DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Kallansa Abba yayi jin irin furucin dayayi, yarasa meyasa duk suka damu kansu akan Nihla, shima yanaso yaga ya faranta ransu ta hanyar amince wa to amma Nadiya fa?
Aliyu yace “farouq bazaka aure taba, shidin shine dai zai auri yarinyar, da yanaso da bayaso”
Momy ta kallesu tace “ya’isa haka,”
Taci gaba da cewa “Abba idan na isa dakai, amatsayina na mahaifiyar ka to inama umarni akan ka auri Nihla, nide amatsayina na wadda tayi renon cikin ka Nihla tafi kwanta min a raina, idan kuma nima zaka nunamin ban’isa dakai bane shikkenan katafi kabar Mazawaje family din Kamar yanda mahaifin ka yace, su Usman ma sun isheni “
Dasauri tafice daga cikin dakin saboda wani sabon kuka daya Taho mata
Farouq ya kalleshi yace ” danma kasamu yarinyar tana sonka, duk tarasa wazata so acikin mu saikai, kaje kayi tayi, kada Allah yasa ka amince, bazata rasa masoya ba”
Yatashi yafice daga dakin, su Aliyu suka mara masa baya suka Barshi shi kadai a dakin
Ahankali Yazauna yadafe kansa ????????♂️
Meyasa kowa yakasa fahimtar sane?
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Daddy tunda yadawo daga wajan taro Yazauna afalon nasa yayi shiru yana tunani, yanda Aisha tatafi tabarshi ai dole ya kyautatawa yarta, yanajin Nihla aransa sosai, duk lokacin daya bude ido yaganta yanajin dadi, bayasan abinda zai rabashi da yarinyar kokadan,
Su Usman suna zaune afalon suma, ya kallesu fuskarsa Kamar Babu damuwa yace “kume kuke jira anan ne? Tunda angama ai yakamata kutafi gida ko?”
Babu musu suka tashi, amma farouq kansa har ciwo yake saboda yanda yayi kuka
Momy ce tafuto tafon taga Daddy azaune shi kadai, tazauna kusa dashi tace “Sannu da zuwa Alhaji”
“yawwa Rahma sannu, ina wannan yarinyar take?”
“tana daki, zazzabi ne yadan rufeta, amma na bata magani tasha, nabarta tahuta”
Jinjina kansa yayi batare dayace komai ba, itace tasake kallansa tace “Alhaji nasamu Abba munyi magana dashi, ya amince da auren, yana cikin dakinsa baitafi ko’inaba, kayi hakuri akan abinda yafaru”
Ajiyar zuciya yayi “ai nayi tunanin yatafi wajan wadda yakeso din, da saide yanemi wani uban, amma baniba”
Itama Jinjina kanta tayi, tace “yana ciki, kayi hakuri Allah yahuci zuciyarka”
Batare dayace mata komaiba yatashi yayi cikin dakinsa
Awannan rana haka Nihla tawuni adaki ko falon bata futoba, gaba daya family din Babu mejin dadi aransa
Acikin yammatan ma Babu wadda taje wajan kowa, ko wacce tana part dinsu tanaji da abinda yadameta
Bayan sati biyu tana zaune a dakinta, yammatan suka zo wajan ta, kullum tana zaune adaki, abincima saide Momy takawo mata, kunyar ma hada ido take da Abba saboda yanda take shishishige masa amma yayi watsi da’ita
Ilham ta kalleta tace “Nihla har yanzu kinqi sakin ranki, yakamata ki Manta da abinda yafaru fa, duk kin rame”
Dida tace “wallahi kuwa, ni bazan d’orawa kaina ba, muma nan dukanmu hakuri mukayi, dama yaya Adam naso, kuma yanzu anbawa Diyana shi”
Tsaki Diyana tayi tace “ni wallahi Dida kina qara ba tamin raina idan kina hadani da wannan mutumin, arasa Wanda za’a bani sai malami, ni kunyar fita ma nake wallahi, adinga nunaka ana ga matar Malam” ????????♀️
Ilham tace “nide bansan yaya Zan zauna da yaya Aslam ba, agabana Anty aysha take wayar soyaiya dashi amma wai ace shi Zan aura, haba aida kunya, amma Zan bashi girman sa yanda yakamata, renin hankali ne bazan daukaba, idan ya min wallahi ramawa zanyi, Dan dagashi har Hajiya Na’ila bazan dauki renin wayonsu ba “
Ta kalli Dida tace” kekuma Dida wannan shiru shirun naki wallahi saikin Barshi, bar ganin yaya Fawaz yaya nane wallahi idan yamiki kicire kunya kirama “
Ahankali tace” inani ina shi Ilham, bazan iya bama, kowa yayi sabgar gabansa “
Diyana ta kalli Nihla tace” ke ya batun yaya Abba kuwa?”
Tace” bansani ba Diyana, Tun lokacin da abin yafaru ban qara haduwa dashiba, banyi tunanin zaimin hakaba, abin takaicin ma shine yanda nakasa cireshi a raina, har yanzu ina nan ina jinsa acikin raina, abinda yake bani tsoro Diyana shine idan na kwanta bacci kullum sainayi mafarkin sa, dana kwanta dashi a raina daban kwanta dashi a raina ba “
Gaba dayansu sun tausaya mata, Dida tace” kiyi hakuri Nihla, lokaci ne “
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tsaye suke a compound din gidan shida Abba, Aslam ya dubeshi yace “Abba biki yanata matsowa bamu gayyaci kowaba”
“nifa Aslam mantawa nake da wannan auren, babu wanda Zan gayyata, tunda sundage saina aure ta, ayi bikin kawai, naji haushin wasiyyar nan, akan wannan qullin nasu suka hana wannan family yin taron komai, wai saboda sun tanadar mana Babban taro agaba, mutsw “
ya qarasa maganar dajan tsaki
Aslam yace” to aikai Dasauqi Abba tunda Nihla zaka aura, amma nifa, qanwar budurwa ta fa, gata da rashin kunya yarinyar “
” idan tayi maka rashin kunya ka zaneta kawai ka wullota waje karufe gidanka “????
Cewar Abba
Ajiyar zuciya Aslam yayi” Abba duk cikin mu kaida Fawaz ne kukai sa’ah, Nihla tana sonka sosai “
” So, so, so, maganar kenan dai, Aslam narasa gane meyasa qananun yara suke daukar kulawa amatsayin soyaiya, kaga mubar wannan maganar dai, na turawa wajan aikina takarda inaso su yimin transfer nadawo gida “
” hakanma yayi Abba, kaga zamufi samun damar kammala abubuwan damuke buqata na company “
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
“my son, kacika rigima dayawa, idan kazo gidan me zakayi? Mami d’inka tana nan lafiya, saini nikuma kana ganina idan nazo”
Shiru yayi yana sauraron yaron nasa, saida yagama jin abinda yace sannan yace “to shikkenan naji, idan kazo ma bazan barka ka kadede ba zaka koma, Allah yakaimu next week din, Yaya batun kayaiyakin da nace katuro? Katuro kuwa?”
Cikin muryarsa Mai cikeda Aji yace “anturo su, zuwa jibi zasu qaraso”
“Ok to, to, ba laifi, zan fadawa mami dinnaka zuwan ka”
daga haka suka yanke wayar, yana juyowa bayansa yaga Ibrahim Mai hakuri, nan take ya fadada fara’arsa yace “a a mai hakuri, kace kana tafe”
Baba yace “ina nan wallahi Alhaji, ai nazo na tarar kana waya, shine nace bari naqyaleka kagama tukunna”
Cikin murmushi yace “eh wallahi ina waya da yusif ne Dan wajena, yadage yanaso nabarshi yazo gida yaga maminsa”
Baba yayi Murmushi yace “to Alhaji abarshi mana, aiya dade yayi kokari ma, daga karatu anzarce harkar canji ai yaro yayi hankali saide muce Allah yaraya mana”
Yace “hakane kam, Mai hakuri abinda yasa nakiraka shine dama nayanke shawara zamu koma Abuja da zama nida Mai dakina, saboda harkokin nawa sunfi yawa Acan, shine nakeso kaima ka shirya akwai wani aiki na canji danake so na doraka akai, idan Babu damuwa inason mutafi gaba dayanmu harkai, mu koma can gaba daya “
Cikin tsananin murna baba yafara yiwa alhaji isma’eeil godia, Alhaji yace” Babu damuwa, sai ka fara shiri, wani satin idan Yarona yadawo, zamu wuce insha Allah “
Cikin tsananin murna baba yace zai shirya, haka suka rabu da maqocinnasa cikin farin ciki
Yana shiga gida yafara hada kayaiyakin gidan yanata farin-ciki, wayarsa ce tayi qara, yana dubawa yaga hajiya Farida ce mutuniyar tasa, cikin farin ciki yadaga wayar “Barka da wannan lokaci hajiya Farida”
Itama anata bangaren “tace yawwa Mai hakuri, mu munata shirye shirye, amma banga yan yalleman sunzo ba”
“shirin me kuke hajiya?”
Tace “Ah Mai hakuri karka cemin bakasan ansawa yaranmu ranar aure ba? Kuma danaga harda Nihla shiyasa nace bari nakiraka naji yaushe zakuzo”????