kallo, sai aikin take da jikinta Kamar batasan ciwon jikinta ba

Kitchen ta wuce yatashi yabi bayanta, yana mata wani irin mayen kallo, “wai har yanzu aikin bai qare bane?”

Kallansa tayi “bai qareba, abinci ma zanyi mana”

“kibar Abincin nan Dan Allah, basai naje nasiyo mana ba, ke kullum bakya hutawa”

Wani irin kallan soyaiya tayi masa “menene abin gajiya acikin girkin mutum biyu”

Ajiyar zuciya yayi yatako yazo bayanta ya rungumeta, yayi qasa da muryar sa yace “please kibarshi”

“ya Fawaz Dan Allah kabarni nayi aikina, sokake kahanani kai kuma ka bata kudin ka, menene amfani na da zakaje siyo mana abinci”

Kissing din wuyanta yayi, yasake qasa da muryar sa yace “wai wajan nan har yanzu bai warke bane?”

Zaro ido tayi, takwace jikinta Dasauri “wallahi be warke ba, bari naje daki akwai abinda zanyi” cikin sauri tafice daga kitchen din tabarshi anan

Murmushi yayi ya shafa kansa sannan yadawo falo Yazauna, yana ganinta takoma kitchen din tana aikinta, harta gama tazo tazuba musu cikin flet daya, cikin nutsuwa suka gama cin Abincin, sannan ta maida komai kitchen, kafin tafuto daga kitchen ya kwanta atsakiyar kafet din falon yafara murqususun qarya Kamar gaske, Dasauri Dida ta qaraso wajansa “ya Fawaz menene? Lafiya kake kuwa?”

Idanunsa a runtse yace “Dida cikina ciwo yake min, bayan kinsan meyake damuna, kuma gashi kince wajan bai warke ba”

Gabanta yafadi, cikin in-ina tace “emana, be warke bafa da gaske dane, sannu insha Allah zai daina”

Yace “shikkenan Babu komai idan na mutu ma shikkenan”

Dasauri tace “mutuwa! A a ba yanzu ba insha Allah,”

Yace “yanda nakeji Kamar mutuwa zanyi Dida”

Cikin shagwaba tace “to shikkenan kazo kayi amma Dan kadan gaskiya, kuma idan nace ya’isa to katsaya ahaka”

Dadi yakama Fawaz, sai yau yaqara tabbatar wa Dida yarinya ce, yace “eh nayarda”

Lokaci daya yatashi ya janyo ta jikinsa, dayake yarinya ce kwata kwata bata ganoshi ba, yanda yamiqe lokaci daya Babu wani alamar ciwo, anan falo yafara nuna mata yanda yayi missing dinta, daga baya sukai ciki

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune take akan kujera har yanzu dube dube take cikin wayar tasa, amma bataci karo da number mace ko dayaba, koda yake tayaya zaiyi saving numbers din yanmatansa a wayarsa, haka nan ranta yake mata zafi Tun safe

Shigowa yayi da sallama ta amsa masa batare data kalleshi ba, yayi Murmushi yana zama agefenta, yace “wash Allah, nagaji wallahi”

Tanaci tayi banza dashi

Hannu yamiqa mata yace “bani wayata, dazu na Manta ban dauka ba”

Asheqe tamiqo masa wayar, ya karba yace “Maryam ina abinci”

“Dining”

Abida tace masa kenan, yatashi tsaye yace “wai saboda wata takira wayata shine kike wannan fishin? Ni nayi tunanin ma kin huce, ai shikkenan, yau bazan samu damar da za’a kaini inci Abincin bama, to zanje na Auro wadda takirani awayar, saitazo tadinga bani, tunda naga alama nema kike ki rainani”

Nanma banza tayi dashi, shima yaje yaci Abincin sa hankali kwance, yana gamawa yakara wayarsa akunne Kamar yayi kira yafara cewa “hello hajiya ta, kiyi hakuri dazun wata qanwata ce tadauki wayar wallahi, kinaji na.. Kinsan me za’ayi yanzu….?

Diyana bataji qarshan wayar ba saboda shigewa dakinsa dayayi yarufo kofa, Baqin ciki yakamata, dama ai tasan matar cushe bata daraja, wani kukane yazomata Mai cin rai, tatashi cikin kuka ta nufi dakinsa, duk kayan ta dasuke dakin tafara hadawa tana hawaye

Dariya takama Adam, yayi fuska, sannan yatashi yazo bayanta ya tsaya yace “mekike shirin yi haka maryam? Ina zakije kike daukan kaya haka”

“gidanmu Zan tafi, bazan zauna bakin cikin wata yadameni ba”

“saboda nace Zan qara aure kike kuka? To aikuwa ki shirya, Dan uku suna nan zuwa, Allah yabani damar dazan ajiye mata har hudu acikin gidannan, kuma ni banyi miki alqawarin cewa Zan zauna dake kekadai ba, garama kisa aranki kishiya tana nan zuwa”

Hannunta ta dora akanta tafashe da kuka, ta tsugunna awajan tana kuka bilhaqqi

Adam baisan lokacin da dariya ta kwace masaba, Yazauna agefen gadon yanata dariya yace “maryam, yanzu saboda kishiya kike wannnna kukan?ashe kina sona haka? To kinga ni wasa nake miki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button