DANGI DAYA HAUSA NOVEL
Cikin nutsuwa Diyana tace “ya Aslam ya jiki?”
Yace “jiki Dasauqi Diyana”
Ta kalli Adam dinma tace “ya Adam ina wuni ya aiki” ????
Shiru Adam yayi be amsa mata ba, haushi yakamata, Hmm zata rama ne
Hajiya Na’ila tace “kema de dabata yawun bakinki kike, kina gaidashi yana wani hura hanci, ajiye musu Abincin mutafi gida” ????
Diyana ta ajiye Abincin tafice daga dakin, hajiya ta kalli Adam tace “kasan abinda ka aikata ai, shiyasa idan na nemeka baka dagaba, to kazo gida ka sameni ina nemanka” tana fadar haka tafice daga dakin
Aslam yace “Adam kayi hakuri, kasan sha’anin mata sai Ahankali, dole sai kakai zuciyarka nesa, da niyya ma zasu dinga qin yiwa mutum biyaiya kasan… Su”
Maganar sace ta katse saboda mintsininsa da Ilham tayi ahannu????
Adam yayi Murmushi, shikam sun birgeshi, inama maryam zatazo ta koyi yanda ake kula da miji anan, yace “to insha Allah, nizan tafi, sai gobe idan Allah yakaimu”
Aslam yace “to shikkenan kakira Abba kafada masa natashi please”
Yace “okey”
Daga nan yaja musu kofar, Ilham tayi masa hararar wasa cikin shagwaba tace “shine zakake fada masa laifi na ko?”
Murmushi yayi yana Kallanta Kamar ba’itaba, Kamar an sauya masa qanwar budurwarsa????
Yace “ya jikinki? Yanzu de Babu kuka kin warke sosai ko?”
Kunya takama Ilham, tasa hannu ta rufe idonta tace “dan Allah ya Aslam katashi Muje kayi wanka” ????
Murmushi yayi, sannan yafara kokarin tashi, yana jin dayan hannun yana masa ciwon kadan-kadan
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Jikinsa a sanyaye yadawo gida yana tunanin mutuwa, kai tsaye dakinsa yawuce yabude kayansa duk wata qwaya datake ciki saida ya dauko ta, nacikin fridge ma yadauko su yazuba acikin wani kwali yanufi dakin Dida dasu, yanaso ya tabbatar mata cewa yau yadena shan komai, yanaso yafara tabbatar wa matar sa cewa daga yau Babu me sake kiransa da Mashayi
Amma me, yana bude dakin yaga bata nan, qarasa shiga yayi yaga kofar toilet dinta abude, afili yace “a a, to ina yarinyar nan tatafi ne? Nasan duk Inda zataje tana tambayata ai”
Cikin sauri yafuto yadawo kitchen bata nan, yaduba compound bata nan, kwalin dake hannunsa yasaki yafadi qasa, yasake komawa cikin gidan da gudu, karon farko daya fara ambatar sunanta “Dida! Dida!! Dida!!!, ina kike ne?”
Wasa-wasa saida Fawaz yagama duba gidan tas yaga bata nan, Kamar mahaukaci haka ya koma dakinta ya kalli Inda akwatunanta suke yaga sunragu, anya kuwa Dida ba guduwa tayi tabarshi ba? Kode taganshi ne dazu bayan yasha maganin mayen nan? Tabbas yarinyar nan taganshi, awajan ya sulale yazube akan gwiwar sa tareda dafe kansa ????????♂️, ya zata masa haka?
Dasauri yatashi yafuto daga dakin yashige motarsa bai zarce ko’inaba sai gida
Kai tsaye part dinsu yatafi, hajiya Abida tana zaune tana kallo sai ganinsa tayi yashigo Kamar mahaukaci
Tace “subhanallah Fawaz lafiya?”
Yana daga tsaye yace “umma Dida batazo nan ba?”
Tace “Dida kuma? Aini rabona da Dida Tun bikinku Fawaz, kai baka taba hankalin dauko ta ka kawomin ita ko wuni ne muyi ba, itama batazo ba”
Gabansa ne yafadi, Yazauna aqasa kafet din falon jagwab, Idanunsa suka kada sukai jajir yace “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un , Umma Dida tagudu tabarni” sai kuka ????
Gaban hajiya Abida yafadi tace “kaini banason sakarci, yanzu Inda qannanka suna nanma haka zaka zauna kanamin kuka, kayi min bayani dalla-dalla meyake faruwa?”
Cikin kuka yace “umma…gani…ganina..tayi nasha wani magani shine… Shine…tagudu”
Tace “ahaf, ni nasan da walakin goro amiya, haba Fawaz, yarinyar nanfa tana kokari, aure kusan shekara biyu amma bata taba kawomin kararka ba, lokacin da akace anhadaka da’ita yarinyar nan ko uhm batace ba, duk family dinnan kowa yasan anfi qwararta akan sauran ‘yan’uwanta, ai kai kamata yayi ma ace kayiwa yarinyar nan gata samada kowa acikin gidannan, kayi mata abinda takeso ka fifitata saboda ta rufama Asiri ta zauna dakai, yanzu ma dakace akan kasha wani magani tagudu bawani magani dazaka sha Fawaz bayan na maye “
Cikin kuka Fawaz yace” to umma kuma saita gudu tabarni “
Tace” a a, bamu bincikaba ba zamuce tagudu ba, tashi Muje wajan maigadi muji ko yaga shigowar ta gidan “
Tashi yayi yana goge hawaye yabi bayanta, suna zuwa wajan maigadi ya tabbatar musu da cewa tabbas yaga Dida Tun rana tashigo gidan, shine ma yabude mata get
Hajiya Abida tayi masa godia takoma part dinta, ta nemi kujera zata zauna kenan Fawaz yasa hannu yariqe rigarta yace “Ummah matata” ????
Qwace rigarta tayi tazauna tace “tome Zan maka Fawaz? Bakaji da bakinka ance tazo gidaba? Ai kasan hanyar part dinsu”
Zama yayi agefen qafafunta yana kuka Kamar mace yace “Ummah Allah nide adawomin da matata, ya za’ai naje part dinsu bayan nasan mamanta bata sona” ????
Hajiya Abida tace “kaga Fawaz karufe min baki, ya zakazo kasani agaba kanamin kuka? Lokacin daka mata laifin kayi shawara Dani? To bari kaji, tunda akai auren ku har yau Babu Wanda yace uffan akan zaman aurenku, Dan haka ba zanje part din hajiya Farida tafadamin magana inqyale taba, wallahi saide kaje”
Bece da’ita komai ba, yatashi yafice daga part din, yayi nasu Dida, hankalin sa kwance yatura kofar falon, a lokacin kuwa Dida tana zaune itada Hajiya Farida suna kallo, kallo daya tayi masa tadauke kanta, cikin ransa yace tana nan kenan
Hajiya Farida tace “a a Fawaz kaine atafe, sannu da zuwa, shigo ka zauna”
Fawaz yanemi waje Yazauna yana mamakin yanda ta karbe shi hannu biyu, sai sunkuyarda kansa yake qasa dan karsu gano yasha kuka ????
Hajiya Farida ta miqe tsaye tace “Dida kawo masa ruwa mana” daga nan tayi cikin dakinta tabarsu su biyu, cikin ranta tace tasan bazai wuce biko Fawaz yazo ba, ita kuwa bada itaba, yaje su qarata atsakaninsu, tunda taga Dida tadawo gida tasan cewa qarshe yakai yarinyar shiyasa tayi fishi tataho gida, to ba zatayi mata dole akan takoma gidansa ba, Dan daga nanma zata iyayin wani gidan su nemeta su rasa, gara yanda tazo da qafarta, takoma da qafarta, amma bazata bakinta a sabgar yara ba
Daga kan kujerar yasauko yadawo kusa da ita har tanajin yanda numfashinshi yake sauka akan fuskarta yace “Dida”
Kallansa tayi, yaune karon farko data tabaji yakira sunanta, harara ta sakar masa tatashi ta nufi hanyar dakinsu, shima yatashi yabita, tana shiga dakin tarufo kofar, shikuma yakawo kansa zai shiga sai qumm tabige masa fuska
Kadan yarage Fawaz yayi hauka agidan surukai ????, haka yafuto jikinsa duk yayi sanya, ko kallan part dinsu baiyi ba yaja motarsa ya koma gida
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe hajiya Na’ila bataga futowar Diyana ba, Dan futowar datake ta yataya aiki ma yau shiru ????
Tace “to wannan yarinya ko lafiya?” tashi tayi ta nufi dakin nata, tana zuwa ta risketa tana kuka adaki, hajiya tace “subhanallah Diyana menene kuma yafaru?”
Cikin kuka tace “Hajiya niso nake natafi gidanmu”
Hajiya tanemi waje tazauna agefen Diyana tace “ai dole kice zaki tafi gida Diyana, tunda shi yazo ya ajiye ki baya tunanin zuwa ya dauke ki, bansan yaushe Adam yakoyi taurin kaiba, nace yazo gida ya sameni Yaqi zuwa, nakira wayarsa kuma yadena dauka ma yanzu, inde baso yake na yiwa babansu maganar ba bansan yaya zanyi ba, hada kayanki ina zuwa “
Gyada kanta tayi, sannan tadauke komai nata na dakin itama ta shirya, hajiya ce tadawo dauke da cup ahannun ta da zuma aciki, tace “ki kalli abinda Zan hada miki kigani saiki dinga yi ,”