DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Dida tace” to Nihla me kikeso suce miki?, lemo yanema ki kawo masa, kinga ai bazai iyu suce karkije ba, babu girmama wa aciki, Inda wani abu yace daban, dole zasubi bayanki “

Tace” to zaman dayake a wajena fa? Shikuma me zakice? “

Diyana tayi Murmushi tace” ai zama wannan kawai ni abinda na fahimta yana gyara kansa ne kawai, ada ma kowa yana cewa Nihla Nihla bare kuma yanzu daya ga abubuwa sun qara baiyana ai dole Yazauna a qarqashinki “????

Nihla tace” to aikuwa zandena zaman falon, bare yazo yananiqe min “

Ilham tayi Murmushi tace” keda abokinki “

Harararta Nihla tayi tace” kimin shiru kiji da abinda yake jikinki, wai Dan Allah idan kin haihu ma sunan wazaki sane? Dafatan nizaki saka “

Ilham tace” hum wallahi ingaya miki yace Ya Abba zaisa, in mace ne kuma Anty aysha “

Yatsina fuska tayi tace” Abba de Abba de, narasa meya musu duk suka daukakeshi haka”

Ilham tace “aikinfi kowa daukakarsa, keda kikace yana nan daram acikin ranki kina sonsa”

Wata irin dariya tayi tace “um da kenan, da kika sani yarinya, wallahi yanzu nafi qarfin sa”

Diyana tace”gaskiya kam, wallahi kija ajinki dakyau, yagane da da yanzu ba daya bane”

Dida tace “Allah sarki ya Abba, nikam wallahi tausayi yake bani, ko’ina yarinyar dayace yanaso din Dafarko?”

Ilham tace “nikam dukda abinda yamiki abaya, wallahi zanso ace kin aure shi, kin auri abokin mijina, muci gaba da zumuncinmu, Nihla ki auri ya Abba Dan Allah, shi ubangiji yanason bayinsa masu hakuri, duk danasan cewa abune Mai mutuqar wahala hakan”

Diyana tace “waiku cewa yayi yana sonta?, Nikaina nasan ya Abba yahadu babu qarya, yakai na mijin dakowacce mace zatayi Burin ace ta samu, to amma kutuna abinda yamata mana”
ta kalli Nihla tace “wallahi koya dawo kinuna masa mata sunada daraja”

Nihla tace “yawwa Diyana, fada musu de”

Haka sukai ta firarsu cikin jin dadi, kasancewar haduwa tana musu wahala

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Ahankali kwanaki sukaci gaba da shudewa, Abangaren Dida, tunda tasamu ya Fawaz ciwon cikin sa yalafa tadena damuwa, sabgarta kawai takeyi, domin kuwa itade tana kunya bazata iya masa komai akan haka ba, cikin Ilham kuwa yaqara girma tana nan haihuwa yau ko gobe, babu wanda yakai Aslam murna saboda yasan cewa kwana kusa zai zama uba

Yau bataje makaranta ba Inda take service, ta dade tana bacci dasafe sai wajan goma da rabi tatashi, doguwar riga ce a jikinta ta bacci amma me kauri, rigar batada hannu, sai hula datasa akanta, tana hamma tafuto falon anan taga Momy itada wani da alama likitane sun futo daga dakin ya Abba, yanayin Momy ta kalla kawai tasan Babu lafiya saboda yanda jikinta yayi sanyi,kuma hakan baya rasa nasaba da abinda likitan yafada mata, sallama sukai da Doc din sannan tajuya zata koma dakin nasa, Nihla tace “Momy lafiya?”

“wallahi Abba ne baida lafiya Nihla”

Tace “subhanallah, Allah yabashi lafiya Momy” tafadi haka tana kokarin juyawa dakinta

Momy ta kalleta da mamaki tace “yayanki baida lafiya, amma kina kokarin juyawa daki? Ba zakizo ki ganshi ba?”

Turo baki tayi gaba alamar shagwaba, Sannan tabiyo bayan Momy suka shiga dakin nasa, yau ne karo na farko data shigo dakin Tun bayan barin ta gidan, gaba daya dakin saiya koma mata sabo saboda ansauya komai nasa

Yana kwance yana bacci, dagashi sai wando three quater, da vest fara qal ajikinsa, kallonsa Nihla tayi, faffadan qirjinsa gashine kwance, sai Dan qaramin bakinsa daya fara bushewa, ko menene yake damunsa oho?

Kallan Momy tayi tace “Momy ai bacci ma yake, bari naje nayi wanka kafin yatashi” tafadi hakanne kawai danta gudu, saboda bata fatan ace yafarka yaganta a dakinsa

Abinda bata saniba kuwa shine idonsa biyu, kawai yana kunyar hada ido da Momy ne, tayaya zai iya Kallanta bayan fama dayayi da ciwon ciki Tun cikin dare kuma yau doc yazo yace yakamata ayi masa aure saboda sha’awa datake damunsa, tayaya zai iya hada ido da Momy?

Momy tace “a a, ai hakuri zakiyi da wannan wankan, nasa Adala tahada masa Tea, zanje na karbo, ki zauna karya farka shi kadai kozai nemi wani abu” ????

Wannan karan kam, ran Nihla baci yayi, harta kasa boye hakan akan fuskarta, Momy ma taga yanda yanayin ta ya sauya amma haka tayi shiru tafice daga dakin, taga alama Nihla har yanzu yarinya ce, yanda takejin ta aranta Kamar su Usman Babu yanda za’ai tadinga Hadata Da Abba Dan wata manufa, itace ta haifi Abba amma dole zata nuna masa kuskurensa akan abinda yayiwa Nihla abaya, amma hakan ba zaisa tazuba musu ido tana kallansu suna zaman doya da manja ba, koba komai dukansu yaranta ne, babu wanda zata nunawa banbanci acikinsu, tana wannan tunanin ta qarasa cikin kitchen din

Shiru Nihla tayi tana tana zaune akan bedside drower, ko Inda yakema bata kallo, shima yana jinta a gefensa amma bai bude idoba, asali ma jiyayi bugun zuciyarsa yana qara sauya wa, kuma yarasa dalilin hakan, yasan cewa a dole take zaune dashi, saboda yanda yake ganin tsanarsa qarara acikin idonta, yasan kozai mutu bazata kulashi ba

Ahankali wata dabara tafado masa, bari ya gwada, yasan idan yayi hakan dole zata ambaci sunansa, sannan tabashi kulawa

Ahankali yafara motsi tareda yatsina fuskarsa, cikin alamun ciwo yace “wayyo Allah nah…. Momy… Momy Zan mutu…”

Cikin sauri Nihla ta kalleshi, amma abin mamaki ko sunansa bata kamaba tace “subhanallahi, sannu” ????

Haushi yakama Abba, waime yarinyar nan take nufi ne? Murqususu yaci gaba dayi Kamar gaske, duk ya rikice Kamar bashi ba, handle din dakin da aka kama za’a bude yasa Nihla tayi tunanin Momy ce zata shigo, kuma tasan fada zata mata tace tana ganinsa ta qyaleshi, hakan yasa cikin sauri tatashi tadawo gefensa tazauna tana cewa “Sannu, sannu”

Jinta akusa dashi yasa yatashi Ahankali Yazauna, sannan yazuro qafafunsa qasan tiles din dakin yamiqe tsaye zai shige toilet, yana Miqewa kuwa mararsa ta murda agaske, cikin azaba yadawo Yazauna, baisan lokacin da yadora kansa akan kafadarta ba, hannunsa kuwa yana kan cinyarta, gaban Nihla yahau luguden faduwa, itafa tarasa gane Inda ya Abba yadosa, meyake nufi hakane?

Ahankali yaji maransa tadena ciwo yabude idonsa, amma me? Saiya kasa dauke kansa daga kan kafadarta, yanda ya kwantar da kan nasa hakan yabawa idonsa damar hango cikakkun nashanunta farare tas, cikin ransa yace wallahi natane Babu qari, but ya’akayi yarinyar nan takoma hakane cikin shekara hudu?

Turo dakin Momy tayi tashigo hannunta dauke da cup din Tea, ganinsu ahaka yasa ita kanta gabanta yafadi, anya Abba kuwa bason yarinyar nan yakeba? Me Abba yake shirin janyo musu? ????????‍♀️

Haka de takawar da tunanin aranta, takawo masa Tea din tace “gashi Abba, tashi kasha Tea”

Ahankali yadago kansa daga kafadarta, cikin dabara ta matsa can gefe dashi tana hamdala aranta, Tea din ya karba yafara shan ahankali, cikeda shawaga yace”Momy zafi “

Tace” nifa Abba dama ba rashin lafiyarka ba kadinga langabewa mutum kenan, kaiba qaramin yaro ba amma kadinga shagwaba, kuma wannan gashin na qirjinka ka zauna ka askeshi Dan Allah”????

Dukda yana jin jiki, saida ya danyi murmushi kadan, yasaci kallan Nihla, sai yaga kanta a sunkunye batama kallansu

Saida Momy tabashi magani yasha sai runtse ido yake alamun bayaso, sannan suka futo daga dakin itada Nihla

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button