DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Qam Yusif yaqame a tsaye, shibe tureta ajikinsa ba, shikuma bai saka hannu ya rungumeta ba ????
Kuka take sosai har hawaye yana d’isa agaban rigarsa
Wata irin ajiyar zuciya yasaki, sannan yasaka hannu ya rungumeta gaba daya, yana bubbuga bayanta, wani irin yanayi ya tsinci kansa aciki, Wanda bai tabajin irinsa ba, cikin kasalalliyar murya yace”kiyi hakuri mana kiyi shiru, menene na kukan? Me aka miki?kokuma Wanda zaki aura kika tuna? “
Girgiza kanta tayi, tace” dan Allah kayi hakuri, kadena fishi “
Yaga alama idan akaci gaba da tsaiwa ahaka to yarinyar nan zatasa yayi mata ba daidai ba, Dan haka ya janye tadaga jikinsa, yace” ya’isa to, ni bana fishi dake, kuma kece yakamata nabawa hakuri, tunda kina ganina kika share ni, saboda kin samu wani”
Wasa tafara da yatsun hannunta tace “kayi hakuri, kuma ba kullum saina kiraka ba, amma wayar taqi shiga”
Tafadi haka cikin shagwaba
Murmushi yayi “to naji, komai yawuce, yanzu Muje ki raka yaya Yusif zai tafi kada yayi missing flight, but banda bawa samari number, kinji ko?”
Daga masa kai tayi, tace “to”
Sannan ta janyo masa jakar suka futo daga dakin, mamy bata falon, kai tsaye dakinta suka nufa domin yayi mata sallama
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Dawowar sa kenan daga makaranta duk yagaji, ga yunwa dayakeji yaji Kamar ana buga get din gidan
Tsaki yaja sannan yatashi yafita, yana budewa yaga samari su uku dukansu yarane bazasu wuce 27 ba, gaba dayansu sun tsuke cikin qananun kaya, kallansu yayi dakyau yace “samari lafiya kuwa? Ko wani gida kuke nema?”
Daya daga cikin su yace “dama munzo wajan qawarmu ne, munyi waya da ita, so tace mana tadawo nan gidan dazama”
Cikin mamaki yace “qawarku kuma? Inaga kunyi batan hanya ne, ba nan bane”
Na biyun yace “bawan Allah ya zakace mana ba nan bane, bayan nan gidan tayi mana kwatance?”
Yace “Wacece qawar taku?”
Na ukun yace “Diyana”
Tsayuwarsa ya gyara yace “Ok ai sai yanzu nagane ku, ashe wajan aminiyarku kukazo, to bismillah, kushigo mana”
Wanda yace wajan Diyana sukazo yakalli Adam dakyau, anya kuwa zai shiga? Da alama fa wannan yayan tane, karfa su shiga yamusu shegen duka ????
Saiya girgizakai yace “no, Barshi kawai,”
Ya kalli sauran yace “Baba kuzo mu ware kawai” ????
Sukuma biyun suka dage sai sun shigo, Adam yana tsaye cikin zuciyarsa yana addu’ah su shigo gidan, ysce”ku qaraso mana, tana ciki fa maryam din “
Sunfara shigowa gidan kenan sai daya yalura da yanda Adam yake tattare hannun rigarsa aboye ????, sai yaja dan’uwansa ya tsaya
Adam yajuyo ya gansu sun tsaya yace” me kuka tsaya yine? Rakaku zanyi “
Adede lokacin tafuto daga cikin dakinta zuwa compound din gidan, tunda aka kawota gidan yaune kawai Adam yaganta da atamfa a jikinta dinkin riga da Zani, kuma sai kayan yayi mata kyau sosai
Tana ganin mazan tasaki murmushi tace” guy’s, ya garin? Yakuka tsaya daga nan? “
Murmushi sukayi, atare sukace” zamu dawo, Karki damu zamu dawo next time “daga nan suka fice da sauri
Itama tajuya cikin gidan ko kallan Adam batayi ba, shikuwa binta yayi da kallo yace” Allah ya shirye ki “
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da yamma suna zaune afalo shida ita, kanta ko dankwali Babu dana daddana wayarta, shikuma yana can kujerar qarshe yana cike wasu takardu daya karbo awajan Abba
Tun safe rabonsa da abinci, Dan haka yana gama cike takardun yadago kansa ya kalleta
Besan meyasa yarinyar nan take san zama kai Babu dankwali ba, amatsayinsa na saurayin yayarta ai yadace ace tana shiga ta kamala, amma kullum kai Babu dankwali, wani lokacin ma shigar da zatayi idan yaganta daqyar zai dauke idonsa akanta ????
Badan yana ganinta amatsayin qanwar budurwar sa ba ai zata iya saka shi awani hali
Ajiyar zuciya yayi yadaga murya yanda zata jiyoshi, saboda basa zama waje daya yace “ke tashi kikawomin abinci”
Hankalinta yana kan waya tace “banajin yunwa banyi abinci ba”
Yace “Wato Ilham na lura kanki yana rawa acikin gidannan, rashin kunyar ki tafara kaini bango, Karki qureni kuma”
“to yanzu yaya Aslam girki akace nazo nayi kome? Ni wallahi bazan iyaba, saikace wata jaka”
Yace “okey Wato nida nake nemowa na kawo gidan na ajiye nine jaki, ????
To bari kiji Dan Allah ki yarda nasake yimiki maganar abinci acikin gidannan”
Yana fada mata haka yatashi yafice ransa abace, wannan qaddararran auren yafara isarsa, haba!
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
“A’a, yanmatan Yusif, kece atafe kenan”
Ajiyar zuciya tayi “wallahi nice Anty Nadiya, mamy tafita unguwa, saini kadai agidan shiru, shine nace bari nataho wajan ki kawai” cewar Nihla
Nadiya tace “hakane kam, kin kyauta masha fira, gashi saurayin naki ma yagudu china”
Murmushi Nihla tayi “wai yaya Yusif, aiba saurayina bane Anty Nadiya, Yaya Yusif yaya nane, yayi min abinda dan’uwana yakasa min, inajin sa a raina tamkar yayana da muka futo ciki daya”
Gyara zama Nadiya tayi tace “waye dan’uwan naki?”
Kai tsaye tace “yaya Abba”
“yaya Abba kuma? Kifuto fili kimin bayani Nihla, NI DAKE, munzama Kamar yaya da qanwa, yakamata kibani labarin ki, menene yake yawan sakaki tunani, har kike bige mutum ahanya batare dakin saniba?” ????
Nihla tace “Anty Nadiya, labarins yana cike da abin tausayi, nida iyayena natashi, mahaifina ne qaramin qarfi ne, bayan na girma mamana ta rasu, nakoma gidan yayanta da zama har Allah yadawo dashi daga qasar waje”
Nadiya tace “wakenan? Kici Gaba mana”
Hawaye ne yataru a’idonta, tace “yaya Abba, Tun muna yara nasaba dashi, har na girma da tunanin sa acikin qwaqwalwata,ganin irin sabon damukai dashi muna yara yasa ya daya dawo daga qasar waje nake kula dashi, yanda nake masa zaki dauka ansaka mana ranar aure ne, ashe shi ba haka bane acikin ransa, yanada budurwa, ranar da akace anhadamu aure acikin mutane yace bayasona, akwai wadda yakeso, ahaka iyayen sa zasuyi mana auren bayan an lallabashi ya amince, sai ranar auren babana yaje yadauko ni, muka Taho nan garin ta dalilin baban yaya Yusif, wannan dalilin ne yasa naje ganinsa Kamar yayana uwa daya uba daya, Yaya Yusif yamin abinda yaya Abba yakasa min shi “tana gama bata labari tashare hawayen idonta taci gaba da cewa” bansani ba ko bankai yasonin bane kokuma banida abin dazai gani a wajena yasoni “
Kai tsaye Nadiya tace” qwarai kuwa bakidashi Nihla “
Da sauri Nihla ta kalli Nadiya cikeda mamaki
Nadiya tace”Nihla Dafarko ki kalli Hijabin dayake jikinki, ki kalli irin atamfar datake jikinki, wallahi idan ni kika bawa wannan atamfar taki saina tambayeki dalili, saina zaunar dake nace Dan Allah meyasa kika bani wannan kayan? A a kin renamin hankali ne kokuma tsabar kin maidani yar qauye ne yasa kika banisu? ????????
Nihla samarin wannan zamanin fa saida dabara, na farko namiji yanason mace Mai aji, Nihla kinje kina zubda ajinki agabansa abanza, wasu mazan zakiga duk wata mace Mai yi musu biyyaiya to zakiga hankalinsu baya kanta, idonsu yanacan wani waje, Nihla tunda nake dake bantaba ganinki Babu hijabi ba, kullum kina cikin hijabi, tayaya zaiga kwalliyarki har wani abu yaja hankalinsa yaji yana sonki? ????
ni macece ‘yar’uwar ki amma tabbas na yabawa kyanki, kinada kyau Dan kyau, amma awajan wani na mijin hankalinsa bayakan kyau kokadan, hankalinsa yafi karkata kan abubuwan more rayuwa, kuma ke bakidasu”
Nihla tayi shiru tanajin maganganun Nadiya, acikin maganar ta Babu ta qarya