DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Shikuwa yana zaune yana kallo yana shan lemo, yana jin salati yace “lokaci yayi kenan” ???? Ahankali yatashi yayi hanyar dakin, yana zuwa bakin qofa sukai karo, jikinta yana karkarwa ta kamashi ta riqe, cikin tsoro tace “yaya Aslam qadangare a toilet dina, wallahi yana ciki, Muje ka ganshi”

Aslam kuwa gunki yazama a tsaye, magana take masa amma yadade da shagala yana kallan surar jikinta, ashe haka yarinyar nan take?

Jijjigashi tayi tace “yaya Aslam!!!”

Firgigit yadawo cikin duniyar mu ????
Yanayin sa yadan sauya kadan, ya kwashe da dariya yace “to daura towel din”

Sai a lokacin talura da towel din dayake hannunta, kunya ta kamata, cikin sauri taja tarufe jikinta, amma takasa kallan idonsa ????

Futowa yayi yabarmata dakin, tabiyo bayansa, yana dauke kafa tana maidawa, yajuyo ya kalleta yace “wai menene?”

Cikin shagwaba tace “to Muje kacire min shi mana, haka kawai saika tafi kabarni”

Banza yayi da ita ya kashe kayan kallo yadauki wayarsa yayi hanyar dakinsa, itama ta doru abayansa ????

Dakinsa yashiga, yafara cire kayansa,cikin sauri tajuya masa baya, Kallanta yayi yanda tajuya bata kalleshi ba, ya zubawa cinyarta ido daga baya, yadauki jallabiya yasaka, yahau gadon ya kwanta

Tanajin ya kwanta tataho kansa ta tsaya tana share hawaye, yanajinta ya qyaleta, ita kuwa daga ta haka saita qara gunjin kuka, tsaki yayi yatashi yafuto yabar mata dakin, itama tasake futowa, cikin ransa yace yau naga ta kaina ????
Hanyar fita daga falon yanufa tabiyoshi, yajuyo ya kalleta “ina zakije ahaka?”

Cikin kuka tace “Allah bazaka fita kabarni ba”

Yace “abinci nakeso naje nasiyo, banaso dare yamin”

Tace “to baga abinci can a kitchen ba, basai kaje kaciba”

Cikin sauri yace “ni? A a riqe abinki, Abincin da ba’abanishi Dan dadi ba saidon wuya?”

Yana fadin haka ya juya zai fice, tasa hannu ta riqe gefen jallabiyarsa
Yuyowa yayi ya kalleta ya girgiza kai sannan yadawo falon Yazauna, itama tadawo tazauna akusa da qafafunsa ????

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Computer datake gabansa Yarufe ya ajiye ta agefe, sannan yadauki coffee din da Adala Sabuwar Mai aikin Momy takawo masa
Yana kai coffee din bakinsa ya runtse idonsa, zaqi yayi yawa, shikuma bayason zaqi, ga shi kansa coffee din har wani d’aci-d’aci yakeyi

Tsaki yaja, yadauko cup din yafuto falo yana kwalawa Momy kira “Momy! Momy!!”

Momy dake kallo afalo tadago idonta ta kalleshi, tace “Abba nah menene?”

Cikin damuwa yace “Momy waye yahada wannan coffee din?”

Tace “waye zai hadama coffee Abba bayan Adalaiye? “

Tamkar qaramin yaro haka yafara yimata shagwaba “Momy wallahi Babu dadi, zaqi yayi yawa, kuma ni kwata kwata ma bayamin dadi abakina Kamar yanda yarinyar nan take min, duk Babu teste”

Momy tayi shiru tana kallansa, Wato Nihla ce bazai fad’aba saide yarinyar nan,ai already Nihla tagama bata Abba da wannan shegen coffee Kamar qa’ida, Tun bayan barinta gidan komai yaci yadinga mita kenan shi Babu dadi ????

ajiyar zuciya tayi afili tace “Abba Tun yanzu?”

Ko’ina masu lizard zasu kwana yau? ????

Oga me coffee ko yaya abin zaici gaba da kasancewa?????

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/23, 11:31 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️

{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

Wannan page din na’yan la’be ne????
kawai sonake yau kuma ku futo kuce wani abu

23&24

Yace “Momy me kike nufi?”

“A a, babu komai Abba, zanyi mata magana saita gyara”

Ajiye cup din yayi “no kibarta Momy, kawai de daga yau karta sake min”

Haka ya juya cikin dakinsa ransa duk ajagule, zama yayi yadauki wayarsa yafara kiran number Nadiya, but number busy, cikeda mamaki yakalli agogo “to Dawa take waya Awannan lokacin ?”

Babu me bashi amsa, Dan haka yayi wulli da wayar ya kwanta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Har sha biyu suna zaune jugum jugum afalo, Aslam sai hamma yake yanaso yaje ya kwanta, gashi wannan yarinya ta hanashi sakat, tazo tasa shi agaba da wannan shegen towel din nata Wanda dashi ma gara Babu
Ahankali yatashi yayi dakinsa, tatashi tabishi, Bece mata komai ba yahaye gadonsa ya kwanta, kujerar datake dakin nasa tahau ta kwanta itama, saide atakure take
Yakalleta yace “kitashi kibarmin dakina”

Ilham kuwa tana jinsa tayi banza ta qyaleshi
Wai akan masifa ta sameta yake korarta, Hmm zata rama ne, da haka tayi addu’ah sannan tayi bacci, shikuwa kasa baccin yayi yazuba mata ido yana Kallanta dukda ta juya masa baya, daqyar yasamu yayi bacci bayan fama da juye juye dayake, idan Yarufe idonsa, surarta kawai yake gani

Tun kafin tatashi daga bacci asubar fari yatashi yaje toilet dinta ya cire lizard din sannan yatafi masallaci

❣️❣️❣️ ❣️ ❣️ ❣️

Yau daga makaranta gida yawuce, yadade agida sannan yakamo hanyar gidansa
Tun kafin yasako qafarsa cikin falon ya ganshi kaca-kaca, yariqe qugu ya tsaya yana qarewa falon kallo, fillow’s din dake kan kujera duk wasu aqasa, matsawa yayi yaje wajan kayan kallo yasaka hannu yataba, yana duba hannunsa yaga qura

Daga murya yayi yafara qwala mata kira “maryam! Maryam!!”

Cikin sauri tafuto daga dakinta,fuskarta cikeda kwalliya, riga da wando ne a jikinta, rigar nan takamata kyam ajiki, wandon kuwa tacika abin ta, Dan qaramin mayafi ne a hannunta tana kokarin nad’ashi akanta tace “gani”

“yanzu maryam abinda kike acikin gidannan yadace kenan? Bakisan mukwana dake acikin gidannan kibudi baki kice Dani ina kwana ba, idan zaki fita unguwa bankai matsayin dazaki tambayeni ba,bakisan kidafawa mijinki abinci ba, now kalli gidannan, kina nema kibar min gida ya lalace, kalli, kalli Dan Allah cikin falon nan “

Yaqarasa magana yana nuna mata cikin falon

Kallansa tayi ” yanzu ya Adam duk kokarin danake dannaga na zauna dakai lafiya baka gani? Auren nanfa baso nake ba, sannan kana maganar abinci aikai malami ne kasani, haqqinka ne kaci Dani sannan kashayar Dani, ni bazan iyaba!, bazan iyaba!! Bazan takura kaina ba, in tashi dasafe, inyi wanka, inyi kwalliya, inyi kokarin hadawa kaina abinci, sannan kuma inzo ingyarama gida, na maka girki, saboda samu ma inyi mopping,inturara gida da turaren wuta, saikace a novel? Aljanar inace nida Zan yi wannan aikin kullum? ????
To kaga ni gaskya ko agaban iyayena Babu me takuramin ehe! “

Tana fadar haka tajuya takoma cikin dakinta, jagwab Adam Yazauna akan kujera tareda dafe kansa ????????‍♂️maryam zata haukatashi

Yadade azaune sannan yatashi yatattare hannun rigarsa yadauki tsintsiya yafara share gidan, takan dakinsa yafara sannan kitchen, sai kuma falo, mopper yadauko ya goge falon tas, sannan ya goge kayan kallan yadauko qur’ani adaki yadawo falon yana karantawa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda taga ya Fawaz har gida yake shigowa da kayan maye yasaka acikin fridge ta shiga damuwa, ya Fawaz koshi ba dan’uwanta bane yakamata tafara nuna masa abinda yake ba daidai bane, balle ma shidin mijinta ne, haqqin kula dashi yana kanta
Jiya tatuno saida yagama qarewa fuskarta kallo sannan wai ta d’agashi tunda dama tasaba ????

Ahankali tatashi tashige cikin dakinsa, ta gyara masa dakin tas, ta lailaye masa gadon tsaf, fridge din dakin tabude kwalaben maganin maye dana mura gasunan birjik, shiru tayi tana tunani, tarasa mafita Dan haka tadau wayarta takira yayarta, bugu daya ta dauka tace “Diyana kinga dakin ya Fawaz nake gyara wa bakiga kayan maye ba, nikuma banaso yanasha wallahi, Yaya zanyi dasu ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button