DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Alhaji Isma’iel ya kalleta yace “yawwa yata, kije nan gidan kikaiwa matar gidan takardun ki kice inji ni, tabawa mijinta su”

Cikin ladabi ta karbi takardun tafita

Tana fita taga unguwar shiru Kamar Babu kowa, kowa yana gidansa yana sabgar gabansa
Ilham ce tafad’o mata arai, cikin ranta tace Allah sarki Ilham ko ya take yanzu?

“kaga Mazawaje, nagaji da wannan halin naka, saina dinga kiran wayarka amma kashareni?”

karo sukayi da juna, har wayar dake hannun wadda take wayar tafadi qasa
Matar tace “subhanallah, qanwata me kike tunani haka har kina bigeni? Bakya kallan gabanki ne?”

Nihla de tayi shiru tana tunani, inde ba kunnuwanta ne suka jiye mata qarya ba, to tabbas taji wannan matar tace Mazawaje, to dawa take waya acikin family dinsu? Dawa take waya acikin samarin dake Mazawaje family? Koda yake may be da d’an wani family din take wayar

Ganin matar ta girmeta yasa tace “kiyi hakuri Anty, wallahi ban kula bane”

Ita kuma matar jin angirmama ta ance mata Anty yasa lokaci daya taji yarinyar ta shiga ranta

Tayi murmushi, tadafata tace “kada ki damu qanwata, kema anan layin kike ne?”

Nihla tace “eh, bamu dade da dawowa ba, kinga gidan mu can”

Matar tace “laaa ai nasan gidanma, to dafatan de zamu dinga zumunci, menene sunanki?”

Tace “sunana Nihla”

Itama tace “ayya suna Mai
dadi, nikuma sunana NADIYA”????

tofa wata sabuwa, anya wannan zumunci zai dore kuwa?

Shin Nihla ta gane Wacece Nadiya kuwa?

Duk kuci gaba da bibiyata, nagode ????????

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/22, 1:47 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

19&20

Murmushi Nihla tayi “Allah sarki Anty Nadiya, nagode, bari inje an akenine”

Gidan tawuce zata shiga Nadiya tace “to ai gidanmu ne, Dan haka tare zamu shiga”

Daria sukayi gaba dayansu, sannan suka shige gidan

Nadiya ta lura yarinyar akwai abinda yake damunta, tabbas akwai damuwa a atattare da ita, amma zata jata a jikinta har taji damuwarta, Dan ita kam haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata, Kamar qanwarta kasancewar batada qanwa mace sai namiji

Nihla tabawa maman su Nadiya takardun, cikin murmushi takarba tace idan yadawo zata bashi, daga nan Nihla tayi musu sallama tafuto, amma fafur Nadiya tahanata tafiya, qarshe ma dakinta tajata suna fira kadan kadan, Nihla ta lura Nadiya Babu ruwanta, gata da son mutane, Tun tana dari-dari da ita harta sake sukayi ta fira Kamar sun saba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke su uku Sunayin break fast, mamy tadubi Alhaji Isma’iel tace “Alhaji Nihla fa batada kayan sakawa sosai, sannan Babu waya ahannun ta irinta ‘yanmata,kuma ace wannan kyakykyawar yartawa Babu waya Alhaji, yanzu idan tafita ta samomin siriki wacce number zata bashi?”

Yusif yana jinta, ahankali ya kalleta, yamaida hankalinsa kan Abincin dayake ci

Alhaji Isma’iel yayi Murmushi, yaga alama hajiya tanaso ta maida yarinyar tata Babbar yarinya yace”to hajiya ai ga yayanta nan, suje su siyo duk abinda takeso, idan sun kawo kinga akwai abinda babu saikiyimin magana asiyo mata “

Dadi yakama Nihla ta kalleshi tace”Nagode Dad”

“Babu godia a tsakanin mu Nihla, sannan ga albishir ki shirya zuwa next week zaki fara zuwa makaranta, saide kuma zaki bar mamynki da kewa”
Daria sukayi gaba dayansu

Suna gama cin Abincin suka tafi shopping ita dashi, suna tafiya ahanya Babu Wanda yakewa dan’uwansa magana, shi har yanzu maganar mamy ce take masa yawo a zuciya, wai saboda tabawa samari number Hmm

Ita kuma Nihla ganin Yaqi bata fuska akan maganar yasa itama tayi shiru

Har sukaje super market din ataqaice yace mata “Futo”

Babu musu kuwa tafuto, sukayi ciki

Dogayen riguna suka diba, masu shegen kyau, saida suka duba Wanda sukayi mata dai dai sannan suka dauka, inde yaga kalar riga zata karbi fatar jikinta saiya dauka yaqara musu, har mamaki yake bata
Da sukaje wajan kayan kwalliya komai Set yake dauka
Kallansa tayi “yaya Yusif sunyi yawa fa”

Yace “zaki dade kina amfani dasu”

Daga haka bata qara magana ba, suka koma wajan perfume dakuma inner wears, Kallanta yayi, yanzu kam bashida damar dazai zaba mata, yace “dauki mutafi”

Kunya ce ta kamata, haka ta matsa taba zaba, da yaga tana kunyar sa saiya kauce yabar wajan

Atamfofi kuwa sun kwashe su sosai, sannan suka tafi shagon saida wayoyi

Anan ma Kallanta yayi yace “wacce iri kikeso?”

Tace “irin tawa tada, iphone ce”

Haka nan yaji zuciyarsa tana zargin cewa mijinda zata aura ada ne yasiyamata wayar, cikin kishi yace “dole sai irinta?”

Itama da taga fuska ad’aure Babu alamun wasa sai tace “A a, ko wacce ma asiya inaso” ????

Babu musu yasiya mata Babbar waya Qirar Huawei

Sannan suka dawo gida da kaya niqi-niqi

Mamy suka samu afalo tana ganin su tare taji dadi, harga Allah tanason Yusif da Nihla, anan Nihla tabata kayan itama tana gani

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin satin mahaifin Nadiya yanema mata admission a wata private university, Base university, yayan manya ne acikin makarantar kowa tanajin kanta ita watace, gayu kuwa ba’a magana, ko wacce mace tanaji da tata wayewar
Direban gidan zai kaita yadawo da ita, saide kawai zuwa take, amma bata gane komai, damuwar datake ciki ma ta isheta, gashi babu wanda zatai sharing damuwarta dashi bare ta cire maganar datake ranta abata shawara ko zataji dadi baba yahanata kiran kowa na kano
Ahankali sabon su da Nadiya yake qaruwa harta kai kowa yana ziyartar kowa acikinsu

Yauma bayan tadawo daga makaranta tana daki tana duba hand out, Nadiya ta kirata awaya suka gaisa sannan sukai sallama, dena karatun tayi tafuto falo, anan taga mamy tana zuba danbun nama dayawa acikin wata roba, tace “mamy wannan ina za’a kai?”

“Na yayanki ne, zai tafi dashi yanzu”

“mamy ina yaya yusif din zaije?”

Murmushi tayi, ganin yanda Nihla tayi mata Tambayar cikin sauri haka, tace “china zai tafi, akwai aikin dayake son yayi”

Jikinta ne yayi sanyi, ahankali ta karba tace “to mamy kawo nazuba masa”

Bar mata tayi, tazuba masa sannan tace “mamy bari nakai masa”
Bata jira amsar mamynba tayi hanyar dakinsa, akaro na farko Tun zuwan su gidan

Turawa tayi ta shiga dakin nasa da sallama, yana zaune yana hada kayansa acikin truly
Ya amsa mata batare daya kalli Inda takeba, zama tayi akusa dashi tace “ya Yusif gashi inji mamy”

“ajiye anan” abinda yace mata kenan

Ta ajiye masa, zuciyarta tana karyewa Kamar zatayi kuka, duk sai shamata kunu yake tunda yadawo, wai ita ya sukeso tayi ne?

Dauka yayi yasaka acikin jakar tasa sannan yatashi tsaye yace “idan kinsamu time kuje keda Nadiya abude miki account idan kina buqatar kudi saiki kirani ki fadamin, zan tafi yanzu, may be nadawo dawuri”

Yana fada mata haka bakowa ne yafado mata araiba sai ya Abba, duk alamomi sai yanzu suke nuna mata cewa dama ya Abba baya santa, itace takasa gane hakan soyaiyar sa ta rufe mata ido, duk su ya Usman Babu abinda basuyi mata lokacin data dawo kano, kowa yana nan nan da ita, amma shi ya Abba itace take nan nan dashi, ????
Gashi shima ya Yusif yadawo amma bata bashi kulawar komai ba sai shine yake hidimta mata, batasan lokacin da hawaye yazubo mataba, ahankali ta miqe tsaye tafada jikinsa tana sakin wani irin kuka abaiyane

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button