DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Diyana tace “um lalle Dida agaisheki, ke har gyaran dakinsa ma kike, tab!”
Dida tace “toya zanyi Diyana, mijina ne ko mahaukaci ne shi dole Zan kula dashi ahaka”
Batare da tunanin komai ba Diyana tace “kidebesu kizubar kawai”
Dida tace “to shikkenan nagode Diyana” daga haka takashe wayar, takwashe duka magungunan tafitar dasu waje ta tsiyayar dasu sannan tayi watsi da kwalaben
Tadawo ta goge fridge din, ta dauko lemuka a kitchen da ruwa tazuba masa su sannan tafuto daga dakin
Abinci taje tadafa musu bayan tagama tayi wanka tadawo falon tazauna tana game a wayarta
Ta dade azaune awajan sannan yashigo gidan, yau yayi mata sallama, cikin ladabi ta amsa masa, tace “a kawo ma abinci ne?”
Yatsina fuska yayi “no kibarshi kawai, ke kidena dafa abinci Ma Dani, kiyi rayuwarki kawai”
Batare data ce masa komai ba ta kwanta taci gaba da abin datake
Yana shiga dakin ya ganshi yasha gyara sai qamshi yake, zama yayi agefen gadon afili yace “wannan yarinyar da naci take wallahi”
Fridge dinsa yabude nan yaga Babu komai, cikin bacin rai yace “kan ubannan!!!”
Belt din jikinsa ya cire yafuto falon afusace, Dida tanayin game kawai sai Saukar belt din taji a jikinta, cikin sauri tatashi tana sosa wajan, be tausaya mata ba yaci gaba da dukanta, tatashi tana kuka sosai tana bashi hakuri, yana binta da duka tanayin baya har sukaje bangon falon ta tsugunna aqasa tana kuka sosai, cikin hucin bacin rai yace “ke Dan uwarki nizaki renawa hankali eh ? Okey wato saboda na sakar miki fuska acikin gidannan kina abinda kikaga dama shine zaki nemi ki takurawa rayuwa ta ko?, to bari kiji duk lokacin dana sake ajiye kayana cikin fridge tsautsayi yasa kika dauke min, saikin yabawa aya zaqin ta “
Yayi wulli da belt din awajan ya koma dakinsa, Dida kuwa kanta yana cikin qafafunta tana kuka, Dagowa tayi ta kalli jikinta, gefen hannunta harya shata
(Allah karabamu da mazaje masu dukan iyalinsu ????????)
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Nihla karatu yayi nisa, alhmdlh tafara kwantar da hankalinta, saide damuwarta daya ya Abba, yana nan daram acikin ranta, amma alqawarin data daukar wa kanta yana nan Babu shi Babu ita,fatanta daya tasamu miji nagari Wanda zai nuna mata soyaiyar dazatasa ta Manta da Abba kwata-kwata, tana fatan samun wannan mijin
Gefe daya kuma shaquwa Mai qarfi tashiga tsakaninta da abdallah, kullum suna tare, tana karatun ta cikin kwanciyar hankali, abdallah yazame mata tamkar aboki, gashi yanada abin dariya, idan suna tare dole nema saiya bata dariya, shiyasa take ganinsa Kamar qawanta, gashi duk abinda bata ganeba yana temaka sosai harsai tagane, fatarta kadai zaka kalla a yanzu kasan cewa lalle tasamu canji, Anty Nadiya tayi mata komai a rayuwa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan tagama gasa jikinta tabawa megadi kudi yasiyo mata magani tasha sannan ta kwanta, amma hawaye take sharewa, kanta har ciwo yake saboda kuka, yakamata tabarwa yaya Fawaz gidansa, Tun ranar da aka kawota gidan nan tafara cin karo da mari, to tunda yafara duka bazai dainaba gara tafara tunanin barin gidan Tun wuri,kuma yazo ya kwanta a jikinta yace itace, bayan duka ga sharri, inaaaa! Da sake
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau agajiye yadawo gida,gashi ya Manta bai siyo abinci ba awaje, tsaki yasaki yafara qwala mata kira “Ilham”
Daga kitchen tafuto, ya kalleta daga ita sai wata qaramar riga da bata wuce gwiwarta ba
Ya Girgiza kai, yarinyar nan bazata dena halin ta ba, batada kunya, batasan shigar kamala ????
Yace “jeki kawomin abinci”
Babu musu tajuya takoma kitchen, Aslam yabita da kallan mamaki, yau shine yace wa Ilham tabashi abinci Babu musu Babu rashin kunya tajuya zata kawo masa? Lalle yau za’ayi ruwa da qanqara
Ilham kuwa tana shiga kitchen tazuba masa Abincin, sannan tad’ebo gishiri Mai uban yawa tazuba masa aciki, tasa spoon ta jujjuya Sanna tadauko takawo masa, zuciyarsa daya yadebi Abincin yakai bakinsa, lokaci daya ya yatsina fuska, gaba daya gishiri yahade masa baki, daqyar ya iya hadiyewa, yadauko Abincin yakawo mata gabanta ya ajiye, tadago kai ta kalleshi dariya ta nasan kamata, cikin fishi yace “Ashe ke zero ce bansaniba?”
Ran Ilham yabaci, ita ya Aslam zai kalla yace mata zero? Itama cikin bacin rai tace masa “To sannu 1”
Tas kakeji yadauketa da mari, yace “Ilham idan kinaji da rashin kunyar ki kiyi abinki ke kadai, tayaya Zan kashe kudi na kawo miki abinci gida na ajiye, banda damar dazaki dafamin, Sannan yanzu nace kikawo min abinci zaki zuba min gishiri aciki?to gashinan zauna tas saikin cinye shi”
Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu tashare tana magana cikin kuka “Allah bazanci Abincin nanba”
Yace “nikuma kika sakamin naci namutu, baki damuba, zauna saikin cinye Abincin nan”
Haka Ilham tasa hannu acikin Abincin nan tanaci tana hawaye, fakar idonsa tayi tatafi dakinta dagudu tana kuka, Kallanta yayi yafara fada cikin ransa, haba yarinya sai Jan magana da rashin kunya, in banda yana mata kallan qanwar budurwarsa yau dasai ta cinye Abincin nan tas
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Futowa tayi tatafi dakinsa kanta tsaye, shi kansa yayi mamakin ganinta a dakin, saboda ba kulashi takeba, agefen gadon tazauna “yaya Adam inason kudi zanyi amfani dashi, banda kudi”
Kallanta yayi yace “banda shi”
“yanzu yaya Adam kaine zakace bakada kudi? Idan ban tambayeka kudi ba wazan tambaya?”
Yace “Allah masani”
Tace “Ok to sata zanje inyi insamu kenan?”
Yace “maryam koma menene kije kiyi, amma nide bazan dauki kudina nabaki kitafi yawon banza ba, kokuma kisa kati ki kira samari, qarya haram!”
“Ok haka kace?”
“yes haka nace maryam, kije kiyi duk abinda kikaga dama”
Tashi tayi tafuto tabar masa dakinsa
Tunani tafara maranta ciwo yake, A’ina zata samu kudin dazata siyo pad, shikuma besiyo mataba sannan yahanata kudin, haka takoma daki ta kwanta ga ciwo da takeji sosai, Tun tanaji kadan-kadan harta faraji dayawa, daga qarshe ma zazzabi me zafi Yarufe ta
Washe gari dasafe ya shirya zai tafi makaranta saboda yanada lacture, yayi kyau sosai cikin farin yadi sai qamshi yake
Har zai shiga Mota ya tuna yarinyar nanfa Tun jiya beji motsinta ba, Dan haka ya koma ciki kai tsaye yashiga dakinta, tozali yayi da ita akan gado tana cikin blanket amma karkarwar sanyi take
Cikin sauri ya qarasa wajanta yace “subhanallah… Maryam!”
Bargon ya janye saiga Diyana tana kuka sosai, yace “bakida lafiya ne?”
Bata iya bashi amsa ba sai kuka, dagota yayi yatasheta zaune sai riyamm tafada jikinsa, kanta yana kan qirjinsa amma tana iya jiyo bugun zuciyarsa,wannan shine karo na farko da mace tahada jiki dashi, sai yaji abin wani iri, goshinta ya shafa yaji zafi sosai, lokaci daya yashiga damuwa, yace “Sannu, sannu kinji, bari nahada miki ruwa kiyi wanka sai Muje asbiti”
Dagota yafara yi daga jikin sa amma taqi tashi, ya sassauta muryar sa cikin sigar lallashi yace “kiyi hakuri, zaki denajin zazzabin insha Allah, kinji ko?”
Ahankali ya maida ta ya kwantar da ita, Sannan yashige toilet dinta yahada mata ruwa, yadawo yakamata zai tasheta, ta miqe kenan taji zuciyarta tana tashi, lokaci daya taji amai, cikin sauri zata shige toilet yatareta zai kamata suje, aikuwa sai amai ajikinsa, farar rigar yadin daya saka ya kalla, gaba daya tabata su da amai, tayi tunanin zataji Saukar duka, amma abin mamaki sai yace mata “Sannu, sannu kinji,”