DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Watan ta d’aya agidan tafara sakewa, kuma tagama gane halin kowa, nacinda Ilham take mata ne yasa suka saba da ita sosai, Dida da Diyana ma suna zuwa, saide Dida tafita zuwa saboda Diyana kullum tana wajan yawo, yawon ma bada yan’uwanta mata ba, maza!

Su yaya Usman da Aliyu fa farouq sosai suke nuna mata gata, Aliyu yakai ta anyi mata dinku na masu kyau amma kullum tana cikin hijabi, da wahala ka ganta tazauna haka Babu hijabi, haka yaya farouq yakai ta shopping tasiyo kayan kwalliya ta jeresu agaban mirrow din dakin nata, Yaya Usman kuwa Sabuwar waya yasiya mata qirar iphone Mai tsadar gaske.
Rayuwar ta take hankali kwance, saide tunda Diddi tarasu wata nutsuwa tasake shigar ta, abu dayane yake damunta, tunda tabar jigawa kullum takira wayar Baba baya dauka, tarasa dalili, lafiya lafiya zata kira yan’uwansa su gaisa da ita amma shi idan takira baya dauka, idan tayi masa text baya reply, amma tasan koma menene zai iya neman ta daga baya, tasan Baba da wahala yayi fishi da ita Babu dalili.

Hisnul Muslim din hannunta datake karantawa ta ajiye tafuto falo, babu kowa da alama Momy ma tana daki, zama tayi acikin kujerun falon tana kallan tashar aljazeera

Wayar Momy dake gefenta ce tafara qara, Ahankali takai hannu tadauki wayar, sunan dake yawo a screen din wayar ta kallah taga ansa Abba nah, haka kawai ta tsinci kanta da faduwar gaba, cikin ranta ta furta “Yaya Abba”

Wayar tana gab da katsewa tayi picking call din tace “Hello”

Shiru yayi anasa bangaren, Idanunsa a lumshe, yana kwance akan katifar robar nan ta cikin ruwa, acikin swimming pool din gidansu, babu riga ajikinsa dagashi sai gajeren wando, gashi Mai yawa kwance akan qirjinsa, cikin ransa ya furta “Sweet Voice”

Shirun dataji anyi ne yasa tasake cewa “Hello” still aka sake yin shiru, hakan yasa takashe wayar ta ajiye ta

Sake qara wayar tayi akaro na biyu, adede lokacin kuma Momy tazo falon tazauna tareda amsa wayar “Abba nah”

“Momy shikkenan ni duk kinmanta Dani ko nemana bakyayi, babu wanda yake missing dina”
ya qarasa maganar cikin shagwaba

Murmushi tayi “Abba kacika rigima wallahi, idan nakiraka kuna aiki kace baka kusa, idan naqi kira kace bana nemanka”

Shiru yayi Bece mata komai ba, baisan mezai cemata ba,itama tasan hali Dan haka tace “yaya aiki, ina Aslam?”

“Momy Aslam baya nan yaje Indonesia,”

“haka kuka iya dai, yau wannan qasa gobe wannan, amma banda Nigeria”

Yasan sarai abinda take nufi Wato sunqi dawowa gida, Dan haka yayi Murmushi cikin aji yace “Momy toki shirya next week zamu dawo”

Cikin farin ciki tace “Alhamdulillah, Allah abin godia, da gaske Abba nah?”

“yes serious Momy, i will call you back” dif ya kashe wayar batare daya tambyeta wadda ta d’aga wayar tasa da farko ba

pls Karku Manta da Comments da sharhi ????????

Amnah El Yaqoub ✍️[6/18, 12:36 AM] El Yaqoub: ❣️ DANGI ‘DAYA❣️

{Romance &Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

11&12

“Anty dawowa zaiyi?”
Nihla tayiwa Momy wannan Tambayar

Zama Momy tayi cikin farin ciki “Nihla Abba zai dawo next week”

Lokaci daya farin ciki yakamata, finally yaya Abba zai dawo, cikin murna tace “Tome za’a shirya na tarbar su Anty? Medame yaya Abba yafiso?”

Hannayenta Momy takama Kamar qawarta ????tace “Yanzu de kije daki ki dauko memo saimu zauna narubuta miki abubuwan da zamu iya buqata, sai kuje keda driver kusiyo, abinci za’a hada Mai yawa yanda zai ishi kowa nacikin gidan nan”

Cikin murna tatafi dakin tadawo dauke da memo da biro tazauna kusa Momy, nan take Momy tafara rubuta mata abubuwan dasuke buqata, duk irin kalar Abincin da Abba yafiso saida Momy ta zayyanewa Nihla tas????

“to Anty naje nayi wanka saimu tafi?”

“A a kibari sai gobe, sai kuje gobe da safe kidawo da wuri”

“to Anty”

Murmushi Momy tayi Wanda yayi kama da yaqe tatashi tace”zanje sauran part din na sanar dasu “

Hankalinta ya koma kan tv, Dan haka ta cewa Momy” to Anty “

Fita Momy tayi cikin sanyin jiki, sai yaushe ne yarinyar nan zata dinga kiranta da Momy Kamar kowa? Anya kuwa Nihla tasan yanda take jinta aranta kuwa? Yanzu idan tayi baqi tana murna ta nuna musu ita cewa ga ‘yarta kai tsaye sukaji takirata da Anty zataji dadi? Me zatayi wa Nihla danta dauke ta amatsayin uwa?

Da wannan tunanin tafara zuwa part din hajiya Na’ila, da sallama ta shiga, hajiya na zaune itada Adam da Alqur’ani a hannunsa yana dubawa????
Gaisawa sukayi, shima ya gaida ta ciki girmama wa

Ta kalli hajiya Na’ila, “Hajiya munyi waya da Abba yanzu, yacemin suna nan zuwa Next week insha Allah”

Hajiya Na’ila tayi farin ciki, amma meyasa ita nata Dan bai kirata yafada mataba sai abakin facala zataji? Dama a family ana rad’e rad’in cewa angama shanye mata yaro, andauke mata shi ankai shi wata uwa duniya da sunan karatu gashinan Yaqi dawowa, nan take ta nuna bacin rai a fuskarta, Murya ciki ciki ta dubi Momy, “Allah yakawo su lafiya, nagode”

Jikin Momy yayi sanyi, tatashi tace “to sai anjima”

Tana fita Adam ya dubeta, “haba Dan Allah mama, meyasa kike hakane?” mutanan nafa sunyi mana komai, mijinta yayi muku kara yatura dansa da danki karatu, gashi nima nagama karatu na ina aiki na mallaki komai, to menene yayi saura awajan ki bayan godiyar Allah mama? “

” aikai dama ba dan agida na haifeka ba Adam to tabbas zan’iya cewa ansauya min kaine, da anfara magana zaka fara kawo aya da hadisi, Allah yace, annabi yace, tashi kabani waje, d’an kare me macacciyar zuciya Kamar ta ubansa “????

Tashi Adam yayi yace” nina tafi masallaci “????

Tsaki tasaki tace” haka de”

Washe gari Nihla ta shirya sukaje kasuwa itada driver da Dida, lafiya sukaje suka siyo komai suka dawo, saboda Dida Babu laifi akwai nutsuwa sosai duk family kowa yayi mata wannan shedar

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Bayan kwana bakwai wannan family ya haukace da hidima, kowa kaganshi yana cikin farin ciki sosai, part din Momy yacika da qamshi anata girke girke, Nihla da kanta ta shiga kitchen tace Momy tayi zamanta itace zata yiwa yaya Abba girki, Momy taji dadi sosai, Dan haka tatafi wajan ma’aikatan gidan domin ta sanar dasu suje su gyara wa Abba dakinsa, a bangaren hajiya Na’ila itama tanacan tana ta hidima

Diyana da Ilham da Dida ne suka shigo part din, dukansu kitchen din suka shige suka kama mata aikin
Sosai Nihla taji dadin zuwan su

Ilham tace “Nihla duk kinyi kaca-kaca a kitchen gaskiya kinaji da yaya Abba”

Nihla tace “ke kuwa qawana guda zai dawo ba dole ba”

Diyana taja kujera ta zauna “nikam nagaji wallahi, kugama nazuba naci” ????
Ta kalli Nihla tace “Kekuma Nihla yaya Abba ne qawanki?, lalle baki samu qawaba wallahi,aini dakika ganni nan gabana faduwa yake da dawowar su, saboda takura tadawo, harna fara blocking numbers din gayu, saboda idan sukazo gida Babu shakka wataran koshi ko yaya Aslam wani zai iya dukana”

Ilham tayi Murmushi tace “baki Manta marinda yaya Abba yayi mikiba ashe”

Nihla tace “au shi yaya Abban haka ya koma? Meyasa toni be taba nunamin ba?”

Diyana tace”inaaa ai zama ne beyi zamaba Nihla,???? shiyasa, amma kowa yasan halin yaya Abba a family dinnan, babu wasa, kwata kwata bayasan raini dagashi har yaya Aslam, shiyasa ma jinin su yafi haduwa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button