DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

“Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, Aisha, haba Aisha, meyasa zaki tafi kibamu, me.. Yas..sa Aisha” ya qarasa maganar yana kuka wiwi, sake rungumeta yayi yana fadin “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, yanzu Aisha dama tafiya zakiyi kibarmu?”

Cikeda tashin hankali tafara girgiza kanta “A a baba, Diddi bata mutuba, lafiya fa muka kwanta, baba Diddi na bata mutu ba kadena cewa tamutu baba”

Cikin kuka Kamar ba babanta ba yadago kansa ya kalleta yace “Nihla Aisha tamutu, Aisha tatafi ta barmu”????

(sannu sannu bata hana zuwa saide adade ba’a jeba, dafatan kun gane)

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/16, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️ DANGI ‘DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

9&10

Kuka take sosai Kamar ranta zai fita, wai gawar Diddi ce a gabanta Akwance haka, akan idonta makotansu da wasu daga cikin yan’uwan babanta sukayi mata wanka, bata taba tunanin zataci gaba da rayuwa batare da Diddi ba, babu me iya bata hakuri saboda kowa yasan yanda tashaqu da mahaifiyarta, gara abarta tayi kukan ko zataji sassauci

Dole saida aka jinkirta jana’izarta har saida yan kano suka qaraso, dirin motar da sukaji ne ya tabbatar musu da cewa sun qaraso, gaba dayansu sunzo yara da manya, Momy tana kuka tashigo gidan, duk hankalin mutane ya koma kanta, cikin dakin tashige, tana ganin Diddi Akwance anrufeta da farin mayafi tasake sakin kuka tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, Allah yaji qanki Aisha”
Nihla ta kalla datake zaune agefe idonta ya kumbura gashi sunyi jajir, Dasauri ta rungumeta, tana bubbuga bayanta “Nihla kidena kuka kinji, kidena kuka bakiyi rashin uwaba, kina damu kinji yata, kidena kuka”

Duk dakin saida suka sakasu kuka, Alhaji ne yashigo Wato yayan Diddi taredasu Alhaji Baqir gaba dayansu, tsugunnawa yayi agaban gawar, yasaka hannu yabude fuskarta, duk jajircewa irinta Alhaji, saida yayi kuka, yasaka dayan hannunsa Yarufe fuskarsa yana kuka sosai, yakasa magana, yadade yana tsugunne a gabanta, Alhaji Baqir da Alhaji Basiru suka jashi, suka fita dashi, sannan sukayi mata addu’ah, aka qarasa shirya ta, ana daukanta za’a fita da ita waje domin sallah Nihla tasaka kuka ta qanqame Momy tace “Anty zasu tafi da ita”

Kasa magana Momy tayi,domin itama wani irin d’aci takeji aranta

Babu yanda suka iya, haka aka sallaci Diddi aka kaita gidanta na gaskiya, saide muce idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani

Ranar da akai sadakar uku data bakwai, da yamma lis yan kano sukai shirin tafiya gida, Momy tana zaune da carbi ahannun ta, wayarta ce tayi qara, wayar tana ajiye kusada Nihla, daukar wayar tayi taga ansa Daddyn Abba hakan ya tabbatar da cewa yayan Diddi ne yake kira, meqa mata wayar tayi tace “Anty Daddy yana kiranki”

Karbar wayar Momy tayi, Cikin ranta tace Daddy.., taji dadin yanda Nihla tace Daddy, amma ita Anty ????????‍♀️, batasan meyasa Nihla take kiranta da Anty ba, kokuma har yanzu bata bata matsayin uwa bane a gareta?

Kawar da tunanin tayi aranta tadauki wayar “ki dauko Nihla kufuto mutafi”

Abinda yace da ita kenan, tace “to” tareda kashe wayar, farin ciki yakamata, ta kalli Nihla tace “Nihla tashi ki sauya hijabi mutafi, tare dake zamu wuce”

Batayi tunanin komai ba ta shiga daki ta sauya hijabin jikinta, sannan tadauki wasu kayan acikin jaka sukayi sallama da sauran yan’uwan babanta suka futo

Motoci uku suna jere akofar gidan, suka nufi daya daga ciki, hannunta yana cikin na Momy, Daddy yatashi yayiwa sauran mutanan wajan sallama, amma kokadan baiyiwa Baba magana akan Nihla ba, kawai de yace musu su suntafi, baba yakasa magana, yayi shiru yana kallansu har suka shiga Mota, akan idonsa aka tafi da Nihla, amma bai nuna komai ko akan fuskarsa ba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Sai dare suka qarasa kano, agate din gidan sukai Parking gaba dayan motocin, zubawa gate din ido tayi, shi kadai ma abin kallone
Ana bude musu gate suka shiga gidan
Anan taga Inda duniya take, Kamar gidan turawa,part hudu ne manya manya agidan, saide akwai nisa sosai a tsakanin kowanne parta, ga kuma Parking space dayake cikeda manyan motoci

Futowa sukai daga motar, kowa yanufi hanyar part dinsa, Alhaji Basiru yace “Nihla sai gobe yan’uwan ki zasuzo ki gansu kinji?”

Daga masa kai kawai tayi, Momy taja hannunta suka nufi nasu part din, suna shiga taga falon yahadu, komai ya tsaru yanda yakamata

Zama sukai dukansu afalon,Usman ya kalleta yanaso yaja hankalinta tadan sake tadena tunani yace “to yar’qauye tazo birni sai kalle kalle take, Momy wannan yarinyar fa sakina rufe mata ido wani lokacin” ????

Murmushi Momy tayi “eh lalle Usman bakason auren naga alama, karfa kazo kana kuka nabaka ita”

Daria sukasa gaba dayansu harda Nihla, Aliyu yace “haba Momy, kirasa wazaki bawa sai yaya Usman? Ai yayi mana tsufa Momy”

Dasauri farouq yace “eh dama ai kasan Nihla tawace, ni Momy zata bawa ko Momy?” ya qarasa maganar yana kallan Momy

Tace “duk ba Wanda Zan bawa, ni mijin yata saiya kasance Mai tsananin sonta kunji ko, bazan badata a araha ba”

Alhaji ne yashigo dauke da sallama, dukansu lokaci daya suka nutsu, yakalli Momy yace “Hajiya nina shiga daki, akula da wannan yarinyar”

Saida Momy tayi Murmushi sannan tace “to Alhaji”

Farouq yace”momy nizan wuce gida, nagaji sosai “

Aliyu yace” yes amarya tana jira “

Daria yayi yace” bakada dama yaya Aliyu, “yakalli Nihla yace” my Sister Zan gudu gida, kinsan momynki ta dade da bawa wata ni, idan kin gama hutawa sosai agidan, ki dauki wayar Momy kisaka number ta, ki kirani Muje nakaiki yawo kiga gari, sannan muyi shopping kinji ko? “

Saida tayi Murmushi Mai kyau dimple dinta suka futo sannan tace” to yaya farouq “
Usman yace” eh lalle farouq da alama wani zaiyi kishi dakai idan yadawo “????

Nihla bata fahimci komai ba akan maganar Usman, Momy de ta fahimta Dan haka tayi Murmushi

Aliyu ma yayi daria yace” saide ayi Yaqi, ba zamu qi kyautatawa yar qanwar mu ba, “
Yamaida kallansa ga Nihla yace” Nihla kina jina ko?, nima idan kin gama hutawa ki kirani nazo da kaina nadauke ki Muje wajan telan mata ta yayi dinki masu kyau “

Usman yace” to nikam Babu ruwana, zanyi rabiya a tsakani, kada naje nashiga ciki wataran Pilot Yaqi ragemin hanya zuwa Saudia “????

Momy tace” Usman baka isaba, bawani rabiya da zakayi, nagane ka, Wato wayo ko? “
Yace ” Momy kinsan de halin mutumin naki ko,?amma shikkenan nima idan tagama hutawa zanzo gidan sai abinda tace tanaso da kanta insha Allah “

Momy tace” eh naji “

Daga nan sukai musu sallama kowa yatafi gidansa, Momy tana qara jin dadin yanda kan yaranta yahadu sosai, kuma tasan ba komai yasa sukewa Nihla wannan wasan ba sai don tasake dasu ne ta kuma kwantar da hankalin ta.

Kallan Momy tayi tace” Anty wai duk sunyi aure ne? “

” sunyi aure Nihla, ni kadai ce agidan yanzu, saikuma ke dakika dawo, shi Abba yadade da gama karatu harma yafara aiki, shida Aslam, basu saka ranar dawowa bane, yanzu haka Alhaji yahana afada musu wannan mutuwar amma da yanzu kin ganshi “

Tace” to Anty Allah yabasu zaman lafiya “

” Amin Nihla, tashi Muje kiyi wanka kici abinci saiki kwanta ko? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button