DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Hawaye suka silalo daga idonta, muryarta ta sauya tace” to baba “

” yawwa Allah yayi miki albarka “

“amin baba”

Daga nan sukai sallama, tayi shiru tana goge hawayen idonta, yanzu ashe dama shiyasa Momy ta barta awajan ya Abba, wani hawayen yasake zubo mata, Allah sarki ya Yusuf, haqiqa tayi rashin masoyi, yasha wahala akanta, tasa hannu tashare hawayen

Ahankali Abba yadubi Aslam yace “dan tsaya Aslam”

Babu musu kuwa ya tsaya, yabude gaban motar yafuto yadawo baya wajan ta Yazauna, Aslam yayi Murmushi yadauke kansa yaci gaba da driving

Sake matsawa yayi jikinta, tanajin yanda jikinta yake gogar nasa, yasaka hannunsa ta bayanta ya rungumota jikinsa, batada zabin daya wuce ta dora kanta akan faffadan qirjinsa

Bayanta yafara bubbugawa Ahankali, yasunkuyo da kansa dede kunnanta cikin rada yace “kiyi hakuri kidena kuka kinji, kukan ki yana tabamin zuciyata, kiyi shiru, kinji?”

Ahankali tadaga masa kanta, wani irin dadi Abba yaji, yanda yaga lokaci daya taji maganarsa

Cikin kunnanta yadora bakinsa yace “kin hakura?”

Wani irin abu taji yana yawo a jikinta, kode ya Abba ya Manta da ya Aslam ne, ahankali ta janye jikinta daga nasa

Shima sai murmushi dayayi, yamatso kusa da Aslam yace “Abokina ina Abba nah”

Aslam yayi Murmushin waskewa yace “kaiko, Hmm”

Dahaka suka qarasa cikin gida, suna zuwa tabude motar tafuto jikinta asanyaye, tayi part dinsu

Momy da Daddy na zaune afalo, Adala tana gefen Momy tanayi mata lissafin abubuwan dazata siyo mata, haka Nihla tazo ta samesu, cikin ladabi ta gaishe su tareda zama aqasa

Momy tace “a a, yana ganki yanzu, yanxun nanfa nake cewa Alhaji yatashi mutafi”

“Momy ai an sallamemu, yace yawarke”

Daddy yayi Murmushi, a lokacin suka shigo falon shida Aslam, suma gaida su sukai suka zauna aqasa

Daddy yace “Abba ashe jiki yayi sauqi”

Lallausar sumar kansa ya shafa yace “eh Daddy”

Yace “to Alhamdulillah, Dafarko de kayiwa Allah godia, sannan ka godewa Aslam,idan da hali ma kayi masa Babbar kyauta ????sannan kaida Aslam din Idan jikinka yagama warware wa kushirya kuje can Abuja kuyiwa yaron nan Yusuf godia, yayi mutuqar kokari kuma yayi maka halacci, sannan dazu mahaifiyarka tayi waya da Ibrahim ta sanar dasu ka farka, sunce asaka musu lokacin da za’ayi biki yan’uwan mahaifin ta zasuzo daga jigawa ahadu anan, na Abuja ma zasu so gaba dayansu duk ayi komai anan, nikuma nafada musu nasaka sati daya, saboda haka sai kayi kokari zuwa next week din kagama shirya komai, saiku tare a gidanku “

Cikin farin-ciki yadan sosai qeyarsa yace” to Daddy insha Allah”

Sannan yakalli Nihla yace “kinji abinda yafaru ko?”

Tace “naji Daddy”

“to kiyi hakuri, ki qara akan Wanda kikai abaya, Allah yabaku zaman lafiya”

Tace “amin Daddy”

Momy ta miqe tace “Nihla taso Muje kitchen”

Bayan Momy tabi abaya, suna zuwa kitchen Momy tabata wani magani tace “kisha wannan yanzu, sai kici abinci kishirya kitafi gidan gyaran jikin”

Cikin ladabi tace “to Momy” tadauka tafara sha tana tunani aranta, Ilham tabata, Momy tana qara mata wani itakam yaya zatayi?
Momy ta kalleta tanajin tausayin yarinyar, gani take Kamar ba’a kyauta mata ba, Allah yasa de taso Abban nata, koda yake tasan Abban ma da naci, zai rarrasheta

Bayan tagama sha tawuce dakinta tazauna agefen gadon tana tunani, yanzu haka aure ne akanta fa, ashe yaya Abba yasani shiyasa yake min wasu irin abubuwa a asbiti, tatuno lokacin da ya Aslam yake cemata yaya marar lafiyarta, Hmm ashe duk sun sani, wayarta tadauka takira Anty Nadiya tabata labarin komai, nan take Nadiya tace zatazo bikin itama domin ta nemi yafiyar sadeek, tayi musu ala sanya alkhaairi, bayan sun kashe tatashi tashiga wanka, tafuto ta shirya tsaf taci abinci, sannan tayiwa Momy sallama tatafi driver yakai ta gidan

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Sai bayan sallar ishsha’i tadawo gida, zaune suke afalo su biyu shida Momy, Momy tana bashi coffee abaki, sallama tayi tashigo cikin falon idonsa yasauka akanta, doguwar riga ce a jikinta Mai godon hannu amma rigar abaje take sosai, ya dinta yanada santsi Kamar na abaya, da mayafin rigar tayi amfani tayafa akanta sauran kuma ta zuba shi baya, dukda fadin rigar hakan bai hana ka hango bajajjan hips dinta, yayinda cikakken qirjinta yadago ,hakan yasa cikinta shafewa, da yar qaramar jakar ta a hannunta

Cikin ransa yafara magana

ya’ilahi! Yanzu haka duk anganta ahaka, amma yaya zaiyi? Bazai iyamata magana ba tunda shine yake neman sulhu

Zama tayi akujera kusa da Momy, tace “wash Allah Momy nadawo”

Zaman datayi awajan kawai wani irin qamshi na daban yake tashi, ahankali ya lumshe idonsa sannan yabudesu

Momy tace “Sannu Nihla, ai gara da Allah yakawo ki, zanje in dubawa Alhaji wasu takardu, karbi wannan coffee din kibashi”

Baki taturo gaba alamar bataso, ita Momy batasan halin ya Abba ba, kawai shagwaba ce take damunsa, amma aiya warke
Haka tasa hannu ta karba Momy tashige dakin Daddy tabarsu anan

Gyara zaman sa yayi akan kujerar ya dauki fillo din kan kujera yadora a cinyarsa yazuba mata ido yana murmushi
Gaskiya yaji dadin abinda Momy tayi, wani irin nishadi yakeji aduk lokacin dasuka kasance su biyu shida ita

Kallanta yayi yace “zeyi sanyi fa”

Dago idonta tayi ta kalleshi, ta janye idonta, sannan tamatso kusa dashi ta diba a Spoon din takai bakinsa, Dan qaramin bakinsa yabude tasaka masa Spoon din, yanasha ya lumshe idonsa, haka taci gaba da bashi yanasha harya qare tas, bedena bude mata bakin ba, ta kalleshi tace “yaqare”

Murmushi yayi yace “bazan samu qari ba?”

Tashi tayi tsaye kanta tsaye tace “eh”

Cikin sauri yasauko daga kan kujerar yace “kawo nariqe miki jakar to Muje dakin”

Babu musu tabashi handbag din nata , shikuma yabita abaya har cikin dakinta

Abakin gado tazauna shikuma Yazauna aqasanta tareda dora mata jakar akan cinyar ta, bayan yadora mata jakar a cinya memakon yadauke hannayensa sai yabarshi akan cinyar tata, bayaso kokadan yadena jin wannan qamshin nata dake rinjayarsa

Nihla tarasa yaya zatayi dashi, ahankali tace “inaso ne nashiga wanka”

Yace “akwai maganar danake so muyi”

Fuskarta Babu yabo Babu fallasa tace “to”

Kallanta yayi yafara tunani, yarasa meyasa har yanzu taqi sakin jikinta dashi, idan yadubi qwayar idonta yana hango rashin sabo atattare da’ita, kokuma har yanzu bata yafe masa bane bai saniba

Ajiyar zuciya yayi, cikin maganar sa Ahankali cikin sigar rada, Wanda dagashi sai itane zasuji yace “ina qara baki hakuri akan abubuwan dasuka faru abaya …. Nihlaaa! “
Yaja sunan nata
Sannan yaci gaba da cewa “Wallahi yawancin kowanne dare bana iya kwanciya harna samu nayi bacci saboda tunaninki, koda yaushe jinake inason ganin ki a kowanne lokaci, duk lokacin dana kasance tare dake inajin wani irin dadi acikin zuciyata, abaya nayi kuskure dana kasa bawa wadda nashaqu da’ita kulawa harta hakura dani,domin kuwa nagama ganewa shaquwa ce kawai tasa na furta mata kalmar soyaiya, amma soyaiya daya Tun ta yarinta ta kena bawa Nihla….. a yanzu nayi miki alqawarin Zan kula dake fiyeda yanda Zan kula da kaina, kiyi hakuri kiyafemin kisaki jikinki dani please “

Shiru Nihla tayi bayan tagama jin duk bayanin sa, Kamar ba shiba wani lokacin idan Yazauna yana yimata wasu abubuwan

Ganin tayi shiru ba tace komaiba yasa shi motsa hannunsa dake kan cinyar ta, ahankali yafara shafa cinyar ta, kasancewar rigar jikinta me santsi ce saitaba shi damar shafa cinyar tata dakyau

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button