DANGI DAYA HAUSA NOVEL
Hannunta ta miqa masa tace “bani takardar Abubakar”
Takardar yasaka mata cikin hannun ta, yana Kallanta ta bude wata qaramar akwati agefenta tasaka takardar aciki, sannan tasaka key tarufe akwatin, tamaida Kallanta gareshi tace “Wannan takardar zataci gaba da zama acikin wannan akwatin har Tsawon shekara goma”
Cikin sauri yad’ago kansa yadubeta “Hajiya shekara gomafa ba wata goma bane, mu kanmu bamuda tabbacin zamu iya kaiwa wannan shekarun dakika ambata”
“Abubakar kenan, kullum addu’armu itace Allah yaraya mana ku, nasan zaka iya amatsayin ka na babba Mai fada aji acikin yan’uwansa shiyasa nabaka wannan takardar, kuma har gobe ina fatan gaba d’ayanku kukai wannan lokacin”
Cikin sanyin jiki yace “to Hajiya Allah yasa”
Tace “Amin Abubakar, Allah yayi maka albarka, mukullin dazai bude muku wannan akwatin zaku iya samunsa awajan Alhaji mamuda, Wato aminin mahaifin ku idan shima lokaci bai cikaba, sannan abu na qarshe dazanyima kashedi akansa shine daga rana irinta yau kada asake taro kowanne irine acikin MAZAWAJE FAMILY, idan anyi haihuwa asakawa yaron suna kawai, maganar taro na biki shima daga kan masu shekaru irinna FAROUQ zuwa qasa kada abari kowa yayi, idan so Samu nema kubarsu su girma kowa ya mallaki hankalin kansa tukunna kafin ku aurar dasu”
Wannan karon kam gumi ne yajiqe masa fuska, wannan wanne irin sharad’i ne? ????
Kallanta yayi” Amma hajiya… “
Cikin sauri ta d’aga masa hannu” dakata Abubakar, wannan umarni nane, banaso kace komai akan haka, Yaya maganar takardar filaye na yara?”
Daqyar yace” Hajiya angama yankawa kowa nasa, dukkan yaran maza kowa angama sama masa nasa filin, takardun ma sunzama ready”
“to idan kowa acikinsu ya tasa, kad’auka da kanka kabawa kowa nasa, Wanda ya wulakanta nasa shiya jiyo, idan mutum yanason zama acikin gida na family shikkenan, idan baya buqata saiya gina filinsa”
Cikin ladabi yace “to hajiya, insha Allah zanyi kokari inga nacika umarninki, nizan wuce gida su Rahma suna jirana itada yara zasu tafi jigawa suyi kwana biyu”
“meyasa kai ba zakaje ba Abubakar?”
Shiru yayi, bai tanka mataba, Dan haka tayi Murmushinsu na tsofaffi tace “Ayi hakuri haka Abubakar, abinda yafaru yariga yafaru, Aisha qanwar ka ce dakuka futo ciki d’aya, bayan ‘ya’yana bakada Wanda yafita duk duniya,kaida Aisha duka DANGI ‘DAYA kuka futo,sannan ba ita kad’aice Mai irin wannan laifin ba, kamanta da abinda yafaru abaya kajiko?”
Yace “to hajiya insha Allah, mungode sosai da sosai da irin ruqon dakika mana, Allah yaqara girma”
Cikin rashin damuwa tace”Amin Abubakar, Allah yayi maka albarka, ya albarkaci mazawaje family “
Yace” Amin hajiya”daga nan yatashi yafita
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda yadawo gida yarasa meyake masa dadi, idan yatunada maganar dasukai shida hajiya duk sai yaji wani iri, wannan ba qaramar magana bace, amatsayin sa na babba acikin family dole abin zai dame shi, to yanzu ita hajiya data d’ora masa wannan nauyin tana da tabbacin zata rigashi mutuwa ne? Idan kuma shi yarigata mutuwa fa? Wannan ba maganar ‘boye-‘boye bace, dole zai kira yan’uwansa gaba dayansu yafad’a musu komai, saisu sake tattaunawa akan batun, duk Wanda Allah yayi masa Tsawon rai acikinsu haryakai lokacin da hajiya ta ambata, saiya zartar da hukuncin, bazai iyu yabarshi aransa shi kad’aiba, zai hada meeting akan hakan dole
“Alhaji tunanin mekake haka tun d’azu nashigo inata sallama bakajini ba?”
Ajiyar zuciya yasauke yakai dubansa zuwa ga matar da tashigo cikin d’akin nasa, kallo d’aya zaka mata ka hango hutu da jin dadi atare da ita, yace”Rahma banji shigowar ki bane, ina yaran suke? Kun gama shiryawa ne?”
Shiru tayi masa tanemi waje ta zauna a gefensa sannan takama hannayensa tace”Alhaji meyake faruwa? Yanayin ka ya sauya bayan qalau kafita, kafadamin meyake damunka?”
Kallanta yayi “wallahi Rahma hajiya ce tadauramin wani Babban nauyi akaina,tabani wasiyya ne, sannan maganganun nata duk sun sanyaya min jiki, tanamin magana Kamar bazata qara kwana d’aya aduniya ba”
Cikin mamaki tace “wasiyya kuma?”
Yace “qwarai kuwa” nan take ya labarta mata abinda yafaru tsakaninsa da hajiya
Ajiyar zuciya tasaki tace “Alhaji, tunda kaga tanemeka kunyi wannan maganar da’ita haqiqa ta yarda dakai ne,tunda duk cikin yaranta bata nemi d’aya daga cikin su ba saikai, kayi kokari kaga kacika umarnin datama, amma gaskiya kasamesu kuyi maganar shi ne yafi, dukda nasan ma wasiyyar bazata wuce maganar hadin kanku ba “
” nima abinda nake tunani kenan Rahma, saide kuma idan hakanne me yakawo maganar taro da za’ace bandashi? “
” ka kwantar da hankalin ka Alhaji, insha Allah Babu abinda zai biyo baya sai alkhaairi “
” to Allah yasa, kwana nawa zakuyi idan kunje? “
” Kamar dai yanda mukai maganar dakai Alhaji, kwana biyu zamuyi insha Allah “
” to saikun dawo, Allah yakiyaye hanya, ki kulamin da yarana “
Murmushi tayi” Alhaji kenan, kanaji da wannan samarin naka, ni kuwa suna sakani ciwon kai, shikkenan za’a kula dasu “
Yace” to asauka lafiya “
Tashi tayi zatabar d’akin, harta fara tafiya Tajuyo tace masa”Alhaji banji kace na gaida Aisha ba “
” fad’ar gaisuwa ta a gareta ai batada amfani Rahma, tunda nina shirya muku tafiyar ai yakamata kisan cewa inaso ki ganomin ita ne”
Murmushi tayi tareda girgiza kanta, cikin ranta tace “Alhaji kenan” ????
Amma afili sai tace masa “to shikkenan zanfad’a mata yayanta yana gaishe ta kuma yana cikin kewarta akoda yaushe”
“kudin hannun ku zai isheku ko?”
shine abinda ya tambayeta a memakon yabata amsa akan maganar datayi masa, sai itama ta basar, tace “zasu isa, mungode,”
Tafuto daga d’akin batare data sake cemasa uffan ba, kai tsaye compound ta nufa, driver na ganinta yataho Dasauri ya karbi handbag d’inta, sannan yabude mata gaban motar ta shiga
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda tataho daga makaranta take kalle-kalle tana waige ko yauma zataganshi and’aukoshi daga makaranta Kamar kullum, saide ko alamun tayar motarsu bata ganiba, afili tace “inajin yauma yarigani dawowa , ko meyasa baya jirana?”
Takardar daya wullo mata d’azu dasafe tatuna tasaki dariya tasake cewa “kome ya rubuta oho masa, DANA SANI na nunawa Diddi”
Tana tafe tana waige har Allah yakawota gida, Tun daga bakin kofar gidan ta d’aga murya tace “Diddi nadawo ” sannan ta qarasa shigowa cikin gidan, turus tayi ta tsaya waje d’aya ganin baqin fuska agidan nasu, maza ne harsu hud’u reras, guda uku suna tsaye suna buga ball atsakaninsu, gaba d’aya wandone ajikinsu three quater, sai guda d’ayan dayake zaune kusa Diddinta ko d’ago kansa baiyiba bare ya kalleta
d’aya daga cikin masu buga ball d’inne ya kalleta dakyau yace “fine girl”
‘Dago kai Diddi tayi ta kalleta tace “Alhamdulillah kinga ‘yar halak, Nihla zonan,”
Kallan uniform d’in jikinta tayi sosai, tasan fad’an Diddi baya wuce anbata kayan makaranta, Dan haka tace “Diddi ki kalli kayana Allah yau ban batasu ba”
Diddi ta kalli matar datake kusata ita wadda taketa zubawa Nihla murmushi tace”Anty Rahma kinji ‘yartaki harta fad’i d’aya daga cikin halin ta ko? “
Matar da aka kira da Anty Rahma tayi daria tace” Nihla zonan, ina kika tsaya baki dawo gidaba har biyu tawuce?”
Qarasowa cikin rumfar tasu tayi, jin Diddi takirata da anty Rahma yasa itama tace ” Anty ina wuni “