DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Ahankali tatashi tafice daga dakin nasa, ko kallan kitchen din batayi ba tashige nata dakin tadauko mayafi da wayarta da jakar ta, tafuto daga gidan, saida ta kalli gidan hawaye yazubo mata sannan tasamu me napep tahau tayi masa kwatancen Inda zai kaita

Yana ajiyeta directly part dinsu tanufa, tana Jan jaka tana share hawaye
Hajiya Farida da Alhaji Habib suna zaune afalo suna tattaunawa akan maganar Diyana, kwata kwata Adam Yaqi zuwa gidanma bare ayi masa magana yadauketa su koma

Kawai sai ganin Dida sukai afalon tashigo tana kuka, gaban hajiya Farida yafadi, tace “nashiga uku Alhaji, meyake faruwa ne yara sai dawowa gida suke daya bayan daya?”

Kafin yabata amsa Dida ta qaraso dakin tazauna akan kujera tareda dora kanta akan cinyar uwar tana kuka sosai
Alhaji Habib yace “ke Dida, meyake faruwa? Kinshigo gida da jakar kayanki bakice mana komai ba”

Cikin kuka tace “Allah ni nagaji bazan koma ba”

“me yafaru?” cewar hajiya Farida

Dida tace “Mom kullum ya Fawaz saiya dinga shan kayan maye, nace yadena Yaqi ji, rannan yacemin yadena sha, shine yanzu ma naganshi yasha”

Alhaji Habib yayi ajiye zuciya, hajiya Farida tace “toke Dida waya fada miki ana kama maganar Mashayi? Ai yanzu zai zauna yadinga yimiki rantsuwa da Allah yadena amma ana jimawa zakiga yasha, waya kai Dan qwaya biyaiya? Idan gaisuwa ce har qasa zakiga yana gaida babba Kamar mutumin kirki, kuma yadinga yimiki rantsuwa shifa yadena shaye-shaye, amma hakan bazai sa anjima inde yaga qwaya yadauka yasha ba, kuma su masu shaye-shaye mace bata gabansu, bare ayi tunanin zataja hankalinsu harsu daina, da wahala kiga Mashayi wai yana kula yanmata, addu’ah daya zakiyi Dida Allah yasa Fawaz ya soki, to wannan kam idan yafara sonki duk abinda kikace zaiyi, amma a yanzu kam saide kiyi hakuri”

Ta kalli Alhaji Habib tace “Alhaji ba zama zakai ba7, tashi zakai kamaidata dakin mijinta”????

Dida najin haka ta qara volume din kuka tace “Mom Allah bazan koma ba, dukana fa yakeyi”

Hajiya Farida da Alhaji Habib suka hada baki wajan fadin “Duka!!”

Alhaji Habib yace “subhanallah”

Hajiya Farida tace “a a, to bazaki koma ba Dida, bazakije ya kashe minke ba, ina sonki, tashi ki shiga daki”

Dida tatashi taja jakar kayan ta tashige dakinta, hajiya Farida tayi tagumi tace “yau naga ta kaina, yarana har biyu agida,Allah ya hadani da sirikai biyu na arziki dana tsiya, shi na arzikin ya koro min ‘yar tana gida, shina tsiyar matar tagudo tabarshi, kaiiii Allah ka sayaya mana”

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Qaran da wayarsa takene yasa yaji baccin duk ya’isheshi, daqyar yabude idonsa ya kalli Agogon hannunsa yaga magrib ta kusa, kaiii gaskiya yadau lokaci yana baccin nan, wani kiran ne yasake shigowa yadauka yana magana daqyar “hello ummah yane”

Ajiya Abida ta Girgiza kanta, Allah ya shirya mata Fawaz, wai ita yake cewa yane tace “naje Asibiti ne ganin mijin qanwar ka naga family kowa yana zuwa amma bangankaba”

Yace “Ummah meyasamu mijin Ilham din”

“wallahi Accident yayi, harya samu karayama, yakamata de kaje, narasa meyake damunka Fawaz, gaba daya baka cikin nutsuwarka, anyi ma fada kadena shan qwayar nan amma kaqi ji, tokaci gaba wataran saita haukatar dakai, yanzu ace mijin yar’uwarka ciki daya yayi rashin lafiya kusan sati amma ace kai baka saniba, ai shikkenan idan Baqin cikin ka ya kasheni “dif ta kashe wayarta

” kai ummah tanada damuwa wallahi, menene kuma na ambatar mutuwa? “cewar Fawaz, daga nan yatashi yashige toilet yayi wanka, tsaf ya shirya cikin qananun kaya, yafuto falon, ganin dakin Dida arufe yasa bai shigaba, yasan tana bacci itama

Kai tsaye Mota yashiga yakira wayar Ilham din tafada masa a asbitin dasuke, sannan ya kashe wayar yaci gaba da driving

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune take agefen gadon akan kujera dede setin Inda kansa yake, Dan qaramin handkerchief ne a hanunta data jiqashi da ruwa tana goge masa kansa dashi, saboda taji kan nasa akwai zafi

Fawaz ne yashigo dakin shida wata nus datayi masa jagora, yana ganin halin da Aslam yake ciki jikinsa yayi sanyi, wannan hannu duk an nad’e masa shi, ga qananun ciwuka, tashi Ilham tayi tabashi kujerar Yazauna, anan yake tambayarta yamai jiki

Shiru sukayi na wani lokaci, Fawaz de jiki yayi sanyi, cikin ransa yake magana tabbas dan’adam ba abakin komai yakeba, kaduba kaga de halinsa Aslam yake ciki rai ahannun Allah shida bayama shan ko wacce irin qwaya, Allah ya jarabceshi da wannan qaddarar, to idan shine dayake aikata wannan mugun halin yaya nasa abin zai kasance kenan? ????
Tabbas dole ne yayiwa kansa fada ya shiryu Kamar sauran yan’uwansa, insha Allah yayi alqawarin daga yau yaraba hanya da kayan maye.
Jiki a sanyaye yayi mata sallama yatafi gida

Shiru Ilham tayi tana kallan Aslam, ita sai yanzu ne take ganin mugun kyansa, ya Aslam ya hadu ba qarya, amma da qiyaiya tahanata gani,Allah sarki, ko yaushe zai farka?.
Ahankali yafara bude idonsa, yasaukesu akanta, rufe idonsa yayi yana tunani nan take hatsarin dayayi yadawo masa cikin qwaqwalwar sa, bude idon yayi yaga tabbas Ilham yake gani a gefensa, meyasa tazo Inda yake? Ai yayi tunanin zatafi kowa murna
Farinciki ya rufe Ilham, cikin murna tace “Alhamdulillah, ya Aslam katashi? Sannu ya Aslam bari nakira Doc.”

Cikin sauri tafice daga dakin yabi bayanta da kallo, menene ya sauya yarinyar nan haka lokaci daya?

Doc. ne yashigo dakin ya duddubashi tareda yimasa yan tambayoyi sannan yace yaci gaba da shan magunguna zuwa jibi za’a warware masa hannun nasa, sannan yafita

Ilham kuwa sai murna take bakinta Yaqi rufuwa, kujerar datake kai takoma ta zauna, ta dora hannunta akan goshinsa tace “ya Aslam sannu, ahadama Tea kasha ko?”

Dayan hannunsa da Babu ciwo yasa yakawar hannunta dake kansa yace “kidena tabani banaso, ai shikkenan tunda hankalinki ya kwanta, ba haka kike so kiganni ba”

Wani irin kuka ne yazo mata maicin rai, batasan lokacin data fada kansa ta rungumeshi ba, tana kuka, hawayenta yana d’isa agefen wuyansa, cikin kukan tace “ya Aslam Dan Allah kayi hakuri Allah nadena”

Aslam kuwa baisan lokacin daya lumshe idonsa ba jin nashanunta masu laushi akan qirjinsa, dama gwadat yake yaga tadena rashin kunyar kokuma de tarkonsa yakama shima tafara sonsa????

Adede lokacin Adam yashigo dakin, hannunsa dauke da ledojin fruits, murna yafara ganin idon dan’uwansa biyu yaude yafarka, adaya bangaren kuma kunya ce ta kamashi ganin yanda Ilham ta rungumeshi tana wani kuka qasa-qasa ????

Aslam yace “Adam sannu da zuwa”
Ya kalli Ilham dako niyyar tashi batayi yayi qasa da murya yace “qanina fa yashigo, zakisa ya renani” ????

Ahankali tatashi tana goge hawayen idonta tace” ya Adam sannu da zuwa, ina wunin “

Adam yayi ajiyar zuciya yace” lafiya Ilham, ashe maigida ya miqe “

Murmushi tayi masa kawai, takama hannun Aslam din tariqe Kamar wani zai qwace mata shi.
Hajiya Na’ila ce tashigo dakin Diyana tana gefenta da abinci a hannunta

Da Adam tafara tozali acikin dakin, yana sanye da qananun kaya, saiyayi mata mugun kyau, ahankali tasauke idonta kasa, shikuwa Kallanta yake yana magana cikin ransa, Wato maryam dayace taje gida saiya nemeta wajansa mahaifiyarsa tatafi kenan ????, dama ai matsalar ka auri wadda kuke DANGI ‘DAYA da’ita kenan, yanzu Inda bare ya aura ko hanyar gidansu bazata nemaba, Dan Allah kalli wannan shegen kayan data saka duk ya kamata hips dinta awaje, kuma mama tana gani shine suka futo ahaka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button