DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Shiru Momy tayi, ko a mafarki taji wannan muryar bazata Manta da ita ba, cikin farin ciki tace “Nihla!!!”

Gaba dayansu hankalinsu yadawo kan Momy jin sunan data ambata, Abba kuwa haka kawai ya tsinci kansa cikin farin-ciki baisan dalili ba

Momy tace ” ‘yata Nihla ina kika shige? Idan nakira Mai hakuri saiya cemin kina lafiya, kina lafiya ko ‘yata?”

Murmushi tayi tace “ina nan lafiya Momy, karatu ne ya boyeni, baba ya maidani makaranta Momy, ina shirin gama level 1 ma”

Momy tace “Alhamdulillah, kice yata tazama yanmatan jami’ah, nasan yanzu samari suna nan buhu-buhu ko?”

Dariya tayi tace “um um Momy karatu na kawai nake, Momy ina Daddy da sauran yan gidan?”

“Daddynki yana nan kalau, yanzu ma yana masallaci Tun sallar ishsha’i bai dawoba, amma daya dawo Zan fada masa kin kira, sukuma yan gida dasu Dida kowa tana nan lafiya Nihla”

Tace “to Momy inasu yaya Usman?”

“Usman gashinan Nihla, duk yayunki sunzo yau suna tayani fira, ga farouq nan da Aliyu, dakuma yayanki Abba”

Gabanta ne yafadi jin an ambaci sunansa, amma saita share tace “Momy bawa yaya Usman wayar mugaisa”

Momy tabashi wayar tace “Usman ga qanwar ka tana magana”

Yana karba yace “da alama de wannan yar qauyen Dani takeyi yanzu, nine na gaban goshin, tunda nita fara nema”

Dariya tayi tace “ya Usman wallahi kamin tsufa yanzu, sai sabon jini”

Yace “aikuwa sainazo an goga Dani, yarinya tuni Zan daukeki daga Abujan nan kidawo kano”

Abba yakalli ya Usman yana mamaki, yaushe tatafi Abuja? Ya akayi besaniba? ????

Nihla kuwa dariya tayi tace “nide yanzu ya Usman Dan Allah bawa ya Aliyu mu gaisa”

Aliyu yabawa wayar, yace “qanwata yakike, dafatan kina lafiya”

“lafiya kalau ya Aliyu, yagida yayara”

Yace “duk suna lafiya,naji kincewa momynki kinkoma school to kidinga karatu sosai kinji ko? Banda kula samari”

“to ya Aliyu insha Allah nagode, ina ya farouq?”

Yace “farouq gashinan azaune yanaji Kamar ya qwace wayar” ????

Dariya tayi tace “to bashi”

Farouq na karbar wayar yace “Wato kin gudu kin barmu, kin lula birnin tarayya, to ki gama karatun kidawo, ina nan ina jiranki auren nan de yana jiranki sai andaura Dani” ????

Dariya tayi sosai tace “to yaya farouq aikai nawane, zan amince amma da sharadin makkah duk sati, yawon bude ido duk bayan wata daya” ????

Yace “inyeee wannan ai kora da hali ne, to bari kiji inde makkah ce saikin gaji, kullum Zan dinga kaiki, muda mukeda Pilot ai bakida matsala”

Sarai tagane Inda maganarsa ta dosa amma saita shareshi tace “to shikkenan, dakai din za’ayi, amma yanzu nide bawa Momy na waya zamuyi sallama”

Kai tsaye farouq yabawa Momy wayar, tana karba kuwa Nihla tayi mata saida safe akan wani lokacin zata sake kiranta, daga nan takashe wayar

Ba Momy kadai ba, hatta Usman, farouq, Aliyu saida mamaki yakama su, meyasa bata tambayi Abba ba? Ko bataji Momy tace suna tare ba?

Shikuwa jikinsa ne yayi sanyi, sai yaji murnar dayake takira waya duk tagushe, meyasa shi batace abata shiba? It means ta tsaneshi, batason jin voice dinsa

(kwana biyu zaku jini shiru, zanyi tafiya ne zuwa wajan wani biki, bazan samu damar typing ba, insha idan mungama zaku jini, nagode da soyaiyar dakuke min i luv u All ????????????)

(ko yaya batun Diyana da Adam?)

(Aslam yabude taro da addu’ah ????ko waye zai biyo baya Kuma? ???? )

Game buqatar wannan littafin daga farko zuwa Inda muka tsaya, ya nemi wannan number 09039066577

Sharhi

Comments

Share please ????

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/29, 11:18 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️

{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

Bayin Allah ya kwana biyu? Alhmdllh mungama biki lafiya, naji dadin yanda dayawa sukamin uzuri saboda sha’anin biki, masu yimin addu’ah nagode sosai, amarya tana godia.

Masu neman DANGI DAYA complt kuyi hakuri wallahi Nikaina banda shi complt a wajena, duk Wanda kukaga anyi muku posting dinsa arana, to wallahi aranar na rubutashi, ganda ma bazata barni narubuta cmplt lokaci dayaba

Masu tambaya sunason littafin gaba daya saboda sun matsu suga dramar Abba da Nihla suma suyi hakuri, sannu sannu bata hana zuwa, kuyi hakuri mu qarasa ahaka, bazai iyu na sauya tsarin labarin saboda Abba da Nihla ba, idan na sauya to komai zai iya lalace wa????

Sukuma masu cewa kona kudi ne sunaso nasiyar musu dashi complt to DANGI DAYA free ne, Tun farko nafada cewa idan labarin yamiki dadi kawai kimin addu’ah, Allah yabarmu tareda masoyan mu ameen????????

27&28

Karan farko dayaji wani Baqin ciki ya kamashi, Ahankali yatashi tsaye ya kalli Momy “Momy Am tired, zanje nahuta” yana fadar haka yayi gaba

Momy ta kalleshi tace “to Abba”

Bayan yashiga daki ya Usman yace “Momy ran Abba fa yabaci, Kamar kishi yake”

Aliyu shi dama Babu wasa, kai tsaye yace “basai yayi ba, shiyasa ko sallama baiyi manaba yayi daki”

Farouq yayi dariya ya dauki wayarsa yace “anayi ina daga gefe ina smiling”

Momy tace “a a shide Abba baice hakaba, ni farin ciki ma naga yanayi” ????

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Dawowar sa kenan daga yawonsa, yashigo falon da sallama, yaji shiru, kai tsaye dakinta yashiga, a lokacin tana kwance tana bacci, daga ita sai d’an qaramin siket under wear shitaja har sama, hakan yasa cinyoyinta suka baiyana, hankalin ta kwance tana bacci bataji shigowar sa ba, yadade a tsaye yana Kallanta, shi sai yau nema ya qarewa yarinyar kallo san ransa, tana yanayi da Diyana sosai, ahankali yataka yaje gaban gadon ya tsugunna yaja qarewa fuskarta kallo, saida yagama ganinta tsaf, sannan yakai hannunsa ya shafa kanta Ahankali, Allah ya temakeshi bata farkaba,Inda tafarka ta kamashi da yaya zaiyi? Shida yake cewa itace take liqe masa
Ahankali yatashi yafuto yayi cikin dakinsa

Zama yayi agefen gadon tareda yin tagumi hannu bibbiyu, babu abinda yake masifar son yasha irin qwaya, gashi ya cewa wannan yarinyar yadena sha, amma a yanda yakeji yanzu idan bai shaba gaskiya akwai matsala, hannu yasa a aljihunsa yadauko su har guda biyu, yasha abinsa sosai yayi watsi da kwalaben anan, sannan ya kwanta yafara kokarin bacci, yasan cewa kafin ma tatashi daga bacci yatashi yayi wanka yafice

Dida kuwa ta dade tana bacci sannan tatashi tashige toilet tayi wanka, shaf ta shirya cikin atamfa dinkin riga da siket, tasan ya Fawaz bai dawoba Dan haka ta nufi kitchen domin dora musu abinda zasuci

Tafuto falon kenan zata shiga kitchen din taga kofar dakinsa abude, cikin mamaki tace “to lafiya?”

Dakin ta nufa tashiga kanta tsaye, ranta ne yayi mugun baci ganinsa kwance shame-shame yana bacci ga kwalaben kayan mayensa nan azube agefe, kenan sake sha yayi, haushi yaqara kamata, cikin takaici ta qarasa wajansa tana dukansa yatashi amma Fawaz ko gizau beyiba, awajan ta tsugunna ta dora kanta akan gadon setin kafafunsa tasaki wani irin kuka Mai cin rai, kuka take sosai tana tunanin Rayuwar ta, duk cikin ‘yan’uwanta da aka musu aure tare ko wacce tana zaune gidan mijinta lafiya amma banda ita, ya Fawaz kullum shaye-shaye, ga duka, dago idonta tayi ta harareshi Kamar yana ganinta,garama tatashi Tun kafin yatashi Yarufe ta dawani dukan, shaye-shayen ma yace ya daina gashinan Akwance bai daina ba, to dukanma tasan cewa bazai fasa ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button