DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

” to shikkenan baba, Allah yasa hakane yafi alkhaairi, “

” amin, Allah yayi miki albarka ki gaida su hajiyan “

” to baba zasuji “

Tana kashewa ta kalli Momy tace” Momy nida baba ne, yana gaishe ki, maganar Auren ya yusif yayi min, Momy nida nafiso saina gama service dina, amma shi baba yace wai basai nagama ba kawai zasuyi magana da babansa, su tsaida magana daya “

Tun lokacin da al’amarin Nihla da Abba yafara wakana, Momy bata taba Jin faduwar gaba irinna yauba, jikinta yayi sanyi, Nihla de da gaske take tarabu da Abba Yusif din takeso
Murmushi ta qaqaro tace” Alhamdulillah, to Nihla ai hakan yafi, menene amfanin jira yata, abinda Mai hakuri yafada gaskya ne, aide kina sonsa ko? “

Momy tayi Tambayar tana zubawa Nihla ido ko zataga yanayin ta ya sauya amma saitaga Babu damuwar komai akan fuskarta
Saima kanta data daga alamar eh tanaso

Murmushi tasakeyi, kafin tayi magana yaturo kofar dakinsa yafuto yayi mutuqar cikin suit kalar ash, qaraso wa yayi Yazauna akan hannun kujerar da Nihla take zaune ????
Yasa hannu yadauki Ruwan da yagani ansha, yazuba a cup yafara sha Ahankali, Nihla sai matsawa take gefe, tarasa wannan abu na ya Abba, duk kujerun falon sai akusa da’ita zai zauna, wayarta tabude tashiga chatting tanayi

Shikuwa yana shan ruwa hankalinsa yana kan wayar tata, jikinta ne yabata ana kallonta, danhaka tashiga cikin chat dinta itada ya Yusif tayi sallama daganan bata jira komai ba tafara tura masa da kiss????????????

Wani irin qullutun Baqin ciki ya tokarewa Abba wuya, ahankali yaji Ruwan dayake sha yafita daga ransa

Yusif kuwa baya rufe datar sa, yana ganin saqon Nihla yadoko mata kira

Nanma akan idon Abba kiran yasake shigowa, murmushi tasaki sannan tayi cikin dakinta tana amsawa wayar

Abba yabita da kallo ransa abace, Momy ta kalli yanayin sa, tace “Abba na sai ina?”

“Momy zamuje Abuja ne nida Aslam”

“Abuja kuma? Wajan wa? Me akeyi?”

“Momy wajan baba Ibrahim zamuje mugaidashi”

Tausayinsa yakama Momy, tasan duk saboda Nihla zaiyi hakan, taji dadi aranta tunda yau Abba zai gyara kuskuren daya aikata, tace “to sai kundawo”

Daga nan tatashi, tsaye tayi hanyar dakinta, Abba ya kalleta dakyau yaga jikinta yayi sanyi, Kamar akwai abinda yake damunta yace “Momy bakyajin dadi ne?”

Juyowa tayi “lafiya ta kalau Abba, kaina ne yake ciwo kadan”

“Momy ko mutafi asbiti?”

“A a Abba na, karka damu ai Nihla tana nan”

Yace”To shikkenan Momy, Allah yasawaqe “
Momy tashige dakinta tafada duniyar tunani, tunda Nihla tayi mata magana akan sunyi maganar Yusif da babanta shikkenan ta saddaqar Nihla bazata auri Abba ba, bazata auri danta ba, ahankali tatashi tasha magani, sannan ta kwanta

Abba kuwa dakinsa ya koma yadauko wayoyinsa, yana futowa daga dakin yaga wayar Nihla akan kujera, mamaki ya kamashi, yaushe tadawo falon?

Hanyar kitchen yanufa yaleqa kansa yaganta a kitchen tana kokarin kunna gas
Bece da’ita komaiba, ya koma falon yadauki wayar tata batare da tunanin komai ba yahadata da bangon falon ya doka, nan take wayar tafashe tayi raga-raga????????‍♀️

Yajuya yafice daga falon, yahau Mota yanufi gidan Aslam

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“congratulation Adam, matarka tana dauke da juna biyu Tsawon wata uku”

Adam yasaki murmushi yace “Doc da gaske kake?”

“qwarai kuwa, haka bincikenmu ya nuna, sannan wannan zazzabin datake fama dashi da amai, insha Allah zata denaji, karkuma kuyi wasa da bata magungunan da aka rubuta muku”

“insha Allah Doc. Nagode sosai”

Kallan Diyana yayi da aka yiwa qarin ruwa, tana bacci, saida Ruwan yaqare sannan yakira Doc aka cire mata, sukayi shirin tafiya gida

Kamota yayi ya rirriqe yana ta mata sannu, ta kalleshi tace “ya Adam sai farin-ciki kake, bayan kuma kasan banda lafiya”

“aidole nayi farin ciki maryam, kinsan me Doc yace kuwa?”

Shiru tayi masa, Dan a tunanin ta baidamu da rashin lafiyar tata bane, Motar tabude tashiga, shima yashiga sannan tace “ina Zan sani saika fada”

Cikin murna yace “to cemin yayi matata maryam tana dauke da Baby na acikinta na wata uku”

Cikin sauri ta kalleshi tace “da gaske?”

“sosai ma kuwa, bari mu koma gida nakira su Aslam da mama nafada musu”

“yanzu ni ahakan ciki ne dani?”????

“maryam kenan kina mamaki kenan, aike yanzu kin zama sarauniya maryama sai abinda kikace”

Shiru tayi masa tazuba masa ido tana kallan yanda yake farin ciki, Allah sarki ya Adam, rayuwa kenan

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kasancewar jirgi suka biyo ko awa daya basu yiba suka sauka,baba yayi mamakin zuwan su Tun lokacin dasuka kirashi awaya

Afalon gidan aka saukesu, mamy takawo musu abin motsa baki suka gaisa dasu, sannan ta basu waje

Sosai suka gaisa da baba, Inda suka sake bashi hakuri akan abinda yafaru abaya, baba ya nuna musu Babu komai dama basune sukai masa laifin ba, amma komai yawuce insha Allah

Yusif ne yashigo falon yayi kyau cikin qananun kaya Baqin wando da farar riga an rubuta handsome agaban rigar
Ido biyu sukai shida Abba, kowa ya kawar da kansa

Tunani Abba yafara, kenan gida daya take rayuwa da wannan gayen, shima Yusif din anasa bangaren tunani yake menene yakawo wadannan gidansu

Ahankali yaqaraso wajansu yamiqa wa Aslam hannu suka gaisa
Sannan yabawa Abba hannu yana kawarda kansa gefe

Shima Abban kansa ya kawar gefe sukai musabaha ahaka ????

Baba yayi shiru yana kallon su, gaisawa suke amma kowa fuska adaure, kuma kowa ya kawar da kansa basa kallan junansu

To tabbas da wani abu aqasa, duk yanda akai yarannan sunsan juna, sannan shi Yusif yayi masa maganar Nihla, ga kuma Abba shima yazo domin gyara laifin dayayi abaya, da alama shima da wani abu a tsakaninsa da yarinyar, to daga nanfa baba yafara tunanin akwai matsala

Suna gaisawa dasu yawuce dakinsa, suma su Abba basu jimaba suka dauki hanyar Airport domin komawa kano

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Azaune take aqasan kafet din dake malale acikin qayataccecn falon na Momy datafe kanta da hannunta guda daya tana kuka, dayan hannun kuma ta riqe fashshiyar wayarta dashi, ba fashewar wayar ce tasa ta kukaba, Information dinta dayake ciki takewa kuka, saboda idan waya ce akwai Sabuwar da ya Yusif yakawo mata, kuma akwai tsohuwar wayarta ta farko duk suna nan

Allah ne yakawo su Usman gidan gaba dayansu

Ya Aliyu ya kalleta yace “Momy me aka yiwa wannan yarinyar ne take kuka?”

“wallahi Aliyu futowa mukai falon nida ita shine mugaka wayarta afashe, shine take kuka”

Ya Usman yace “subhanallah… To garin yaya ta fashe Momy?”

“yaya ma za’ai kayimin wannan Tambayar Usman, Abba zai fasa mata wayar nina sani”

Farouq yace “haba Momy, ya za’ai yafasa mata waya, Abba bazai yi hakaba, da hankalin sa dakomai yazaiyi yafasa mata waya”

Momy tace “a a Farouq rabu da shiru-shiru, rabu da shiru-shiru farouq, dukanku nice na haifeku Babu Wanda bansan halinsa ba acikinku, nafada muku Abba ne yafasa wannan wayar”

Suna wannan zancen yashigo cikin falon, yayun nasa yagaisar sannan yace “Momy nadawo”

Momy tace “naganka ai Abba” ????

Ya Usman yace “Abba meyasa kafasa wa yarinyar nan wayarta, saboda me haka kawai zaka fasa waya?”

Juyawa yayi ya kalli Nihla datake goge hawayen idonta, haushi ya kamashi, saboda yafasa wayar da saurayinta yake kira shine take wannan uban kukan

Yamaida kallansa ga Usman yace “ya Usman ni ban fasa mata waya ba” yanemi waje Yazauna yana cire jacket din saman suit din jikinsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button