DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Kai tsaye wajansa tanufa, taja kujerar datake gefensa ta zauna ta kalleshi dakyau
” Ya Abba sannu da zuwa, mekake cine haka, kaga yanda ka sauya kayi fari ka qara kyau kuwa?”

Murmushin kefen baki yasakar mata “kema haka”

Abinda yace kenan

Murmushi tayi “haba de ya Abba wace ni? Gashinan kana nema ka kamoni fari”

tafadi haka tana matso da hannunta me dauke da dogayen yatsu kusa da nashi hannun, Dan yagani ya ban bance

Bin farar fatar hannun nata yayi da kallo, d’an siriri dashi, Wanda yake tunanin idan yayi mata kyakykyawan riqo zai iya karya ta ????????????‍♀️

Kafin yace mata wani abu, Daddy yayi gyaran murya ganin suna nema su Manta dasu awajan “Am yata zuba mana Abincin ko?”????

Tashi tayi tabude Abincin, babu kunya tafara Jan flet din gaban Abba tazuba masa, sannan tadauki na Daddy????

farouq, Usman, da Aliyu gaba daya suka koma yan kallo awajan, Aliyu cikin ransa yace anya idan Nihla da Abba suka fara soyaiya Momy zata iya bude idonta? ????

Saida tagama zuba musu sanan tazuba nata Dan kadan, sannan kowa yafaraci

abinci takeci amma hankalinta yana kansa, tana kallan yanda yake cin Abincin cikeda nutsuwa, Miqewa tayi tsaye Ahankali, tadauki just din dake gaban ya Usman ta tsiyaya a glass cup sannan ta tura wa ya Abba agabansa, takoma tazauna tanaci gaba da cin abinci, Aliyu da farouq suka hada ido tareda Jinjina kai ????
Gaba daya Babu wata damuwa aranta take nuna masa kulawa, sai tarairayarsa take Kamar Dan qaramin Baby

Tsawon lokaci suka dauka kafin su Gama, falo suka dawo suna kallo, su Usman sai tsokanarta suke suna janta da fira, ahankali yatashi ya kalli Momy “Momy zanje nayi wanka nahuta”

“to Abba nah,”

Wani irin kallo yayiwa Nihla Wanda ni kaina nakasa fassara shi, amma tabbas za’a sami matsala idan aka yiwa mutumin daya dade yana cikin soyaiyar ka “ina Diddi? Why bakizo da itaba?”

Gaba daya falon shiru sukayi, kowa yakasa bashi amsa
Shikuma ya tsareta da Idanunsa, dago kanta tayi ta kalle shi takasa magana, karkata kansa yayi alamun yana jiran amsa yace “uhm inajin ki”

Idanunta ne suka cika da qwallah, Ahankali ta dago kanta ta dubeshi “Diddi tarasu ya Abba”

“what?”

Dasauri ya kalli Momy yace “Momy, me yarinyar nan take fada haka?”

Jijjiga kai Momy tayi, alamun da gaske ne, Lokaci daya mutuwar Diddi ta dawowa Nihla sabuwa, da gudu tatafi daki tana kuka ????

Lokaci daya jikinsa yayi sanyi “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, Diddi tarasu, Momy meyasa baku fadamin ba? Haba Momy, meyasa? Innalillah…”
Yadafe kansa da hannunsa????????‍♂️ya koma kan kujera Yazauna jagwab

Dafashi Momy tayi “kayi hakuri Abba, Aisha ta rasu Sanadin zazzabi na kwana daya, Daddynku ne yace kada afada muku, hankalin ka zai tashi, addu’ah take buqata idan kuka dawo sai kuyi mata”

“Momy yanzu Diddi tarasu?ashe ganin qarshe nayi mata?”

Su Aliyu dake zaune jiki a sanyaye, sune suka fara bashi hakuri, sannan ita kuma Momy tabi bayan Nihla daki

Zuwa dare ta ware, tadan kwantar da hankalin ta tadena kuka a dalilin nasihar Momy, tana kwance agadon dakinta tana daddana wayarta, yauma takira ya yusif yafi sau biyar amma wayar taqi shiga, ko a wanne hali yake?
ta duba Agogon dakin karfe tara da arba’in da bakwai, Dasauri ta furta “kaiiii goma saura”

Dasauri taduro daga gadon tafuto falo, kitchen tashige tafara hada coffee Mai Dan karan dadi
Momy ce taji motsinta, ta furta alhmdlh aranta, tunda tasaki ranta harta futo falo

Kitchen din ta shiga taganta tana aiki “Nihla me kike hada mana ne da wannan daren?”

“Anty bafa mu nake hadawa ba, Ya Abba nake hadawa coffee, nasan zaiji dadinsa”

ha’ba Momy ta riqe, “to Allah ya temaka, nima kallo zanyi shine naji motsinki na futo”
Tana fadar haka tajuya zuwa falo

Itama Nihla tana gama hadawa tadauka adan qaramin tire, tazo tawuce tagaban Momy tashige dakin nasa, saura kadan tasaki farantin dake hannunta, saboda yanda taganshi dagashi sai gajeren wando ????, babu riga ajikinsa,gashi kwance a qirjinsa, yana kwance yana waya qasa qasa, batasan dawa yake wayar ba

Qamewa tayi a tsaye, takasa qaraso wa ciki, tayi dana sanin shigowa dakin nan nasa batare da nocking ba

shi kansa baiyi tunanin shigowar taba, futowarsa kenan daga wanka yasaka Dan gajeren wandon, ko shirya wa baiyi ba aka kira wayarsa shine yad’an kishingid’a yana wayar

cikin ransa ya furta “yasalam! Yarinyar nan kada ta raina shi fa” ahankali yatashi zaune tareda zubo qafafunsa zuwa qasa

Ya tsareta da ido Bece mata komai ba, hannunta ne yafara rawa, duk ta rikice, wanne irin qirji ne dashi haka me fadi? Duk Ta diririce tarasa me zatayi

Shima ya lura da yanayin data shiga, ko menene ya tsoratata take karkarwa haka? ???? ????
Ya tambayi kansa.

Cikin in-ina tafara magana “Am dama… dama coffee…”

“zoki ajiye”
Abinda yace da ita kenan

Ahankali ta taka ta qarasa wajansa, sai kawar dakai take, takasa kallansa, ta tsugunna ta ajiye masa agabansa tafuto da sauri

Binta yayi da kallo, to menene abin tsoro ajikinsa ? To kodan ta ganshi haka ne dukta tsorata? Tabe bakinsa yayi, sannan ya kalli wayar tasa yaga anma kashe, shima bai sake kiraba yayi wulli da wayar yadauki coffee din data kawo masa

Tana futowa daga dakin tazauna afalo kusa da Momy suna kallo, amma gaba daya hankalinta bayakan kallan, ????

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tsawon satin su biyu da zuwansu , koda yaushe da irin kulawar da Nihla takewa Abba, zuwan yanzu kam, kowa yasan cewa Nihla nason Abba, Shidinne de suka rasa gane Inda yadosa

Alhaji ne yashigo falon nasu dawowar sa kenan daga wata tafiya dayayi, Momy tanayi masa sannu da zuwa, ya amsa mata, yana zama akan kujera, “ina ya rannan ne?”

“Nihla bata nan taje wajan Ilham, Abba kuma ni Tun safe ma banganshi ba “

Wayarsa yadauka ya kira Abban
” kazo kaida Aslam ku sameni agida yanzu, kokuma ka turomin shi “
Yana fada masa haka ya kashe wayar

Basuda dauki lokaci ba sai gasu sun shigo shida Aslam din, cikin ladabi suka tsugunna agabansa bayan sun gaida shi,Alhaji ya dubesu ” Aslam inaso ka shirya kaje India ka dauko Aisha daga makaranta, munyi magana da abokina cewa harma tarafa university, to Zan turoma adress din gidan, saika shirya kaje kutaho tare “

Momy ta kalleshi tace ” Amma Alhaji lafiya kuwa? “

” lafiya kalau Alhamdulillah, kawai de lokacin karanta wasiyyar hajiya ne yayi, tunda Allah yayi mana Tsawon rai, gara intara kan kowa na family a karanta wasiyyar agabansa “

Momy ta Jinjina kai, tace” hakane, Allah Mai iko, kwanci tashi kenan “

Beyi mata magana ba, yadubi Aslam din yace ” shine kiran dama, ka shirya katafi, ka tabbatar kun dawo akan lokaci “

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

” gaskiya Ilham akwai matsala “

” matsala kuma Nihla? Allah yarabamu da matsala, ????
Meyake faruwa? “

” Ilham ina tunanin son yaya Abba nake wallahi, shikuma naga Kamar hankalinsa baya kaina, ina yawan tunanin sa, sannan ni Tun ina qarama nakasa mantashi a raina, Ilham ina tsoro kar yaya Abba Yaqi saurara ta “

” soyaiya Nihla? Kuma ma da yaya Abba? Anya baki debo da zafi ba Nihla? “

” nima abinda nake tsoro kenan Ilham, bansan ya zanyi ba wallahi “

” kinga ki kwantar da hankalin ki, shima nasan Babu yanda za’ai yaganki amma baiji aransa cewa yana sonki ba,Nihla Allah yamiki kyau, sannan kuma ke dashi duka DANGI ‘DAYA ne, bazai qikiba, dan’uwanki ne, tunda duk cikin mu Babu Wanda yake sakewa da’ita Kamar ke, amma idan zaki iya to kiyi masa maganar mana “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button