DANGI DAYA HAUSA NOVEL

“wallahi ina wajan friend dinane, kawo natayaki karatun”
Yaja littafin ta yana gani, itama da taga yanada kokari saita fara Tambayar sa abinda bata saniba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe take shiri zataje wajan biki, wanka ta dauka taci kwalliya Kamar me, sannan ta shirya tsaf tafice batare data kalli ko Inda dakinsa yakeba, shima daya shirya yafuto zai tafi makaranta bai gantaba, kuma beyi tunanin neman Inda tatafiba, Yarufe gidan yayi tafiyar sa
Tun azahar yagama abinda yake amma saiya zauna baidawoba sai yamma, daya dawo gidanma abin mamaki bata nan, yayi shiru yana tunani, yarinyar nan tunda akai aurensu gaisuwa ma bata Hadashi da ita, ga mu’amula datake da samari awaje duk yana sane da ita, me zaiyi mata ne yaja hankalin ta ta daina abinda take?
Dariyar dayaji ne yasa yadago kansa da sauri ya kalleta, wani shegen mayafi tayafa ga kayan datasa dinkin irin dede da itan nanne, ta kalleshi taci gaba da wayarta tana cewa “ashe pictures sunyi kyau, kaima kagani ashe,”
Ta saki dariya tashige dakinta
Adam yabita da kallo, yanzu idan Diyana zata fita bekai tafada masa Inda zataje ba? Anya yarinyar nan kuwa tasan me ake nufi da aure? ????
Binta yayi cikin dakin tana zaune tana cire Dan kunnanta, yace” daga ina kike? “
Hankali kwance tace “daga gidan bikin wata qawata”
“ke ba’a isa da keba kenan, kindauki qyale qyalen duniya kinsa aranki, maza suna kawo miki ziyara, kinada aure akanki kina waya da wasu qartin banza, to Karki Manta de da aure na akanki, kuma duk abinda kika aikata zunubi kike kwasa akanki”
Kallansa tayi tace “zunubi?”
Takaici yakama Adam, tabbas idan yaci gaba da kula yarinyar nan, zai iya yimata dukan tsiya, kuma yasan hakan a addinance Babu kyau, cikin bacin rai yafice yayi dakinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Kalau yadawo gidan yau yana cikin nutsuwarsa,yana sanye da qananun kaya sunyi masa kyau sosai, kayan kallo take gogewa tadago taganshi taci gaba da abinda take, beyi mata sallama ba yaqaraso falon Yazauna yana ganin yanda take komai cikin nutsuwa, itama ko kallan Inda yake batayiba, harta gama tashige kitchen
Bayanta yabi da kallo kenan shi yarinyar nan saboda bata daukeshi a mijiba ko gaida shi ba zatayi ba bare sannu da zuwa
Ajiyar zuciya yasaki yatashi ya shige d’akinsa, Dan qaramin fridge din dakin nasa yabude yadauko magungunan maye ya ajiyesu a gefensa, Yazauna agefen gadon yabude kowanne yasha, sannan ya koma gadon ya kwanta yana lumshe idonsa
Acan kitchen kuwa Dida lemon Kankana tahada Mai dadi tahada da Abincin datayi tazuba masa sannan tafuto zata kawo masa, tana zuwa falon taga baya nan, Dan haka kai tsaye tashige dakin da Abincin
Tana zuwa gabanta yafadi ganin uban kwalaben dake gabansa shikuma gashinan Akwance yana bacci ko takalma bai cire ba
Girgiza kai tayi ta ajiye Abincin agefe ta tsugunna tadauke kwalaben, karantawa tayi, afili ta furta “Benalyn, Codein,Emzolynn, ????????♀️tabdi harda su Emzolynn acikin kayan mayen?”
Karaf maganar ta shiga kunnansa, a lokacin bacci yafara fizgarsa
Dida kuwa kwashe shu tayi, ta ajiye masa agefe,kafarsa takama tafara kokarin cire masa takalmin, tana cirewa ta zubawa kafarsa ido tana gani, kafar me kyau kuwa, saide Mai kafar bashida kyan hali, ahankali tatashi zatabar wajan yasa kafarsa yabigeta, lokaci daya ta’iyo kansa tafada Kirjinsa, sai jin mutum yayi akan Kirjinsa, Dasauri yabude idonsa yazuba mata ido yana Kallanta
Dida kuwa idonta yana kan bakinsa, meyasa yana shan kayan maye amma lips dinsa beyi baqi ba?
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Kasancewar yasan Babu me shigo masa daki yasa daya futo daga wanka yana daure da towel iya qugunsa yanufi cikin kayansa yadauko manyan kaya, saboda baqi dazasu gani shida Abba akan shirye shiryen bude campany nsu.
Kayan yadauko ya ajiye sannan yagama shafe shafensa yadawo zai saka kayan, gajeren wando yadauko, ya cire towel din ya wulllashi kan gado, zai saka kenan sai gata taturo kofar dakin tashigo ????????♀️
Tana ganinsa haka tasaki qara tafuto aguje, gabanta sai faduwa yake, Innalillahi..????,meyakaita dakin yaya Aslam?
Shikuwa Aslam yana jin qaranta ya tabbatar yarinyar taganshi, qarasa saka wandon yayi Yazauna agefen gadon yadafe kansa ????????♂️, shikkenan girmansa yazube a’idon qanwar budurwarsa, zance yaqare taga komai
Haka yatashi ransa abace yagama shirya wa yafuto, tana ganinsa futowarsa takwasa aguje tayi dakinta, shikuwa Aslam ko Kallanta beyiba yawuce zai fice daga falon, ta kalli bayansa tasaka dariya, tashige dakinta
Sarai yana jinta yayi fuska ya shareta, toba dole tayi masa dariya ba, duk yanda yake kare mutuncinsa saida yarinyar nan taga komai, wallahi yanda yakeji aransa idan ta kuskura yadawo tayi masa dariya wallahi sai jikinta yayi tsami ????
Bayan sun gama ganawa da baqin harma suntafi, sun tsaida ranar dazasu shirya bude campany, Aslam yayi shiru yana tunani, Abba ya kalleshi yace “meke damunka”
Ajiyar zuciya yayi yace “wallahi Abba akwai damuwa”
“wacce irin damuwa?”
“Abba kaga tunda akai auren nan, yarinyar nan ko abinci bata min, kullum ina wajan cin abinci, idan na yi mata magana tafadamin ba dadi”
“Aslam wannan ne dalilin dayasa nake fada muku kudena kula qananun yara, amma bakwa ganewa,”
Ajiyar zuciya yayi yace “yanzu de abinda nake fadama yarinyar nan fa taga komai, koda nayi mata fada bama lalle taji ni ba”
Abba yace “Kamar ya, mekake nufi”
Cikin haushi Aslam yace “kagane mana, saina futo fili nama bayani ne”
Dariya takama Abba, sosai yake dariya yana kallan Aslam
Aslam yace “tomiye kuma abin dariya, miye hakan, wallahi Zan huce akanka”
Abba yace “maida wuqar abokina, kaima saika rama abinda tama, kaga shikkenan kunyi 50 50, babu wanda zaiyi wa wani dariya”
Kallan Abba yayi yace “Kamar ya Abba? Ma kake nufi?”
Abba yakama Kunnan Aslam yayi masa rada
Lokaci daya sukasa dariya, Aslam yace “kai Abba wallahi bakada dama, natafi, yanzu yanzu zanje nasiyo, sai munyi waya”
Daga nan kowa yayi gida
Aslam bai zarce ko’inaba sai wani super market da ake saida kayaiyakin wasan yara, daga nan yayi gida, lokacin yamma liss, yana shiga falon yaji qamshin abinci yadaki hancinsa, ahankali yaleqa kitchen yaganta tana girki tana waqa hankali kwance, cikin sand’a yadawo da baya yashige cikin dakinta, yabude toilet dinta yadauko lizard cikin aljihunsa yasaka mata shi dede Inda yaga tana shanya panties dinta, cikin sauri yafuto Yarufe dakin Ahankali ya koma falon Yazauna yadora kafa daya kan daya yana jijjigata
Agabansa tafuto daga kitchen din, ta kalleshi tayi Murmushi, tazauna tazuba Abincin ta ita kadai tanaci tana murmushi
Kallanta yayi yasan sarai dashi take, sotake yamata magana tafada masa marar dadi, Dan haka yayi shiru yaqyaleta, suna zaune ana kallan kallo har dare yayi, bega tatashi ta shiga dakiba, shikuwa sallah yake zuwa yadawo falon Yazauna, daga qarshe ma bayan sallar ishsha’i wanka yayi yadawo falon Yazauna yana kallo, abin harya fara bata mamaki, yatsina fuska tayi tashige daki, zuciyarta daya tazage ta shiga wanka, cikin nishadi tasha wankan ta tas, ta janyo towel zata daura kenan tayi ido biyu da qadangare, tsaro ido tayi????
Cikin faduwar gaba tace ” Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, nashiga uku me yakawomin masifa cikin toilet” dagudu tafuto towel ahannu