DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Daga masa kai tayi, yadaga hannunsa ya cire rigar jikinsa, yadawo daga vest sai dogon wandon jikinsa
Kamata yayi suka shige toilet din, sannan yafuto yabarta aciki, dakin ya gyara tsaf, yasake gyara mata gadon, sannan yabude kayan ta yana dubawa kozaiga Mai Dan sauqin sakawa, amma gaba daya da riga da wanduna yayi ar’ba
Wata atamfa yagani yajanyota, ya ajiye mata akan gadon, shikuma ya juya ya koma dakinsa yasake shirya wa sannan yadawo dakin nata
Bude toilet din tayi tafuto, taganshi yasaka qananun kaya, cikin ranta tace ashe yana saka qananun kaya,kayan kuwa sun karbi jikinsa, Kallanta yayi sau daya yakawar da kansa cikin sauri, yace “ga kaya nan kisa, saimu tafi asbiti yanzu”
Yadauki wayarsa yayi kira “hello monitor ki fadawa kowa cewa bazan samu damar zuwaba, matata batajin dadi”
Dasauri Diyana ta kalleshi, yanzu saboda ita yaya Adam zai fasa zuwa wajan aikinsa?
Fita zaiyi daga dakin tace “ya Adam”
Juyowa yayi Bece da ita komai ba tace “banda pad, kuma inaso zanyi amfani dashi”
“idan mun fita sai asiyo” yana fadar haka yafice daga dakin, yaga alamar Diyana batasan cewa bayasan ya zauna da ita Awannan halin datake ba, kokuma kallan dutse take masa waya sani, ita kuwa ko a jikinta
Kalau ta shirya suka tafi asbitin aka dubata aka bata magunguna Sannan sukaje suka siyo pad din, suka dawo gida
A sauqaqe yadafa mata indomie da dafaffan qwai ????saboda bazai iya soyawa ba, yadoro spoon akai tareda gorar ruwa, sai ganinsa tayi yashigo dakin da abinci, karon farko da taji Tausayinsa ya kamata, meyasa take masa Wulaqanci? Tabbas sai kana jinya zaka zaka gane masoyinka na gaskiya
Zama yayi akusa da’ita, yace “maryam tashi kici abinci kisha magani saiki kwanta”
Ahankali tatashi tasa hannu zata karbi flet din, yace “A a, ai naga jikin naki Babu qarfi, kibari nabaki”
Ta Girgiza kanta tace “zan’iya ci ya Adam”
“maryam banason musu fa”
Shiru tayi, takasa yimasa gardama, ahankali ya matsa kusada ita har jikinshi na gugar nata, yafara bata indomie din abaki, saida yaga ta qoshi sannan yabata maganin tasha, yace “ki kwanta kihuta, Allah yasawaqe”
Tace “amin” idonta akansa, tashi yayi daga kan gadon Yazauna akan bedside drower yayi shiru, itama haka Babu me magana acikinsu, saide cikin ranta tabbas ta Jinjina wa ya Adam, saika zauna da mutum sannan zakasan halinsa ????
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe ya shirya yabi jirgi zuwa Abuja, yakamata yaude yaje yaga Nadiya yaji A’ina suka tsaya akan maganar aurensu, yanaso kawai yaturo iyayen sa agama maganar komai
Baisha wahala ba daga Airport kai tsaye wani abokinsa dayake tuqin jirgi amma bangaren state, yadauko shi a motarsa suka qaraso gidan nasu Nadiya,akofar gidan sukai Parking ,suka futo daga cikin motar yakira wayarta nan take tashiga
Tana dauka cikin muryar sa Mai cikeda aji yace “Nadiya gani agidan ku”
Cikin mamaki tace “gidanmu kuma?”
“eh, nazo ne muyi magana dake Mai muhimmanci, koda yaushe kina tambayata yaushe zanzo yaushe zanzo, banda lokacin ki, banida kirki, to yaude gani”
Tace “ayya, gashi kuma wallahi bana nan, naje lagos gidan Antynmu, munata shirin biki”
Be tambayeta bikin waba, sannan Beyi tunanin komai ba yace “okey, to shikkenan idan kindawo saiki sanar Dani, lokacin dana samu dama sainazo, but yanzu Zan turo miki 50k sai kiyi anko dashi”
Tace “to shikkenan Sadiq nagode”
Suna ajiye waya yatura mata kudin, sannan yadubi abokinsa yace “kaji batanan taje lagos, next time kawai”
Maigadi yaji dirin Mota abakin get kuma yaji shiru baiji ance yabudeba, Dan haka ya leqo, yana futowa yaga su Abba, nan take yagane shi
Cikin farin ciki yace “a a yallabai ashe kune kuke tafe, toku qaraso ciki mana”
Abba yace “A a sammani kada kadamu, ai munyi magana da ita ma yanzu tace taje lagos ko?”
Sammani maigadi yace “eh wannan gaskiya ne yallabai, ya hakuri kuma?”
Cikin mamaki Abba yace “wanne irin haquri kenan sammani?”
Yace “to yallabai Wanda yarasa mace Kamar Nadiya ai yayi Babban rashi dole a jajanta masa, ai lagos din data tafima sunje hado kayan lefenta ne itada mijinda zata aura ????,
bikinma yanzu haka saura sati uku” ????????♀️
Lokaci daya kansa yasara, cikin tsananin mamaki yace “sammani me kace?”
Sammani maigadi yace” wallahi gaskiyar kenan yallabai “
Lokaci daya yafara karanta kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju’un abaiyane, da abokinsa da sammani maigadi basu zataba kawai sai ganin Abba sukai aqasa????????♀️
Cikin sauri sukayi kansa suna kira, abokinsa yana cewa “Abba! Abba!!”
Shikuwa sammani yana kira “yallabai! Innalillahi…”
Daqyar suka cacimeshi suka saka amota, sannan abokin yaja cikin sauri, sukabar kofar gidan
Asbiti yakaishi, anan doctor yake tabbatar wa da abokin cewa kawai yaji abinda ya razanashi ne shiyasa ya suma, allura akayi masa, ba’a dauki lokaci Mai tsawo ba yafarka, amma yakasa cewa komai, abokin nasa yabashi hakuri, amma Abba bai iya cewa komai ba, daga qarshe ma tashi yayi ya cewa abokin yagode amma yanaso yabar garin yanzun nan, duk yanda abokin yaso hanashi tafiya abin ya gagara, dole sai Airport yakaishi yabi jirgin dazai tashi zuwa kano
Ikon Allah ne kawai yakai Abba gida, Momy tana zaune afalo sai ganin shigowar Abba tayi yana tafiya yana layi Kamar d’an maye, baima kalli Inda takeba yashige dakinsa da alama baima lura da’itaba
Fadawa yayi akan gadonsa, Baqin ciki yazame masa goma da ashirin, kenan kudin ankon aurenta yatura mata? ????
Lokaci daya yaji hawaye yana zubo masa, ga wani zazzabi dayakeji me mugun zafi, blanket dinsa yaja yashige ciki yana kuka, tabbas Nadiya taci amanar soyaiya
Momy taturo kofar dakin tashigo, ganinsa cikin bargo yasa ta qarasa da sauri tazauna a gefensa tace “subhanallah… Abba na lafiyarka kuwa?”
Dasauri yatashi yadora kansa a cinyar Momy cikin kuka yace “Momy Dan Allah kiyi hakuri, kuyafemin keda Daddy, bazan sake ba Momy”
Gaban Momy yafadi, bafa qaramin abu ne yakesa Abba kuka ba, anya kuwa kalau yake? Cikin tashin hankali tace “Abba meyake faruwa ne? Me kayi kake bada hakuri? Kayimin bayani”
Kuka yake harda Jan zuciya, yakasa fadawa Momy abinda yake faruwa, tayaya zai fada mata cewa yarinyar dayaso bijire musu, yaso Yaqi yi musu biyaiya akanta ta yaudareshi zata auri wani? Tayaya?dole ne yanemi yafiyar iyayen sa akan qin biyaiya dayaso ya musu
Momy tace “to shikkenan bari nafadawa Daddynka tunda ni bazaka fadamin ba”
Nan take takira Daddy, yana dauka tace “Alhaji takwaranka fa Babu lafiya, gashinan yazo yanata kuka wai nayi hakuri”
Daddy yace gashinan zuwa, Momy ta kalli Abba taga ko alamar dena kuka bayayi tace “to inaga addu’ah zanyi ma Abba, meyiwa gamo kayi” ????
Alokacin Daddy yashigo dakin, Abba yana jin shigowar Daddy yace “Daddy Dan Allah kayi hakuri, natuba Daddy wallahi bazan sakeba”
{Allah sarki Abba,????Dani kabawa kudin ankon ma wallahi ???? ????}
El Yaqoub ✍️
[6/24, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to DANGI DAYA GROUP ????
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
25&26
Daddy yadubi Abba yace “yanzu Abubakar da girman ka kasamu agaba kana kuka kamar mace!, sannan mun tambayeka abinda yake damunka kayi shiru, sai hakuri kake bamu, to hakuri akan me?”