DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Kai tsaye tace” bazan iyaba Ilham, yanamin mugun kwarjini wallahi, kullum naganshi agabana ma gabana tsananta faduwa yake, sannan yana cikamin ido, koba wannan bama bazan iya tunkarar namiji da wannan maganar ba “

Ilham tayi ajiyar zuciya,” hakane kam,gaskiya gara shiya fara furta miki, amma mezai hana cikin siyasa kifara nuna masa? “

” to ta wacce hanya kenan Ilham? “

” kulawa, kidinga bashi kulawa yanda yadace “

” Ilham duk Wanda Yazauna a part dinmu zaisan cewa ina bawa ya Abba kulawa ta gaske, saboda haka kicire kulawa a lissafi”

Girgiza kanta tayi tace “gaskiya ne wannan, nima shedace, ke kinga mudena bata lokacinmu akan wannan tunanin, duk miskilancinsa qarya yake ya juyawa mace Kamar ki baya Nihla”

tace” da gaske kike Ilham? “

Girgizakai Ilham tayi,” da gaske nake “

Cikin farin ciki ta rungume Ilham

(to ko yaya zata kasance?ko yaya bayanin wasiyya? Fatana kuci gaba da kasancewa Dani)

Kada amanta da sharhi da Comments ????????

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 12:52 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

13&14

Bayan kwana biyu Aslam ya shirya yatafi India domin tahowa da Aisha, yaso sutafi tareda Abba amma sai Abban Yaqi
Yana sauka a Airport yakira number da Daddy ne yaturo masa amma wayar taqi shiga, haka yadinga tsaki shi kadai
Daga qarshe saiya kira Daddy yafada masa, a lokacin Daddy yasa Alhaji Basiru yatura masa number Aisha

Aslam na ganin number nan take yakirata, amma yakira yakai sau hudu bata daga wayar ba, haka yasake kiran Daddy ya sanar masa, daga qarshe de sai Daddy ne yayi masa kwatancen gidan da kansa, shikuma yahau taxi suka tafi, daqyar ma me taxi din yagane abinda Aslam din yake nufi, saboda shi Babu turanci, shikuma Aslam Babu yaran hindi ????

Sunyi tafiya Mai nisa sannan yasauke Aslam ya nuna masa bus din dazai shiga, zata kaishi har kofar gida

Dole saida dala yayi amfani wajan sallamar me taxi din, sannan yafara jiran zuwan bus
Yanayin garin yake kalla da dan hadari kadan, Kamar wasa kuwa aka fara yayyafi, mutane dasukasan kan garinsu kowa sai yake baza lema, Aslam kuwa sai kare ruwa yake da hannu amma abin ba riba????

Ruwan yafara jiqa masa kayansa saiga bus din tazo ta tsaya awajan, gani yayi mutane suna shiga, shima yace ai ko ba ita bace wallahi shiga zaiyi, sukaishi koma ina ne ????

Duk kujerun motar ma sun cika, sai wata yarinya datake zaune gefenta akwai kujera daya, kallo daya yayi mata yagane cewa Babbar arniyace, shigar ta kadai zaka kalla kagane hakan

Riga da wando ne a jikinta kayan ya kamata sosai, sannan gashinta awaje sai Dan qaramin mayafi data dora akai Wanda dashi da Babu duk daya
Itama kallansa tayi, taganshi a tsaye yariqe karfen Mota, kayan jikinsa sunyi masa kyau sosai, da yaren India tace masa yazo yazauna, taga ko Kallanta ma baiyiba alamun baima san dashi takeba
Dan haka tace “hi”

Sai lokacin ya juyo

Tace “please come and sit”

Kallanta yasakeyi ya yatsina fuska, “no, thank you” yafada mata haka yana yatsina fuska
Hankalinta ta maida kan window bata qarabi ta kansa ba

Wayarsa yaciro yaciro daga Aljihun jeans d’insa yakira Abba, Abba yana dauka Aslam yafara zuba “Abokina kasan me? Wallahi gara da Allah yasa baka biyoni ba, gani nan muna tafe awata bus tana tafiya yanda kasan hawainiya, ni a tsaye ma nake narasa wajan zama”

Abba yace “Kamar ya?”

“to gashinan de kowa yana zaune, babu kujera sai guda daya, ita kuma wata qatuwar arniyace azaune nake fadama ????, inani ina zama kusa da manyan arna????
Shegiya harda cewa wai in zauna, d’an iska neni, ina zama zata liqemin daga nan kuma ta addabi rayuwata”

Murmushi Abba yayi, yasan halin Aslam sarai, “to kayi hakuri mana, insha Allah zakuje lafiya”

Wani uban birki aka taka, hakan yasa Aslam yayi gaba yasake dawowa baya, nan take yakashe wayar yasake riqe karfen ????

Mutum uku ne suka fita, kujerar datake gaban yarinyar Babu kowa, nan yakoma Yazauna, yarinyar tanata kallansa

Kafin su qarasa Inda zaije motar ta lalace, kowa yafuto, wasu suka fara tare Mota, wasu kuma suka tsaya, kiran sallah yaji anayi awani masallaci, Dan haka yaje wani dan case agefen su yasiyo ruwa, yadawo wajan motar ya tsugunna yafara daura alwala

Yarinyar tana tsaye a gefensa, duk tana kallansa, ajiyar zuciya tayi, tataka Ahankali ta qaraso wajansa cikin yaren hausa tace masa “bawan Allah Dan Allah idan kayi sauran ruwan inaso nima zanyi sallah, kudin hannuna baida yawa bazai isheniba”????

Shiruuu Aslam yayi Kamar an kwada masa sanda????????‍♀️
Kasa Dagowa yayi, bare yahada ido da ita ????

Tasake cemasa “dan Allah, kaji”

Sai a lokacin yadago kansa, cikin kuskurin kunya yace “yanzu ke, dama kinsan kina jin hausa kika barni inata zuba?”

Murmushi tayi batare datayi magana ba, Ruwan ya miqa mata yace “gashi inde ruwa ne, ai ruwa baya had’a fad’a, shi musulmi ai dan’uwan musulmi ne” ????

Hannunta ta meqo zata karbi gorar Ruwan idonsa yasauka akan wani abun hannunta irin Wanda yan gayu suke daurawa maza da mata, amma nata anrubuta mata MAZAWAJE da manyan harufa ????

Fasa bata Ruwan yayi, ya tsaya yakalli fuskarta dakyau, aishi sai yanzu nema yaga yarinyar tanayi masa kama da Nihla sosai, saide tafi Nihla cika dakuma ‘yar qiba, yayi ajiyar zuciya yace “ke fadamin, Yaya sunanki?”

Murmushi tayi tace “Aysha Basiru Abubakar Mazawaje” ????????‍♀️
Cikin ransa yace tabd’i, dara tasake cin gida kenan, yatsunsa biyar ya nuna mata yace “uwaki” ????

Yaci gaba da cewa “to a qasar nan qafata qafarki dake Zan koma Nigeria, Aslam ne Dan gidan Alhaji Baqir yayan babanki”

Cikin sauri tace “yaya Aslam, Innalillah…, ya akai nakasa ganeka?”

“aikokin ganeni, ko baki ganeniba, daga nan, babu Inda zan barki kije,wuce Muje muhau wata motar kikaini gidan”

“toka bari muyi sallah mana, bani Ruwan nayi alwala ni”

“da wannan shigar zakiyi sallah? Haba, haba, wannan kam baki isaba, ina wayarki ina kira baki dagaba?”

Jakar hannunta ta duba tace “kaganta acikin jaka, niban saniba”

Yace “yayi kyau, to wuce Muje gidan” ????

Daga nan tajuya sukayi bakin titi domin tare wata motar

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kallanta yayi idonsa akan manyan qirjinta yace “gaskiya naji dadin rawar nan, gashi gayu sunzo dayawa, club din yacika sosai, Ina alfahri dake Diyana kin iya rawa ba qarya”

Murmushi tayi tace “najjashi kenan, ai mutum ya mori yarintarsa, yayi amfani da lokacin sa kafin yaqure masa, nan gaba idan natara yara ai bazanyi ba”

Yace “wannan gaskiya, toga kazar taki, nasan kinason kaza shiyasa nasiyo miki ita, zakiji dadin ta”
Yafadi haka yana miqa mata ledar kaza

Hannu tasa ta karba tace “to najjashi nagode, kaga dare yayi, sha d’aya saura, Zan shiga gida”

Idanunsa ya lumshe sannan yabude su, ahankali yadora hannunsa akan qirjinta, kafin ta farga yafara murzawa,????????????‍♀️
Cikin kasalalliyar murya yace”to yanzu ya za’ai kenan? “

Da qarfi kuma cikin fishi ta bige hannunsa, bacin rai ya baiyana akan fuskarta qarara, ta kalleshi dakyau tace” najjashi bude min Mota nafita kafin na tsinka maka mari anan, anfada maka ni ‘yar’ iska ce? Saboda ina yawo club club bashi yake nuna jikina nake kaiwa ana amfani da niba, “

Runtse idonta tayi cikin tsananin bacin rai taci gaba da fadin ” najjashi nace kabudemin kofa kafin inbude idona “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button