DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Mamy tayiwa sallama tatafi gidansu Nadiya, tana zuwa taganta da kayaiyaki agaba, itada mamanta suna dubawa, mamanta ta kalli Nihla tace “to Ga kayan lefe de sun qaraso, Nihla zauna ki gani kema”
Tatashi tafita, tabar musu dakin
Jikin Nihla yayi sanyi, ta kalli Nadiya “Anty Nadiya meyasa zakiqi aurensa?”
Cikin rashin damuwa Nadiya tace “kekam Nihla narasa irin zuciyarki, kin damu dayawa akan naqi auren Sadiq Mazawaje, saikace wani dan’uwanki?” ????
“ba haka bane Anty Nadiya, akwai tausayi dayawa, yana sonki sosai”
Nadiya tace “ya akai kika sani?”
“kawai alama nagani Anty Nadiya, amma Allah yabaku zaman lafiya”
Nadiya tace “yawwa qanwata haka nakeso naji, shawarar me kike nema?”
Nihla tabawa Nadiya wayarta tace “kinga abinda yaya Yusif yaturomin, harda kudi ra dubu talatin, Anty Nadiya kudin sunyi yawa me zanyi da kudi har dubu talatin?”
Nadiya tagama karanta text din duka tayi Murmushi tace “ai Nihla bakya buqatar shawara anan, kai tsaye ki amince, kina zaune lafiya da iyayen sa, shi yana sonki, kawai kicire wannan Abban daga ranki kisa Yusif, sannan kina maganar dubu talatin nawa dubu talatin din take awajan ‘yan canji? Cemiki akai su suna jin kudi ne? Ki kwantar da hankalin ki kawai Nihla, kema ki tura masa cewa kin amince kuma kinga saqo kin gode “????
Cikin damuwa tace” Amma Anty Nadiya yaya Abba… “
Nadiya ta katseta” dan girman Allah Nihla ki rufamin Asiri da zancen Abban nan haba!!, tunda kika dawo Abuja da zama yataba nemanki ne? Inda ya damu dake zaizo har Inda kike ya nemeki”???? ????
Tace” to shikkenan, nagode, dama shine shawarar, whtspp nake budewa natafi gida “
Murmushi Nadiya tayi tace” to sai anjima “
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Hajiya Na’ila tana shigowa gidan kai tsaye dakin Ilham tashige, ta tarar da’ita tana kuka sosai, cikin sauri ta qarasa gadon tace “subhanallahi, yanzu ke Ilham jinyar kikewa kuka saikace qaramar yarinya? Um to Allah ya kyauta, Aslam yamin waya tashi ki shirya Muje asbiti”
Hawayen idonta tashare, idanun nan yayi jajir, tatashi ta sauko daga gadon tanufi wajan kayan ta tana tafiya tana bude qafa, hajiya Na’ila tana ganin haka tafahinci komai, kuma ga yarinya daga sai daurin kirji, yanzu dama yaran nan haka suke zaune wata da watanni? ????
Afili tace “Allah ya kyauta, Kinshiga Ruwan zafi ne?”
Kuka Ilham ta fashe dashi ganin hajiya ta fahimci abinda yafaru, wallahi ya Aslam ya cuceta, fasa saka kayan tayi takoma gadon tazauna tana kuka sosai
Hajiya Na’ila tace “yau naji ta’bara, wai ni Ilham akanki aka fara karbar budurci ne?”
Ilham tasake jin wata kunyar, hajiya Na’ila kuwa tashi tayi tafara duba mata kayan dazata saka da kanta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tafiya yake yana driving amma tunani fal ransa, gaskiyar magana dayasan haka aure yake, da tuni yasauke girman kai ya lallaba yarinyar nan, yasaki murmushi Ahankali yace bazan iya Manta wannan ranar ba, maganganunta ne suke dawo masa, Mugu, Azzalumi, sai Allah yasaka min, yayi ajiyar zuciya yace oh Ilham tadauki abinnan da zafi, tunani yafara ko tana lafiya yanzu? Ko mama taje? Zuciyarsa tayi nisa a tunani saiji yayi yaci karo dawata motar, lokaci daya motar tasa tai gefe tadaki wani gini, mutanan dasuke wajan suka fara salati, aka tafi da gudu domin kai masa dauki
Daqyar suka zaroshi daga cikin motar kwata kwata Babu alamun rai atare dashi, wani daga cikin su yabude wayarsa domin sanar da yan’gida halin da ake ciki
Hajiya Na’ila takamo hannun Ilham suna tafe daqyar, sai mita take tana cewa zata hadu da Aslam din ne
Wayar hannunta tayi qara, cikin sauri tace “yawwa gashi nanma”
Ta daga wayar tace “kai gashinan muna hanyar zuwa Asbitin”
Daga daya bangaren akace “hajiya bashi bane, me wannan wayar yasamu hatsari yanzu nan, Allah yayi masa rasuwa”
Gaban hajiya Na’ila yayanke yafadi, tace “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, hatsari!!, yanzu Aslam dinne yamutu?yana ina yanzu? Ina zanga dana?
Kwatancen asbitin da’aka kaishi yayi mata, sannan ya kashe wayar
Kuka hajiya tace” shikkenan, Aslam yatafi yabar dan’uwansa Adam, yatafi yabarmu, Ilham Aslam yamutu “
Jin maganar hajiya take wani iri haka, wai wanne yaya Aslam din ake nufi? Girgiza kai tafara” A a, a a Hajiya, ni mijina be mutu ba, Yaya Aslam bazai tafi yabarmu ba, Anty Aysha tarasu, kidena cemin ya Aslam yamutu hajiya, yana nan da ransa… Sulalewa tayi tafadi awajan, hajiya Na’ila ta dora hannu aka tana kuka
Alhaji Baqir tayiwa waya, a lokacin su suna Asbitin ma, Abba yaji labari ya sanar dasu, shine yazo da kansa yasaka Ilham din amota sannan suka dauki hanyar Asbitin
Suna hanya Ilham tafarka, amma takasa gaskata abinda hajiya tafada mata, kuka take sosai, Alhaji Baqir dakansa shine yake bata haquri, amma abanza.
Suna zuwa Asbitin sukaga iyayen nasu duk sunje, Abba yafi kowa shiga tashin hankali, dazu-dazu Aslam yabar gidansu amma yanzu ace yana wannan halin,kwata-kwata yakasa zama sai zagaya wajan yake, Ilham tana ganin iyayen azaune tasake fashewa da kuka tafada jikin ummanta, Haushi yakama Abba, kasa boye bacin ransa yayi ya kalleta yace “koki rufewa mutane baki anan kokuma wanka miki mari yanzun nan, marar kunya kawai, koma menene bake kikaja ba?”
Alhaji Baqir mahaifin Aslam din yace “Abba! Kayi hakuri mana”
Likata ne yafuto daga dakin da aka kai Aslam din, gaba dayansu suka nufeshi, yace “Am Alhaji ku kwantar da hankalin ku, be mutu ba, yana nan da ransa saide yasamu karaya a hannunsa saikuma ‘yan rauni dayaji, shima insha Allah zamuci gaba da bashi kulawa, zaku iya shiga ku ganshi amma Dan Allah banda surutu”
Ajiyar zuciya suka sauke gaba dayansu, domin kuwa dukansu kiransu akai awaya akace Aslam yamutu
Dakin suka shige, yana kwance yana bacci, ciwukan dayaji duk anyi masa aiki awajan, Ilham kam bataji kunyar kowaba tafada jikinsa tana kuka sosai, duk dakin Babu Wanda bata bawa tausayi ba
Haka suka wuni a asbitin, Ilham itace take masa komai duk da halin datake ciki itama, har Tsawon kwana biyar amma Aslam bai farka ba, Dafarko sun shiga damuwa, amma likitoci suka tabbatar musu da cewa Babu damuwa zai iya farkawa a kowanne lokaci, hakan ne, yasa hankalinsu yadan kwanta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Kwance take akan gadon dakinta da Daddare, tunani take akan irin amsar dazata bawa yaya Yusif dangane da message din daya turo mata Tsawon lokaci
Idanfa ta amincewa yaya Yusif hakan yana nufin tabbas zata iya auren sa ne, wata zuciyar tace to Wanda kike haukan akansa shi baya sonki, kawai gara ki amince koshi din zai nuna miki tsantsar soyaiyar dazata ki Manta da Abba
Afili ta furta “yaya Abba, duk kaine kasani cikin wannan halin”
Amsa ta turawa Yusif din cewa ta amince, sannan tayi addu’ah Allah ya tabbatar musu da alkhaairi a tsakanin su sannan kuma ubangiji yayi mata Zabi nagari bawai son zuciyarta ba
Momy ce tafado mata arai, Allah sarki Momy haqiqa tana tsananin sona, ko yaya take yanzu? Tana kewarta sosai
Afili ta furta “i’m sorry Baba”
Tadau wayarta tafara saka number Momy, kasancewar ta riqe number
Adede lokacin Momy tana falo azaune tareda yaranta gaba dayansu, Usman, Aliyu, farouq, dakuma oga kwata-kwata Abba ????
taga Sabuwar number na kiranta,cikin nutsuwa tayi picking tace “Salamu Alaikum”
Abangaren Nihla kuwa tunani tafara, da wanne suna zata kirata? Tasan cewa Babu abinda Anty takeso Kamar takirata da Momy, Dan haka cikin farin ciki tace “Momyyyyy, i miss you Momy nah”