DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Tana kwance akan kujera tana kallo har bacci yayi awon gaba da’ita
Angon nata kuwa yana can awajan Abba Yaqi yataho gidan, daqyar yataho gida ganin karfe daya tana neman yi, harda ledar kaza a hannunsa ????
Yana shigowa falon yaji qaran tv, falon yakalla tsarin komai yayi masa yanda yadace
Can yahangota tana bacci akan kujera, ‘yan qananun kitson da aka mata yayi mata kyau kuma yafuto mata da goshinta, sai fuskarta tayi fayau
Ahankali yataka yaje kanta ya tsaya, kayan baccin dake jikinta ya kallah kana iya hango yanda qirjinta yake azahiri, haushi ya kamashi, ya za’ai wannan yarinyar tasaka wannan kayan tazauna haka tsabar rashin kunya amatsayin sa na saurayin yayarta ????????♀️
Saida yasami dede cinyarta sannan ya d’aka mata duka, cikin firgita tatashi tace “subhanallah,”
Tabude idonta sosai taganshi a tsaye akanta, cikin bacin rai tace “ya Aslam lafiya zakamin irin wannan dukan Kamar agidan kurame? Kira daya idan kamin ai Zan tashi”
“Ok ke saboda tsabar rashin kunya nizaki koyawa yanda Zan tasheki daga bacci?”
Tayi shiru tana jinsa, sosai taji zafin dukan, ledar hannunsa ta kaza ya wullo mata jikinta yace “gashinan kici, idan kuma ba zakici ba shikkenan kinyi wa kanki”
Hararar ledar daya wullo mata tayi, tawurgar da ita awajan tayi cikin dakinta tabarshi awajan a tsaye
Shikuwa da kallo yabita yace “Dani kike zancen”
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
“mami bade kinfara bacci ba”
“wallahi nafara bacci Yusif, ina ka tsaya ne baka dawoba?”
“mami naje wani waje ne, ga Ice-cream nataho muku dashi ko zakusha”
Dukda tana bacci hakan bai hanata murmushi ba, wai ga ice-cream yakawo musu, ita da girman ta ina ita ina wani ice-cream, kawai de yace ga ice-cream na kawowa Nihla ????
Kokarin tashi take tace “nikam na qoshi Yusif saide Nihla, bari nakai mata”
Cikin sauri ya Dakatar da ita yace “a a a a, mami aikin fara bacci, kiyi baccinki bari nakai mata”
Tace masa “to saida safe”
Daga dakin yafuto kai tsaye yayi dakin da aka bawa Nihla, abin mamaki a zaune ya taddata tana kallan saman dakin tana hawaye, tana tausayawa Rayuwar ta sosai
Kallanta yayi ya girgiza kansa, sannan yaqaraso cikin dakin
Cikin sauri ta goge hawayen fuskarta tace “Sannu da zuwa yaya Yusif”
Yaji dadin yanda takira sunansa Tsawon shekaru
Zama yayi agefenta kan bedside drower, yakalli abinci agefenta alamun bataci komai ba
Fuska Babu alamun wasa yace “sauko kici abinci”
Babu musu ta sauko, tazauna aqasa, shikuwa be motsa daga Inda yakeba yazuba mata ido yana Kallanta
Abincin ta dauka tafaraci amma wani irin daci takeji acikin ranta, daqyar take tura abincin, idonta yayi rau-rau Kamar zatayi kuka, kafin kace me tuni hawaye sun zubo mata, saikuma tasaki kuka sosai, daga qarshe ma saita saka kanta akan gwiwar ta taci gaba da kuka
Ajiyar zuciya yasauke yadawo kusa da ita Yazauna har tana iya juyo hucin numfashinsa akusa da ita
Haushi ya kamashi, yace “kuka kike akan mijin naki ne?”
Cikin sauri tadago kanta ta kalleshi, sai ganinsa tayi dab da ita Kamar zai sakata cikin jikinsa, nan take yayi mata kwarjini, ta girgiza masa kai tace “a a Anty”
Ajiyar zuciya yasauke, yace “to kici Abincin Karki zauna da yunwa”
Abincin tafara ci amma hannunta sai karkarwa yake, gashi Yazauna dab da ita, duk atakure take tarasa yaya zatayi
Shikuwa ganin haka yasa yakai hannunsa kan nata hannun yariqe, sannan yadauki spoon din da daya hannun yafara bata abaki, babu musu take karba tanaci, cikin zuciyar ta fal tunani, kulawar da dan’uwanta ya Abba yakamata yabata, bebataba amma gashi wani bare yanayi mata
Saida ya tabbatar taqoshi sannan yabata ledar ice cream din daya shigo da ita yace “ga wannan, idan bazaki iyasha yanzu ba, ga fridge nan kisaka gobe sai kisha”
Daga masa kai tayi, yatashi tsaye yace “saida safe”
Daga nan yafice Yarufe mata dakin
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tun tana jiran zuwan Ango harta daina tahaqura, girman gidan yasa takejin tsoro sosai, gashi bakajin qaran komai, shiru garin, haka tatakure waje daya afalo cikin kujera har bacci yadauketa
Shikuwa fauwaz yanacan mashaya, da temakon Allah da temakon wani abokinsa da sukasha tare yadawo gida, dirin motar da taji ne yasa tatashi afirgice, Agogon falon ta kalla karfe biyu da rabi, tashi tayi tsaye cikeda tsoro
Yana tangadi irinna yan maye yashigo cikin falon, gabanta yafadi, tunda take bata taba ganin mutum murararan cikin maye hakaba sai yau, gadan-gadan yataho wajanta tana ja da baya, har yazo gab da ita, cikin muryar maye yace “keeeee..uban waye yakawo ki nan eh?”
Girgiza masa kai tafara tace “yaya Fawaz Dan Allah kayi hakuri”
Idanunsa yake son budewa sosai amma yakasa, yayi tangal-tangal zai fadi qasa tayi sauri tariqeshi aikuwa saiya dawo kanta gaba dayansa, dagashi har ita sukai baya suka fada kan kujera, shine akanta ita kuma tana qasa, tureshi tafara kokarin yi amma yamata nauyi sosai, shikuwa jinshi Akwance yasa nan take yafara bacci, kansa ta kalla taga yadora shi akan qirjinta, nan tafara ture masa kansa, amma saiyayi juyi ma yaci gaba da baccin sa
Haka ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, wai ita Dida itace qato Akwance akanta, wannan Baqin ciki da yawa yake ????
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da asubar fari yafarka daga baccin da yake, amma Idanunsa a lumshe bai budesuba, qamshin turaren dayake shaqa Mai dadi ne yasa cikin sauri yabude idonsa, da fuskarta yafara tozali, mamaki ya kamashi, laushin dayaji akansa ne yasa cikin zabura yadaga mata qirjinta
Tashi yayi tsaye yana qarewa yarinyar kallo, gaba daya kunya ta kamashi, yaushe ya aikata hakan? Yarinyar nan shi tunda yake ko kallo bata isheshi ba ko a family house dinsu, amma tayaya zaizo cikin maye ya kwanta a qirjin yar mutane d’ame d’ame?????
Cikin borin kunya ya wanka mata mari
Azabure tatashi ta dafe kumatunta, qwallah tacika idonta, cikin tsananin mamaki tace “ya Fawaz menama?”
Yace “ashe dama ke ana ganinki shiru shiru ke ‘yar iska ce bansaniba? Ni zakizo ki kwantawa a jiki?”
Hawaye ne suka zubo mata tace “ya Fawaz kaine fa kaz…”
Kafin ta qarasa magana yace “waye yayan naki? Amma kuwa bakiyi sa’ar yaya ba, ki kirani guy, bawani fauwaz kingane ko?”
cikin dakinsa ya shige fuuuuu, yana zuwa ya zauna akan gado yadafe kansa,????????♂️ Allah ya soshi ya qwaci kansa awajan yarinyar nan ????
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
“Ibrahim tunda auren yarinyar nan bai iyuba ai bekamata tazauna hakaba ko, yakama ace takoma makaranta”
Baba yadubi Alhaji Isma’iel “to Alhaji wacce makaranta zatayi, kawai tazauna haka har Allah yakawo mata miji tayi aure,”
“A a Ibrahim ba za’ayi hakaba, yarinya zata fara karatu idan Allah yakawo mijin sai tayi aure, akwai maqocina me wannan gidan na hannun damana, already nayi magana dashi, yana aiki a university, yanzu kaje ka dauko min takardun yarinyar Zan bashi, saiya nema mata admission takoma school kawai “
Baba yayi shiruuu, sai can yace” Alhaji da wanne baki Zan gode maka? Alhaji kayimin kayiwa yata? “
” kada kadamu Ibrahim, ai anzama daya “
Alokacin baba yaje ya bincika kayansa yadauko takardun Nihla, yakawo masa, adede lokacin akayi wa Alhaji Isma’iel din kiran gaggawa daga office dinsa,Dan haka yakira wayar mamy yace taturo masa da Nihla, a lokacin suna kitchen suna aiki tare, har Nihla tafara sakin jiki da mamy saboda yanda take janta da fira
Tana fadawa Nihla, tadauki hijabinta dogo tafuto compound din gidan wajansu
Har qasa ta tsugunna tace “gani baba”