DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Nadiya ta dafata tace ” babanki yamiki gata daya dauko ki,saboda dakin aure shi ma wahala kawai zakisha, sannan kuma ki godewa Allah dakika hadu Dani, domin kuwa komai yazo qarshe, zan temaka miki, kishigo gari Kamar ko wacce budurwa da takeji da kanta, ta yanda Abba kikace kowa? Bashi kadai ba kowanne namiji ma idan yaganki, saiya sake kallan ki, amma bazai iyuba saikin kwantar da hankalin ki, kin cire shi aranki “
Nihla ta kalli Nadiya tace ” gaskiya Anty Nadiya inason ya Abba “????
Murmushi Nadiya tayi tace” matsalar ku kenan yara, saiku dauki soyaiya kusa aranku Tun bakuje ko’inaba, kinganni nan Nihla, babu na mijin dazan zauna ya renamin hankali,
Idan naga take takenka agu Zan tattaraka na ajiye agefe, akwai wani saurayina SADIQ MAZAWAJE, naje germany karatu anan muka hadu, shida kansa ya nuna yana sona kuma na amince, sai daga baya nagane cewa nayi kuskure danake saurarensa, na farko bayamin kalaman soyaiya, sannan bayasan kirana nice nake ta kiransa, ke qarshe ma kwanaki dana kirashi muna waya kawai naji yana magana da wata mace agefe, naji yana cewa zoki ajiye anan, wallahi Nihla tunda nakashe wayata ban sake nemansa ba sai rannan, amma ni Inda yake birgeni akwai riqe alqawari, munyi alqawari dashi zamuyi aure, amma gaskiya Nihla nagaji, ko wacce mace tanason kulawa, amma ni bana samu awajansa, aikinsa kawai yasa agaba,tunda nagane haka saina saka shi awani bangaren daban na ajiye, naci gaba da kula samarina masu bani kulawa, (????)
To kinga ko rabuwa mukai dashi bazanji wani haushi ba, bari kiga pic dinsa “
Wayarta tadauka tadubo pic dinsa, tadorawa Nihla data zama mutum mutumi wayar akan cinya, tace “bari in shiga toilet na futo”
Batare data lura da yanayin Nihla ba tashige toilet
dak! dak! Gaban Nihla yake faduwa, cikin ranta ta furta yaya Abba!!!
Gaskya ne, Sadiq yana nufin Abubakar kenan, yanzu dama yaya Abba shine saurayin Anty Nadiya? Saboda Anty Nadiya yaqita?
Kallan pic din tayi, karon farko data taba ganinsa cikin kakinsu na pilot Mai launin fari da baqi, yayi bala’in yin kyau a pic din, yana zaune akan kujera wajan da’ake tuqa jirgi
Wato ita da yakeso harta samu pic dinsa, amma ita batakai wannan matsayin ba
Jikinta har rawa yafara saboda tsananin firgita, abin yabata mamaki sosai, dole dole tasan abinyi
Nadiya ce tafuto daga toilet tace “kin ganshi?”
Cikin in’ina tace “eh na.. naganshi Anty Nadiya, amma yayi kyau”
Nadiya tace “ke rabu da wannan kyan yarinya, kyau Babu kulawa ina wani kyau, idan na aure shi kyan zanci ko kulawar zanfi buqata, shareshi kawai” ????
Hausawa sukace naka nakane, hakanan taji bataji dadin furucin Nadiya ba, meyasa zata fadawa dan’uwanta haka?
Nadiya tace, kishirya gobe zamuje kasuwa akwai abubuwan dazamu siyo, sannan kincemin akwai atamfofin da Yusif yasiyo miki basuda dinki, zamuje wajan telana ya gwada ki yayi miki dinki nagani nafada, Sanna wannan kan naki zamuje wajan saloon awanke shi, wani satin kuma sai Muje wajan gyaran jiki ayi miki, sonake qanwata ta sauya ta yanda Babu wani na mijin dazai qara rena miki hankali “
Murmushin yaqe Nihla tayi” tace ” to Anty Nadiya, Allah yakaimu, dama akwai kudin dayamin saura irin Wanda ya Yusif yake bani, saimu hada dashi”
Nadiya tace “Karki damu nima akwai kudi a wajena,”
Washe gari Tun safe suka yiwa many sallama suka tafi wajan tela, Nadiya ce ta karbi tif din da kanta ta aunata, kuma itace tabasu irin Style din datake so ayi mata, daga nan kasuwa suka wuce suka sai :
Alkama
Shinkafa
Gyada
Ridi
Dawa
Hulba
Gero
Aya
Zogale
Kanumfari
Waken soya
Sannan suka dawo gida,Nadiya tace” Sai gobe kuma zamuje wajan saloon,da wankin qafa, “
Nihla tayi shiru ta kalli kayan dasuka siyo tace” yanzu Anty Nadiya me za’ayi da wannan hadin? “
Murmushi tayi tace” kece zaki dinga sha kullum safe, da dare, idan zaki iyama har rana, zakisa ka ruwa kadan ya tafasa saiki debi garin wannan maganin kidamashi a cup dadan kauri, saiki zuba acikin Ruwan zafin nan nakan wuta kina juyawa har yayi kauri saiki juye kidinga sha da madara ko nono kindirmo, Nihla nabaki wata uku cikakke qirjinki zai qara cikowa sosai, Sannan hips dinki ma zasu sake budewa “
(yanmata masu buqata da matan aure zaku iya gwadawa yanayi sosai, shine de ake zuba mukushi aroba azo asiyar muku shi dubu uku uku, dukansu zaki hadesu waje daya ki soya su sama-sama, saiki kai aniqa miki, ki tankade kidinga damawa kinasha ????????)
Jikin Nihla yayi sanyi, jiki a sanyaye tayi mata godia ta tafi gida dashi,da daddare tana zaune agadon ta har sha biyu na dare takasa bacci, tunanin Nadiya kawai take, dame zata sakawa Anty Nadiya? Yazama dole ta cire ya Abba daga cikin zuciyarta kodan Anty Nadiya,dole zata dage da addu’ah akan Allah ya yaye mata, afili ta furta ” insha daga yau nahakura dakai ya Abba, koda sanka zaimin illa insha Allah daga ranar yau, nahakura da kai, saide yamin illlar”
(kunga laifin Nihla? ????)
Ina godia sosai da sosai masoyana, yan group din DANGI DAYA kuna sani nishadi, wallahi sharhinku yana bani dariya ???? oh Abba ma yaga takansa ????
Amnah El Yaqoub ✍️[6/22, 11:41 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
21&22
Tunani taci gaba dayi, mahaifin ta bashi dashi Mai qaramin qarfi ne, meyasa ma Tun farko hankalinta Yaqi karkata kan karatu? Wata zuciyar tace saboda soyaiyar Abba
Juyi tasakeyi, gashi wadda yaqita saboda itanma bawani sonsa takeba, ita kuma yafuto bainar jama’ah yace baya sonta, gara ta hakura itama dashi, idan taci gaba da sonsa har Anty Nadiya tagano gaskiya haqiqa zatace ta munafurceta, to gara Tun wuri ta tsaida Rayuwar ta waje daya, itama ta haqura dashi dukda tasan abune Mai wahala amma dole zata kamanta , tsaki tasaki afili, tayi juyi tareda addu’ah tarufe idonta
Washe gari suka tafi wajan saloon bayan tadawo daga makaranta,ba Nadiya kadai ba, hatta masu shagon tsayawa sukai ganin yanda gashinta yaqara tsawo, gashi Kamar ba ‘yar hausawa ba, ita kanta wata irin iska takeji tana shigar ta
Duk lokacin data ga Anty Nadiya saita tuno da ya Abba, amma tana kokarin kawar da tunanin sa acikin zuciyarta
Sati na zagayowa sukaje wajan gyaran jiki, Nihla saita koma Kamar wata amarya, mamy de tanata Kallanta tana wannan bidiri, saide tayi Murmushi kawai, taga take taken Nihla qarfi dayaji sotake ta sauya
Sosai ta maida hankalinta akan karatu, babu ruwanta da kowa a makarantar, kawai karatun ta tasa agaba,dinkunanta da sukaje suka karbo shi tafara sakawa, babu meyi mata kallan raini, bata shiga harkar kowa bama bare ta fuskanci wani bacin rai
Kamar yauma tana zaune awaje daya cikin makarantar, littafi ne a hannunta tana dubawa, taji anyi mata sallama, dago kanta tayi ta dubeshi, batare data ce komai ba, shima yayi Murmushi Yazauna dab da ita yace “baki ganeni ba ko?”
Tace “eh, bangane kaba”
Yayi Murmushi yace “qanin Anty Nadiya nefa Abdallah, anan makarantar nake nima, tacemin kullum kina shigowa shine taturo min number ki tace nanemeki, to nakira taqi shiga sai ita nakira tafadamin Inda zan sameki”
Lokaci daya tayi Murmushi tace “ashe kaine, ai inajin labarin ka awajanta,amma ban taba ganinka ba, ya gari?”