DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Shiru Abba yayi Bece dasu komai ba, shi ya’isa yafada musu gaskiya? Ai kaf family dinnan sai sunyi masa dariya wasu ma suce Allah yaqara
Dan haka yayi shiru yaqyalesu
Momy tace” Alhaji Abba fa ba magana zaiyi ba, nikam kaga tafiya ta “tasa hannu tadauke kan Abba dayake cinyarta tafuto daga dakin ????
Shima Daddy yace” to ai shikkenan tunda haka kazaba “
Yafuto daga dakin, yaje wajan Momy yace”ko menene yake damunsa? Amma miskikanci ya hanashi magana?”
Momy tayi Murmushi tace “to awajan wa yadauko halin”
Shima murmushi kawai yayi, yashige dakinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tun bayan dukan dayayi mata ta tattara shi ta watsar, gaba daya tadena shiga sabgarsa, idan taji yashigo gidan ma tana falo cikin sauri take shigewa dakinta Tun kafin yashigo falon, abinci kuwa zatayi tabarshi anan, idan yaci shikkenan idan baici ba kansa yayiwa itade tasan cewa batada haqqin kowa akanta, koda rasuwa tayi tasan tafita haqqin sa saide nata haqqin dayake kansa
Tunanin abin datasa aranta yasa duk tafara ramewa, idanunta duk sun futo
Yauma shi kadai ne azaune afalon, Tun safe baije ko’inaba amma baiga futowarta ba, Kamar wasa saigata tafuto daga daki zataje kitchen, ta kalleshi ta watsar ko gaisuwa Babu, taje ta dauko ruwa tasake komawa dakin
Shikuwa Fawaz Yana binta da ido kawai
Yayi ajiyar zuciya yatashi yabita cikin dakin, yaune karon farko daya taba shigowa dakinnata, yanemi waje Yazauna yana Kallanta tanashan ruwa, saida tagama sannan yace “meyake damunki kika lalace haka?”
Shiru tayi masa, Dan renin hankali kawai, yagama dukanta yadawo yana Tambayar me yake damunta, idanunta sukai rau-rau zatayi kuka
Sassauta murya yayi yace “bazaki fadamin ba?”
Duk yanda Dida taso boye hawayen ta saida suka zubo, tasa hannu tashare tace “banasan abinda kake aikatawa ya Fawaz, kana dukana, kanashan kayan maye, nikuma banaso”
Tana qarasawa tasake fashewa da kuka
Fawaz yayi shiru yana tunani, Wato yau sabodashi ake kuka, yau saboda andamu da abinda yake aikatawa ake kuka yadena,nan take yarinyar tabashi tausayi
Kallanta yayi yace “to kiyi hakuri, dena kuka, insha Allah daga yau nadena”
Cikin mamaki ta kalleshi ido duk hawaye tace “da gaske?”
“yes da gaske nake”
“harda dukanma?”
Yasake cemata “nace miki nadena, kema saiki daina kukan ko? “
Aikuwa nan take tashare hawayen idonta
Yatashi tsaye yace “Zan fita, but banaso kina zaman dakinnan, kifuto falo ki zauna, kici Gaba da abinda kikeso kinji ko?”
Cikin murna Dida tace “to”
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda Diyana tafara rashin lafiya Adam yake kula da’ita, kokadan baya barin ta tayi aikin komai
Yauma shida kansa yakawo mata abinci har daki, ya tarar tana gyara dakin, yace “maryam ga abinci”
Tace “ya Adam aina warke ma, nagode sosai da temakon dakamin, yau nice yakamata nadafa ma Abincin” ????
Adam yayi Murmushi yace “nagode, amma ba yanzu ba,kici Abincin kishirya zamuje gida”
Cikin farin ciki Diyana ta rungumeshi tace “yawwa nagode ya Adam”
Cak jijiyoyin jikin Adam suka tsaya, yarinyar nanfa kada tasa yakasa aiwatar da abinda yayi niyya, cikin wata irin slow voice yace “Diyanaaah” yaja sunan nata
Ahankali tadago daga jikinsa ta kalleshi yaune karon farko data tabaji yakirata da wannan sunan, koda yaushe maryam yake cewa, gashi yanda yakira sunan nata ma kadai ya’isa yasaka mutum cikin wani hali, ya’iya kiran sunan, tana gama wannan tunanin tayi fari da idonta tace “na’am”
Yace “kije kishirya mana, university nakesan wucewa daga gidan”
Murmushi tayi tace “to”
Sannan tasakeshi tashige toilet
Sai a lokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya sannan yafuto daga dakin yadawo falo, abinda yake shirin yi shine daidai, dole zai nunawa Diyana kuskurenta, idan akaci gaba da zama ahaka to akwai matsala
Bata dauki Tsawon lokaci ba tafuto, ko hijabi bata sakaba kawai wani yalulun mayafi tayafa suka futo, shima Bece da ita komai ba, suna tafiya ahanya yana driving qira’ah tana tashi acikin motar
Har sukazo bakin get din gidan nasu Babu Wanda yace da dan’uwansa komai, amma Diyana tunanin Adam ne fal acikin zuciyarta, ashe haka yake da kirki? Babu ruwansa duk abinda take masa ko ajikinsa
Tsayawa ya kalleta yace “kishiga ciki, nizan wuce makaranta”
Cikin mamaki ta kalleshi tace “Kamar ya nashiga ciki, kai bazaka shigo ku gaisa ba?”
Fuskarsa Babu alamun wasa yace “kema ba gaisuwa nakawoki ba, gaba daya nadawo dake gida, kije saina nemeki”
Gaban Diyana yafadi, cikin rawar murya tace “ya.. ya.. Adam”
Cikin tsawa yace “yes abinda kikaji hakane, Maryam kitashi kifice min daga Mota kitafi gida saina nemeki”
Wani irin kuka ne yazo mata, Dasauri tabude motar tafuto da gudu tana kuka tayi cikin gidan
Kansa yadora akan sitiyarin motar idonsa yayi jajir, cikin kwana kin nan datayi batada lafiya tabbas yasan cewa yakamu dason yarinyar, saide bazai taba nuna mata hakanba, saita gane kuskuren data aikata abaya, shi aure ko wanne iri ne ba abin wasa bane
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Damuwa tayi masa yawa, gashi abin acikin ransa yarasa wazai fadawa yaji dadi aransa
Wayarsa ya janyo yakira Aslam “hello Aslam idan kasamu lokaci kazo gida inason ganinka, banda lafiya wallahi” ????
Aslam yace “subhanallah, to gani nan zuwa Abba”
Dama yana kan hanyar zuwa gida ne, Dan haka ya juya kan motarsa zuwa family house dinsu
Kai tsaye part dinsu Abba yaje, suka gaisa da Momy yashige dakin nasa
Akwance ya ganshi yana danna waya Yazauna yace “Abba da alama ka warke, tunda gashi wayace a hannunka”
Ajiye wayar yayi bayan yagama goge pictures din Nadiya da numbers dinta ????
Yace “banasan tunani yamin yawa ne”
Aslam yace” menene yake damunka? “
Abba shiru yana tunani, kode yafadawa Aslam ne? Kaiii wallahi Aslam ma sai yafi kowa yimasa dariya, Dan haka yace” kawai banajin dadin jikina ne “
” to Abba kaima kayi aure kaqi, ka zauna agaban Momy tuzuru dakai “????
” Aslam bana tunanin yin aure yanzu “????????????♀️
“meyasa?” inji Aslam
Abba yace “haka nan, banda ra’ayin auren yanzu” ????
Ajiyar zuciya Aslam yayi “to shikkenan Allah yakaimu lokacin, daga campany nakefa kakirani, mungama tattara list din ma’aikatan da za’a dauka, yanzu kawai ina jiran kiran wayarsu ne, sunce zasu saka mana date din dasuke ganin shine yadace da bude campanyn, wallahi Abba banasan komawa gida, Ilham tacika rigima, yarinyar nan jiya gishiri tazuba min acikin abinci na, batajin magana “
Ran Abba yabaci ” meyasa zaka tsaya yarinya ta raina ka haka Aslam? “
Aslam yace” to Abba ba dole raini yashiga tsakanin muba, tunda taga tashigo dakina taganni haka “
Murmushi Abba yayi yace ” Aslam ni aganina zancen boye boye yaqare atsakaninku, why not ka koya mata hankali sau daya, daga ranar zata dinga yima biyaiya, shikkenan anwuce wajan “
Dariya Aslam yayi yace” kai Abba, akwai shawara, toshknn Zan wuce gida, inaso nahuta kafin Baqin sukira wayata “
” to Aslam “
Aslam yafuto yatafi gida yana mamakin yanda suka shaqu da Abba, kowa yana fadawa kowa damuwar sa, gashi de bayasan magana amma inde da Aslam ne tofa zakaji maganar sa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da gudu ta qaraso part din nasu, cikin kuka tafada jikin mahaifiyarta tace “Mom ya Adam ya tsaneni”
Hajiya Farida ta dagota tace “ke kiyi shiru kimin bayani, meyake faruwa?”
Hawaye ta share tace “Mom cewa yayi natafi gida saiya nemeni, Allah Mom bazan zauna ba”