DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Dariyar yaqe yayi, yayi tunanin zai samu abinda yakeso awajan ta, yayi tunanin itadin yar hannu ce,koda yaushe yanaso ya gwada sa’arsa akan Diyana ko zai dace, amma abin ya faskara,
cikin borin kunya yace ” dama fa gwadaki zanyi, ????
Kuma kinci Interview”
Cikin fishi tace “uwar Interview, nace kabudemin kofa,” ta qarasa maganar cikin tsawa, babu musu yabude mata kofa, tawullo masa ledar kazar tafice daga cikin motar
Adede lokacin Adam yadawo daga wajan meeting din dasukai a Makaranta, qare mata kallo yayi tana sanye da riga da wando, duk shape dinta yafuto, babu wani namiji Mai cikakkiyar lafiya dazai ganta ya qyaleta
Yakalli Agogon motar yaga shadaya saura, yana Kallanta tashige cikin gidan, sannan najjashi yaja motar sa yabar kofar gidan, shima Adam din yayi horn megadi yabude masa, cikin ransa yana fadin Allah ya shirya, yarinya kam tagama lalace wa saide addu’ah ????, Dan nasiha bazata karbuba adede wannan lokacin ????
Tana zuwa part dinsu taga Babu kowa afalon danhaka tashige cikin dakin su itada Dida, tana shiga ta gansu azaune dukansu, Ilham, Nihla, da Dida
Zama tayi akan gadon tana sakin tsaki, dukansu suka kalleta, Nihla tace “meyake faruwa ne Diyana?”
Cikin bacin rai tace “wallahi daga club nake, wani gaye ya ajiye ni abakin gate d’an iska jiyake nima irinsa ce shine yasa hannu yana tabamin nono”
Gaba dayansu suka hada baki suna fadin “Nono” ????
Kallansu tayi, “to miye abin hada baki anan? Ku daga anbaku labari zaku nemi ku ta rawa mutum jama’ah”
Nihla tace “tab, ai abinne da nauyi, kema Diyana kidena wannan yawon, wannan shigar dakike duk bai kamata ba”
Ilham ma tace “ato shikuwa gaye ina ruwansa yaga abubuwa asarari ai dole ya gwada ko zai dace” ????
Dida tace “gara de ku fada mata ko zataji,” sannan ta maida Kallanta ga yayar tata tace “gara ma wallahi, gaba kya sake fita” ????
Diyana de tayi shiru tana jinsu, amma tabbas yaukam najjashi ya nuna mata cewa ita yar’qaramar ‘yar club ce
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Aslam yasamu tarba sosai daga wajan abokin daddy, cikin kwana biyun dayayi a qasar ya fahimci halin Aysha, tanada nutsuwa sosai da sosai, bako Mai ne yake qara birgeshi da yarinyar ba sai Kallanta, duk lokacin data daga ido ta kalleshi sai yaji wani abu ya soki zuciyarsa
Haka nan ya tsinci kansa dajin dadin kasancewar su tare da yarinyar, kwata-kwata ya Manta da maganar Daddy dayace kada su dauki lokaci Mai tsawo basu dawoba
Yau kuwa Tun safe Daddy ya kirashi yace sukamo hanya su Taho gida, Dan haka washe gari sukai shiri suka Taho shida ita
Acikin jirgi ma tana gefensa, sau uku tana kamashi yana Kallanta
Tace “yaya Aslam lafiya kuwa?”
“akwai abinda yake damuna qanwata”
Kokarin saka belt take saboda sanarwar da ake cewa jirgi zai tashi
“meyake faruwa?, meyake damunka?”
Yace “kece, kece damuwata Aysha, narasa yanda zanyi da soyaiyar ki”
Sakin belt din Hannunta tayi ta rufe fuskarta cikeda kunya ????
Dab da ita ya matso yadauki belt din zai saka mata, tanajin sa akusa da ita, Kamar zai maida ta jikinsa
Harya saka mata belt din bata bude fuskarta ba
“kibude fuskar ki mana”
Cikin kunya tabude fuskar tata
Hannunsa yadora akan nata yariqe yace “Aysha kimin alqawari duk rintsi bazaki rabu da niba”
Wani iri takeji yanda yakama mata hannu, danta taqaita maganar tace masa “insha Allah yaya Aslam, nayima alqawari”
Ajiyar zuciya yasauke, sannan yasaki hannunta yana jin farin ciki naqara ratsashi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tsaye suke a Airport, Fawaz, Adam da Abba
Suna jiran jirginsu Aslam ya sauka, Fawaz yace “guy’s kunsan menene, ni arayuwata kwata kwata mata basa gabana wallahi, amma tunda nayi karo da’ita take nema ta addabi nan d’ina”
Yaqarasa maganar yana dora hannunsa asetin zuciyarsa
Da mamaki Abba da Adam suka kalleshi, Adam yace “Wacece?”
Ahankali yace “Nihla”
Dasauri Abba ya kalleshi, haka nan yaji haushin maganar Fawaz din, yayi shiru baice komai ba, Adam yace “Babu laifi tanada hankali, yarinyar akwai Face, duk family dinnan idan kana neman kyau kazo wajanta kagama Alhaji”
Fawaz yace”no ni bawai kyanta ne yajani ba, ina tunanin idan na aure ta bazata damu da halaiyataba, zata barni insha abinda raina yakeso “
Wannan karon Abba kasa hakuri yayi yadubi Fawaz din yace masa “Nihla?”
Hankali kwance Fawaz yace “yes”
Adam yace “nikam gaskiya idan Zabi za’a bani ko to Zan Zabi Dida, najima ina son yarinyar but narasa yanda Zan fuskanceta in fada mata, bazan iya zuwa wajanta da girmana ina qaramar murya akan tasoni ba, amma gaskiya sosai nake sonta, dama inka dauke Nihla da Dida da Aysha, tofa sauran biyun sai Ahankali, Ilham rashin kunya, Diyana kuwa Hmm karma kasata acikin lissafi, Dan rannan ma wani gaye nagani yasauketa amota “????
” dan Allah kundameni da maganar wannan yaran, ku yanzu ko kunya bakwaji kuzauna kuna cewa qannan bayan ku kukeso? Ahaifi yaran agabanku amma kudinga wannan maganar? “
Cewar Abba
Fawaz yadafa kafadarsa
” zamu ga yarinyar da zaka Aura Abba “
Suna wannan maganar su Aslam suka futo, shine yake riqe da jakar ayshan, Tana ganin Fawaz ta qarasa ta rungumeshi tace
” yaya Fawaz “
Cikin farin ciki yace ” Sannu da zuwa qanwata, “
Su Adam ta gaisar, gaba daya sun sauya mata, in akan hanya ta gansu ba lalle taganesu ba, shima Fawaz din dan kullum suna gaisawa dasu ne ta cht
Hannun ta yaja yabude mata Mota ta shiga, Adam ma yashiga, shikuma Aslam zasu tafi shida Abba
Ta glass din motar ya leqo kansa yace “my dear shikkenan sai munyi waya ko?”
Kunya ta kama Aysha, shi yaya Aslam ko kunyar qaninsa Adam dayake wajan bayayi zai yi mata wannan maganar?
Ahankali ta daga kanta, Fawaz ya kalli Adam suka hada ido ????
Basu cemusu komai ba, sukaja motar suka tafi
Shima Aslam ya shige ta Abba suka tafi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan dawowar Aysha da kwana biyu Aslam yazo part din su Abba, suna zaune agefen gado da takardu agabansu suna tsara yanda zasu gina wani sabon kamfanin dasuke son budewa tare
Suna gama tattaunawa Aslam ya ajiye file din a gefensa yakalli Abba “Abokina gaskiya inason yarinyar nan, Aysha tagama tafiya da nutsuwa ta, zan jira agama wannan meeting din da Daddy yace za’ayi bayan angama Zan sanar dasu kawai ayi mana aure, inyaso saita dawo nan taci gaba da karatun ta tunda yanzu tafara”
Kallansa Abba yayi “Aslam kuna bani mamaki yanda kuka dage akan wannan qananun yaran”
“Abba karka renamin hankali, haka kakeso muyi ta zama ne? Ko kana tunanin muna germany bana sane da irin juyin dakake cikin dare kakasa bacci?” ????
“Malam ni bana wani juyi cikin dare”cewar Abba
“qarya kake Abba, to lemon tsamin danake gani cikin dozbin fa?ni bazan kashe kaina ba, aure nakeso kawai”
“to karka min kuka” inji Abba
Adede lokacin taturo kofar dakin tashigo, bakinta dauke da sallama, tana riqeda flet me dauke da meat pie
Kallansa tayi “ya Abba ga meat pie nayima,”
Agajarce yace mata “Ok”
Ta kalli Aslam tace “Barka da wannan lokaci ya Aslam”
Cikin sakin fuska yace”yawwa Nihla, mungode sosai “
Murmushi tayi tajuya tafice daga dakin
Aslam na ganin fitarta ya kalli Abba “Abokina yarinyar nanfa nagama lura tana sonka, irin yanda take kula dakai zaisa kowa yagane hakan”
Kallan Aslam yayi “wacce irin magana kake haka Aslam? Yaushe Nihla ta girma dahar zatasan wani soyaiya? She’s 17 year’s fa”