DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Dida tayi Murmushi tace”amin ya Fawaz, Wato harka huduba ko”

Yace “yes, Adam bai qyamaceni ba shida Diyana, basu qi halaiyata tadaba suka sakawa dansu sunana, kinga nima tunda Allah yabani ai sai nasaka sunansa, shikuma Aslam saboda zumunci nasaka, da sunan Abba zansa, but kinga already Aslam ya rigani”

Tace “hakane, to Allah yarayasu yasa suyi halin masu sunansu”

Yace “amin Dida ta”

Sunje asbiti andubata anbata magunguna, sannan an rubutawa yara madarar dazasu dinga sha saboda itama tadan huta wani lokacin

Kafin azahar kuwa gidan Dida yacika taf da jama’ar Mazawaje family

Ranar suna kuwa yara sukaci sunan Adam da Aslam, Babban shine Aslam, qaramin kuma Adam, wannnna karon ma hajiya Na’ila mamansu Aslam itace kan gaba akan komai, saboda anyiwa yayanta duka biyun takwara, gaba daya tahana iyayen Dida da Fawaz komai itace takeyiwa yarinyar abubuwan daya dace

Yaran kuwa basa zama ahannun Dida, kowa daukar su yake, da Dida da Diyana da Ilham da Nihla duk suna zaune awaje daya
Aka umman Fawaz takawo wa Dida yaran tana basu nono suna sha, sai runtse ido take

Nihla tace “tab wannan azaba har ‘ina, sannu Dida”

Ilham tayi dariya tace “idan tasaba ai shikkenan, yanzu de saura ke, zamu ga me zaki haifa, Dan Allah ki haifo wa Abba na matar aure”

Diyana tace “a a wallahi, Fawaz dina yarigashi, haka kawai wani Abban ki, yaro yana tafe shiru shiru kana ganinsa kaga halin takwaransa” ????

Dariya sukasa Ilham tace “wallahi kuwa kamar kinsani, har mamaki nake, shegen son girma ne da lil Abba, haka kawai zaiyi wa ya Aslam shiru idan yana masa magana, shida kansa ya Aslam rannan haka yace yaga alama lil Abba de yadauko halin ya Abba”

Dida tace “to aiga yan biyu sunzo, saisu raba muku gardama, tana haihuwa sun samu matar aure” ????

Nihla tace “oh, Tun kafin na haihun har akewa yara kamu? ????
Abinda cikin watansa biyar bamusan mezan haifa ba?”

Diyana tace “insha Allah ma matar lil Fawaz zaki haifa” ????

Haka sukaita firarsu abin sha’awa, har dare yayi sannan kowa mijinta yazo yadauketa

Nihla suna hanya ya Abba yadubeta yace “dazu mudasu Aslam muke cewa kema yakamata ki haifi namiji, tunda duka jikokin Abubakar Mazawaje maza suke haifa, abin Kamar alamara kowa namiji namiji, shi Fawaz ma daya fimu aiki yasamu biyu” ????

Nihla tayi Murmushi tace “kuma ashe kunyi zancen, mumafa adaki haka suka sani agaba wai kowa sai cewa yake idan na haifi mace to wallahi dansa na haifawa mata” ????

Ya Abba yayi Murmushi yace “sunada gaskiya, amma ni idan namiji kika haifa ma sunan Yusuf Zan saka”

Tace “to Allah yakawo nagari”

Haka suka qarasa gida suna firarsu cikeda kulawa

Cikin Nihla yana cika wata tara Momy tace akawo mata ita gabanta, haka suka sake dawowa gidan Momy
Saida tayi kusan sati biyu agida, sannan Allah yakawo tata haihuwar, tana fara naquda kuwa Momy da Abba suka tafi asbiti da’ita, dakuma kayan Baby, amma da sukaje sai likitocin sukace haihuwa tukunna

Gaba daya Nihla ta jigata, ya Abba sai sintiri yake Yaqi zama, suda sukazo da azahar har wajan magrib tana abu daya, lokaci daya kuma suka fara jiyo kukan ta, Abba yatashi tsaye yanufi dakin haihuwar, Momy tayi sauri ta riqe shi, “ina zakaje haka Abba?”

Idanunsa suka cika da qwallah yace “Momy tanasha wahala wallahi… Sai sharrrr hawaye yazubo masa ????

Momy tace” toya zamuyi Abba, kayi mata addu’ah kajiko “

Suna tsaye shida Momy wata nurse tafuto hannunta dauke da Baby ta miqa musu tace” Hajiya tasauka lafiya, ansamu Baby girl “

Cikin sauri Momy ta karbi yarinyar tana murna, shikuwa Abba nurse din yanufa yace
” zamu iya ganin mamanta yanzu? “

Tace” kuyi hakuri tana dakin hutu, zaku iya ganinta anjima “

Dawowa yayi wajan Momy ya zubawa yarinyar ido, fara ce sol Mai mutuqar kama da Nihla, gata bulbul masha Allah, idonta abude sai kallansu take, sumar kanta yala yala da gashi

Momy tace” Alhamdulillah, yau su Abba anyi ‘ya, karbe ta mana kayi mata addu’ah “????

Ahankali yamiqa hannunsa ya karbe ta yace

“Welcom to the world DIDDI nah “

Momy tace “kayi tunani Mai kyau Abba na, amma yanzu de share hawayen naka” ????

Murmushi yayi yasa hannu ya goge idonsa, saida suka dauki lokaci sannan aka basu damar ganinta, tana zaune akan gadon ya Abba yadora mata yarinyar acinyarta, Nihla ta kalli yarinyar taji lokaci daya wata irin qaunar yarinyar aranta, ashe haka iyaye sukeji akan yayan su, nan take tafara yiwa Allah godia

Sai dare aka sallamesu, kai tsaye kuwa gidan Momy suka koma
Yan’uwa suka cika part din Momy, Ilham kuwa da Diyana da Dida dasuka zo dauke yarinyar sukai kowa yazo saiya fadi albarkacin bakinsa akanta

Ilham tace “wallahi jinake Kamar na dauketa gaba daya”

Diyana tace “kekoni, Kamar yar larabawa yarinyar wallahi” ????

Dida tace “a a ni zaku barwa yan biyu na sun samu qanwa” ????

Saida sukai kai dare awajan ta sannan suka tafi gida, Momy tana ganin take taken Abba takafa ta tsare iya karsa da Nihla saide in falo tafuto ????

Yauda safe ya shirya zai fita wajan Aslam, yashigo dakin nata yaganta tana bawa Baby nono, zama yayi kusa da ita yasaka hannunsa ya riqo waist dinta, yana kallan yanda take yatsina fuska
Yace “Sannu”

Hararar wasa tayi masa tace “duk bakai neba, kuma itama gashinan zata qarasa ni”

Yace “sorry, mun tuba”

Yasaka hannunsa yana shafa qirjinta Wanda take bawa yarinyar, sannan yafuto da dayan waje, yasaka harshansa yana lasa, Nihla bata hanashi ba, tabarshi Tun yana lasa yadawo yanasha ahankali, yanda yake sha ne ahankali yasa ta lumshe idonta, cikin muryar jin dadi tace “ya Abbaaaa… Saika shanye mata abinta ko…”

Shiru yayi yana tsotsa harda lumshe idonsa shima

Adede lokacin Momy tashigo dakin,qaran bude kofar dayaji ne yasa cikin sauri ya cire bakinsa ????

Yasunkuyar da kansa qasa yana sosa qeyarsa
Momy tace “Sannu Abba, sannu kaji” ????

Tashi yayi Cikeda borin kunya zai bar dakin, Momy tasake cewa “Allah yakiyaye hanya, mujima da yawa”
Shide yayi wuf yafice daga dakin

Tadawo da Kallanta wajan Nihla tace “idan kika biyewa jarabar Abba ko shekara ba zakiyi ba zaki sake daukan wani cikin, kinde ji abinda akeji awajan haihuwar”

Nihla tayi shiru kanta aqasa, ga wata kunya data rufeta, shima kansa gogan yaji kunya bare ita

Ranar suna yarinya taci sunan Aysha, amma Suna kiranta da Diddi
A family house din akai taron sunan, gidan yacika sosai, kowa sai daukan yarinyar yake, Muddin ka dauketa sai kaji tashiga ranka, Mamy batazo ba amma taturo Rafi’ah wajan sunan da kayaiyakin barka, saikuma baba dayazo ganin jikarsa da kansa, kuma Sabuwar matar sa

Rafi’ah ma tana dauke da nata cikin na wata shida, amma haka ta daure tazo tunda mamy bazata samu damar zuwan ba

Tunda aka gama taron suna Momy tafara gyara Nihla, ciki da waje datage tana gyara yarta

Saida sukai Arba’in sannan sukai shirin tafiya gidansu

Tun safe kuwa Abba yagama shirya wa su kawai yake jira, Momy ta kalleshi ta girgiza kanta tasan cewa yau sai Nihla ta yabawa aya zaqin ta ????

Saida suka futo, zasu tafi Momy tace “to kokun Manta da Little Diddi ne?”

Gaba dayansu sai kunya ta kama su, Abba yakalli Nihla yafara borin kunya, yace “Dama baki goyata ba kika futo?”

Nihla tayi masa wani irin kallo tace “ba kaine kake ta cewa nayi sauri ba”

Ta kalli Momy tace “Momy ina take?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button