DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

“to menene aciki?”

Hannu yadaga masa “no, no, dakata Aslam, kafi kowa sanin nafisan na Auri mace babba, wadda ta waye, me ilmi, ta mallaki duk abinda nakeso ajikin mace, sannan me hankali, amma Nihla renonta kawai zanyi, Aslam nasan kaina inada tsananin sha’awa, kuma ni kadai nasan yanda nakeji, wannan yarinyar zan’iya kakkaryata Tun a daren farko idan ma ta nuna kenan, bare ma yanzu dabata nunaba “

” dan Allah ka dakata Abba, wannan yarinyar fa qanwar ka ce, menene aciki idan ka aure ta? Meka dauki mace Abba? Kana maganar nuna ai kaine zaka maida ta hakan “

” dan Allah kadena min wannan maganar Aslam, nafadama bazan iyaba, nafisan mace me tarin ilmi, wadda tahada komai, amma Nihla amatsayin qanwata nake ganinta “

Aslam yace” nasan dalilin dayasa kake wannan maganar, kuma kasan hakan ba qaramin kuskure bane idan ka aikata shi, ba kuma ranka ne kadai zai baci ba harda namu baki daya, inaso ka tuna halin da Diddi ta shiga itada baba Basiru akan hakan “

Yana fadar haka yayi wulli da file din dasukai magana akansa yafice daga dakin cikin fishi

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“wayyo Allah ummah cikina ciwo, zan mutu ummah, ummah Dan Allah kiyafemin, kicewa Abbanmu shima yayafemin”

Hajiya abida tashare hawayen idonta “Aysha kidena maganar mutuwa, ba zaki mutu ba, ‘yata bazaki tafi kibarni ba”

Ilham idanunta sunyi jajir tace “Anty Aysha kiyi shiru Dan Allah, bazaki mutuba, zaki tashi mu rayu tare”

Hannun Ilham ta riqe tace”ilham kicewa yaya Aslam ina sonsa, bazan tashi ba Ilham ni nasan yanda nakeji, nadade ina wannan ciwon cikin, amma nayau dabanne ilham “

Alhaji Basiru ne yasa hannu da kansa yadauketa suka futo daga cikin motar suka shiga cikin asibitin dasuka qaraso

Likitoci ne suka karbi aysha, nan take suka shiga bata temakon gaggawa, Alhaji Basiru Yazauna awajan yayi tagumi

Daga baya yan gidan gaba dayansu suka qaraso asbitin, Aslam yafi kowa shiga tashin hankali, Daddy ya kalli Alhaji Basiru yace “wai dama batada lafiya ne?”

“wallahi yaya Abubakar kwana mukai bamuyi bacci ba, cikin ta yana ciwo, bayan wani dan lokaci saiya lafa, shine muka Taho Asbiti yanzu”

Alhaji Baqir yace “subhanallah, Allah yabata lafiya”

Gaba dayansu sukace amin, haka suka zauna jugum jugum, babu wanda yankewa dan’uwansa magana, har likitocin suka futo

Gaba dayansu sukai kansu da tambaya, Likitan ya goge gumin fuskarsa yace “Alhaji saide kuyi hakuri, Allah yayi mata cikawa, munyi iya kokarin mu ganin mun ceto Rayuwar ta, amma hakan ya gagara sakamakon ciwon Hanta datake dauke dashi, hantarta tariga ta lalace, kuyi hakuri”

Ilham najin haka ta yanke jiki tafadi, yaran kuwa kowa kuka yake, Aslam ya sulale Yazauna aqasa yana maimaita kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju’un acikin ransa

Gaba daya waje ya kaure da koke koke, babu me lallashin wani, haka suka dauki gawar Aysha suka tafi gida, akai mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Aslam kuka Kamar mace, duk yafita a hayyacinsa, saide muce Allah yaji qanta, idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda akai wannan mutuwa gidan yadawo shiru, Diyana kuwa kullum tana cikin hijabi????
tunda taga aysha qiri-qiri tamutu da quruciyarta, sosai mutuwar tataba matasan gidan, saboda basu taba kawowa kowa mutuwa acikinsu ba
Ranar ukunta yayi daidai da ranar da Daddy ya sanar za’ai meeting, amma ganin anyi musu rashi yasa aka sanarwa kowa sai bayan sati biyu akwai gagarumin family meeting.
Hakan ce kuwa ta kasance,ranarda sati biyu tacika kowa yatafi Babban dakin taro nacikin gidan mata da maza manya da yara, Usman shida matar sa da yaransa biyu, sai Aliyu shima yazo da matar sa da dansa daya namiji, farouq kuwa matar sa ko haihuwa batayi ba
kowa yazo yanaso yaji abinda wannan wasiyya ta qunsa
Samarin ne awaje kawai basu shiga ciki ba suna jira saisu Daddy sun qaraso

Sunata fira kadan kadan amma Aslam baya magana, Adam kuwa gabansa ne yake ta faduwa harya kasa boyewa yace “nifa gaskiya meeting dinnan danya zama dole ne amma gaskiya da bazan zoba, yau inada lacture, sannan gabana faduwa yake narasa dalili”

Fawaz kallansa yayi bai tankaba, Abba ma shiru yayi, Aslam kuwa daja tunda aysha tarasu suka kasa gane kansa

Kallansu yayi yace”wai badaku nake bane duk kunmin shiru?” ????

Ajiyar zuciya Fawaz yasauke yace” kai sai yanzu kakeji,? ni Tun jiya gabana yake faduwa, Kamar akwai abinda yake san faruwa Dani, amma koma menene Allah yasa ya sameni ni kadai banda Nihla “????
Kallansa Aslam yayi cikin mamaki, to kode Fawaz nason Nihla ne? ????

Kafin wani yace wani abu su Daddy suka qaraso wajan, shida Alhaji Baqir da Alhaji Basiru
Dakin taron suka shiga, sannan suma samarin suka bisu abaya

Wajan meeting din yayi kyau an qawata shi da lemuka da ruwa domin baqi ????

Nihla tana kusada Momy, yayinda Ilham ma take gaban ummanta hajiya abida, suma su Dida itada Diyana suna gaban maman su hajiya Farida

Su daddy suna zama hall din yayi shiru, Kamar ruwa ya cinyesu, megadin gidanne yaqaraso dauke da akwatin da aka rufe takardar wasiyya aciki ya ajiye yajuya yafita ????

Daddy dakansa yatashi yabude, kowa yazuba masa na mujiya, yadauko takardar Yazauna sannan ya’ajiyeta agabansa

Yakai dubansa wajan samarin sun zauna waje daya gaba dayansu, Adam ya kalla yace “Adam taso kabude mana taro da Addu’ah”

Babu musu yatashi yadinga kwararo musu addu’ah, sannan aka shafa

Daddy yayi gyaran murya, yafara magana “Alhamdulillah, muna qara yiwa Allah godia akan Tsawon rai dayayi mana har muka kawo wannan lokaci cikin kwanciyar hankali, wadanda suka rasu acikin wannan family Aisha, da takwararta Aysha, muna yi musu addu’ah Allah yaji qan su”
Gaba daya aka amsa masa da “Amin”
Sannan yaci gaba da fadin
“insha Allah yanzu zamuji dalilin daya taramu anan wajan “

hall yaqara yin tsit, Daddy yabude takardar yayi tozali da rubutun Ajami, yadaga kansa yasake duban Adam yace”da Ajami sukayi rubutun, Adam kaine malami zoka karanta mana”

Hajiya na’ila tafara karkad’a kafarta tana hura hanci , jin ansake kiran dannata akaro na biyu

Jikin Adam a sanyaye yaje gaban iyayen nasa ya karbi takardar yafara karanta wa :Assalamu alaikum jama’ar wannan dangi Mai albarka, ni Abubakar Mazawaje mun zauna tareda matana guda biyu mun rubuta wannan wasiyya badan komai ba saidon hadin kan wannan zuri’a,mun yanke shawarar hada jikokinmu aure domin zumunci yaqara qullu wa,…

Adam yana zuwa nan yaji gabansa yafadi, jikinsa yafara rawa, hannunsa sai karkarwa yake yaji maganar akansu ne Wato jikoki

Cikin daure fuska Alhaji Baqir ya kalleshi “kai menene haka? Cigaba mana”

Muryar Adam na rawa Kamar ba namiji ba yaci gaba da karatun

“Duk mazan da suke cikin wannan family an mallaka wa kowa filin dazai gina,duk Wanda yayi aure acikin wadannan yara dazamu ambata, to lalle lalle ya tabbatar yasake wani auren yacika namu Burin

munyanke shawara tareda umarnin cewa Ilham ‘yar gidan Basiru zata auri Aslam Dan Alhaji Baqir

Dida yar gidan Farida zata auri Fawaz yaron Alhaji Basiru

sannan Adam yaron Alhaji Baqir zai auri Diyana, yarinyar hajiya Farida

saikuma na qarshe takwarana Abubakar Wato Abba, zai auri Aisha yar gidan Alhaji Basiru tareda Nihla yarinyar Aisha “

Wannan dalilin ne yasa mukayi muku hani akan duk wani taro acikin family, na suna kona aure, saboda gagarumin taron dazaku hada na auren jikokinmu, muna yiwa kowa fatan alkhaairi “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button