DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

damuwa ce ta baiyana a fuskar matar, Dan haka tace” Nihla Anty kuma? Momy zakice kinji ko? “

d’aga mata kai tayi, ta zauna awajan tareda cire d’an qaramin hijabinta, doguwar sumar kanta ta baiyana, Diddi tasake Kallanta tace” A’ina kika tsaya? Kintsaya kad’ar tsamiya ko? “

Tace” a a Diddi, qara nakai wata yarinya wajan malamin mu, kullum saita dinga tsokanata tana cemin ‘yarme fad’in gira “????
Daria sukasa gaba dayansu harda yaran dasuke tsaye suna buga ball, amma shi Wanda yake zaune agefen Diddi ko murmushi baiyi ba bare dariya

Diddi tace” to Allah ya kyauta, aisaikiyi haquri, wataran zata daina tsokanar ki”

Mazan dasuke ball ne suka fara musu atsakaninsu, momy tace, “Farouq, Usman, Aliyu, kudena mana, banasan shirme “

Ta kalli diddi tace “shiyasa fa banasan tafiya da maza wallahi”

Daria Diddi tayi tace “toya zakiyi tunda mazan Allah yabaki?”

Dena buga ball din sukayi, suka dawo cikin rumfar, suka zauna Nihla tabisu da kallo, dukansu farare ne Kamar ita, Wanda ke kusa da Diddi ne kadai wankan tarwad’a, bekaisu haske ba

Momy ta dubesu tace “Usman ga qanwar ku Nihla,”

Cikin wasa Farouq yace “taso nakoya miki ball my sister”
Daria kawai Nihla tayi batace masa komai ba

Momy ta kalli na gefen Diddi tace “ABBA, bakaga Nihla bane?qanwarka cefa, yarinyar Diddinka”

Sai a lokacin yakai Kallansa gareta, sau daya yakalli fuskarta, duk a tunanin su ita yake kallo, amma azahiri ba fuskar tata yake kallo ba, hankalinsa yana kan dogon gashinta, ahankali Kamar me koyon magana yace “na gan ta”

Dan Baqin ciki Momy ko kulashi batayi ba, ta dubi Diddi tace “nikam Aisha anan wajan ku Babu malamai ne masu addu’ah, irin masu roqon Allah d’innan?”

Cikin mamaki Diddi tace “malamai kuma anty Rahma? Me zakiyi awajan malamai?”

Momy tace “zuwa zanyi nayi musu bayani su temaka su tayani da Addu’ah akan Abba,???? inma rubutu ne suyi masa saiya dinga sha, Aisha idan Abba Yazauna awaje bazakiji maganarsa ba, idan ma zaiyi magana saide kiji yanayi daqyar Kamar anyi masa dole kokuma wani d’an sarki, bayan Babu Inda muka had’a dangi da sarauta, idan kinga Abba yazage yana miki surutu da Fara’ah to yaga jirgin sama ne, shi ala dole yanaso yazama matuqin jirgin sama”

D
A-Abba
N-Nihla
G
I
D
A
Y
A

FAN’S ya bayan saduwa?????
please ta hanyar Comments d’inku ne zaisa nagane cewa labarin ya karbu, harma inci gaba da turowa ????????

Amnah El Yaqoub ✍????[6/13, 11:26 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

3&4

Murmushi Diddi tayi “haba dai Anty Rahma, basai kinje wajan kowaba, kiyi hakuri kibarshi yanda yake, kinsan kowa da irin yanayin sa, haka Allah yayishi, hakan ai kwarjini yake qara masa, mazantakar kenan, yanzu kinga Nihla idan tafara zuba miki surutu saikin gaji, kowa da irin yanayin sa “

Momy tace” to shikkenan Aisha tunda haka kikace, Allah yaqara shirya mana zuria “

Tace” Amin Anty Rahma “

Hankalinta ta maida kan Nihla tace”ke tashi kije kicire kayanki kiyi sallah saikizo kici abinci “

Tace “to Diddi” sannan tatashi tayi cikin d’akin datake kwana aciki, anan taci karo da kayan abinci da katan katan d’in lemuka, lokaci d’aya wani farin ciki yakamata, saida taje ta tattaba su sannan tafara cire kayan nata

Usman Wanda shine babba acikinsu yakalli Diddi yace “Amma Diddi idan zamu tafi tareda Nihla zamu tafi ko, saiki bawa Momy ita”

Shima Aliyu Wanda yake binsa yace “eh wallahi, kinga bamuda qanwa mace, mu kadai ne, Diddi kibamu ita Dan Allah”

Abba yakalli Usman harya gama magana, Aliyu ma yana farawa yasake maida kallansa kan Aliyu, saikuma farouq Wanda yake bin Aliyu yace “Diddi, idan kika bamu ita kinga tazama qanwar mu, komai mune zamu dinga yimata, munasan Baby amma Babu agidan mu, saisu dinga tafiya makaranta itada Abba”

Momy ta kalli Abba dayakebin yayun nasa da kallo tace “Abba nah bakace komai ba, kanaji duk brothers d’inka sunyi magana, kaima kanaso abamu Nihla saiku dinga wasa tare ko?”

Ataqaice yace mata “Eh”

Girgiza kanta tayi sannan ta kalli Diddi tace “Aisha, kinsan lokacin bikina da yayanki, duk yaran nan da hankalin ki aka haifesu, Tun kafin Allah yabani haihuwa nakeso Allah yasa nahaifi mace, amma Allah da ikonsa bai baniba, saide maza, Aisha Dan Allah kibani Nihla wallahi inason yarinyar sosai, bazan iya kwatanta miki yanda nake santaba, “

Daria Diddi tayi”yanzu Anty Rahma banda rigimarku idan na baku ita nikuma fa?”

Cikin sauri momy tace ” Sai Allah yabaki wata, may be ke Allah yayi mata zaki dinga haifa shikuma yayanki maza”

“A a Anty Rahma, kuyi hakuri amma bazan iya baku ba, ‘yar tawa ita kad’ai jal Zan dauka naqara miki, sun zama su biyar fa kenan, nikuma Babu ko daya”

“idan kika bani ita saikiga Allah yabaki wata”

“Anty Rahma, Allah hakuri zakuyi, amma kyauta kacokam, inaaa”

Cikin sanyin jiki Momy tace “to shikkenan Aisha, Tun farkoma dana sani Mai hakuri na yiwa maganar ba keba, nasan shi bazai min musu ba,”

Diddi tace “zata dinga zuwa muku hutu dai, shima ai yayi”

Momy tace “Aisha irin wannan soyaiya idan zakiyi auren ta yaya zaki yi?”

“ni kaina bansaniba Anty Rahma, amma banason rabuwa da ‘yata”

Murmushi kawai momy tayi, tana Jinjina irin wannan qauna da Diddi takeyiwa Nihla, saide anata bangaren kawai jinta take,banda de itace ta haifi Nihla dazata iya cewa duk duniya banda ita Babu Wanda yakai ta son yarinyar, jitake Kamar ta d’auketa gaba daya

Diddi ta dubeta tace “Anty Rahma ban tambayekiba, yaya labarin matar yaya Basiru kuwa? Tasauya ko halin ta yana nan?”

Ajiyar zuciya tayi “Aisha ai wannan baiwar Allah halin ta bazai sauya ba sai wani ikon Allah, gaba d’ayafa nema take ta lalata tarbiyar yaranta, shi Fawaz nema yakema yafi qarfin iyayen, abokan banza yake kulawa, idan su Abba zasu tafi school bayason binsu sai anyi da gaske,gaba d’aya sunansa yabace, idan zaki wuni kina cewa fawaz bazai amsaba, saide gaye ????, ita kuma Aysha takwararki tace bazata sake zuwa makaranta ba saide afitar da’ita qasar waje, Acan zatayi????, ita kuma qanwarta Ilham tana nan tana zuba rashin kunya, bata barwa kowaba, yara qanana sai rashin kunya “

“Amma yaya Basiru yana gani yazuba musu ido yana kallan su?”

“to yaya zai musu Aisha?????Kinsan hali dai, dama yayanki ne Mai tsawatarwa, to shima yayi shiru yazuba musu ido, yace lokacin dazaiyi auren ai baiyi shawara dashiba”

“to ina Diyana da Dida, su Aslam da Adam?”

Momy tace “wallahi kowa yana lafiya,”

Haka sukaci gaba da firarsu, Diddi tana Tambayar Momy labarin gida, ita kuma tana fada mata, har yamma tayi liss
Diddi ta dubi Nihla data baje kayan wasan ‘yar tsana tanayi tace “Nihla tashi kidauki nera hamsin agefen katifar nan kije shagon bashari kisiyo omo naduka”

Tace “to Diddi”
Sannan ta kalli Abba daya zubawa kayan wasan nata ido tace masa “zakaje?”

Girgiza mata kai yayi, alamun bazashi ba, saida ta harareshi sannan tace “karkaje d’in” ????
Ta d’auki kud’in tayi ficewarta

Momy tayi daria tace”walllahi kuwa,yasha zamansa kema kin huta abinki, “

Ta kalli Abba tace” kaide akan wannan halin naka na miskilanci bakada ranar samun matar aure, Dan babu wacce zata soka ahaka “

Diddi tace” Haba Anty Rahma, meyasa kike fad’ar haka, tayaya zai rasa matar aure? Abba nefa, ABUBAKAR SADIQ, me sunan mahaifina sannan kuma me sunan yayana, nida kaina Zan samo masa matar dazai aura muna nan dake “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button