DANGI DAYA HAUSA NOVEL
Daria yayi, sosai kuma dariyar tayi masa kyau yace”Diddi Zan kaiki umarah”
Cikin farinciki tace “Umarah Abba!”
Yace “harda Hajji”
“Alhamdulillah yau haihuwa tayi rana, Yaya bekaini ba gashi Abba zaikaini”
Momy tace “inde Abba ne zamu ganku arana”
Dariya sukayi gaba dayansu
“Diddi ga omon” cewar Nihla data shigo yanzu
Karbar omon tayi, tace “jeki zuba ruwa inzo na wanke miki kanki, saina miki wanka ma gaba d’aya”
Ruwan tazuba tadawo ta zauna agaban Diddi kusa da Abba, sannan ta d’ora kanta akan cinyar Diddin, hannu tasa ta warware mata gashin kanta, daga Momy har yaran nata duk kallan yawan gashin yarinyar suke,
Saida tagama warware mata sannan tace “Muje na wanke miki to”
“Diddi Zan wanke mata”
Cikeda mamaki kowa yake kallansa, musanman Momy, cikin ranta tace tabd’i
Amma a fili sai tace, “lalle Nihla kin ciri tuta”
Diddi tayi daria tace”lalle yau haihuwa tanamin rana sosai”
takai Kallanta ga Nihla tace ” ke tashi kije yayanki ya wanke miki kanki “
Babu musu tatashi ta cire kayan jikinta, daga ita sai pant tabishi suka futo tsakar gidan ta tsugunna, shima tsugunnawa yayi sannan yafara zuba mata ruwa akan, ba komai yasa yace zai wanke mata kanba, saidan yanaso yataba gashin yaji, omon yad’auka yazuba mata akan sannan yafara wankewa yana dirzawa da duka hannunsa biyu
Momy dasuke zaune a rumfa kallansu take tanajin d’ad’i aranta, ashe Abban nata ya’iya wankin kai,???? shikuwa Usman hannu yasa a aljihun jeans d’insa yad’auko wayarsa yana musu photo
Kannata yafita sosaai amma haka yaita wasa da gashin sannan yadena zuba mata Ruwan, ya kalleta Ahankali yace “kicire wandon nayi miki wanka”
Hannu tasa ta goge Ruwan daya zubo mata a fuskarta ta d’aga murya tace “Diddi wai yamin wanka?”
Cikin rashin damuwa tace “Eh yayi miki mana”
Ahankali tatashi ta cire wandon sannan ta tsugunna, babu bata lokaci yafara yimata wankan, saida ya wanke mata jikinta tass sannan yacemata “tashi kije”
Bata damu da yanda yayi mata maganar Kamar bayaso ba, tatashi tatafi d’aki da gudu
Da yamma Usman da Aliyu da Farouq suka fice yawo ganin gari
Nihla kuwa tunda Abba yayi mata wanka ta shiga d’aki tasaka wata ‘yar qaramar riga marar hannu tashan iska, ta kwanta tana wasa tana surutun ta ita kad’ai anan bacci ya dauke ta
Diddi ta kalli Abba da Idanunsa suke lumshe wa tace”me sunan yaya nah, kai ba zakaje yawon kaga gari ba? “
Hamma yayi yace” Diddi bacci nakeji “
” to tashi ka shiga d’aki mana, jeka kwanta kahuta, dama ai akwai gajiya kunsha hanya “
Yana shiga d’aki yaga Nihla na bacci, katifar tanada girma sosai, shima ya kwanta agefenta, nan da nan kuwa yayi bacci
Saida Momy ta leqo d’akin taga sunyi bacci dukansu sannan ta kalli Diddi tace” Aisha kin tambayeni kowa amma baki tambayi yayanki ba, “
Lokaci d’aya yanayin Diddi ya sauya,” Anty Rahma yaya bayasona yanzu, wannan shine dalilin dayasa bazan iya baki Nihla ba, qiyaiyar dayakemin bakan kowa zata komaba sai kan ‘yata,nikuma ina son yata, banasan wani abu yasameta, yanzu haka tsoron irin amsar dazaki bani ne yasa ban tambayeki shiba, saboda nasan ba zanji amsa Mai d’ad’i ba “
hawaye ne suka zubo mata, wasa wasa Tun ta nayi marar sauti harta dawo tana kuka sosai Kamar qaramar yarinya
Ajiyar zuciya Momy tayi, ta dafata “Aisha yayanki baya fishi dake yanzu, idan ma yanayi to kad’anne,kisaki ranki kidena damuwa, wai Aisha ke kadai kikai wannan laifin ne? Baga Basiru nanba, ganin yarane yasa banyi miki fada ba, ki kalli jikin ki aisha kin kasa kwantar da hankalin ki duk kin rame, meyasa hakan Aisha “
Cikin kuka tace” dole zanyi kuka Anty Rahma, ki kalli irin Rayuwar danake nida ‘yata, Yaya yana dashi bazai tallafamin ba, uwarmu d’aya ubanmu d’aya, wacce irin qiyaiya ce wannan? “
“Aisha idan kika sake zancen qiyaiyar nan tsakanin keda yayanki ranki zai baci yanzun nan, yanzu haka yayanki ne ya shirya mana wannan tafiyar, kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, watarana komai zaizo qarshe”
Jakarta ta bude tadauko kudi masu yawa ta miqa mata, Diddi tasa hannu takarba,sannan tasake dauko mata wata sarqa ta gold tabata, sannan tace “ki ajiye wannan sarqar awajan ki, dakaina nasiyo miki ita, tanada tsada, duk lokacin dakika buqaci kudi idan babu ahannun ki kije kasuwa kisiyar kiyi amfani da kudin, shikuma wannan kudin dubu hamsin ne,yayanki yace akawo miki”
Hawaye masu d’umi suka zubo wa Diddi, taji dadin kyautar amma wani bangare na zuciyarta ya kasa yarda cewa yayanta ne ya aiko mata da kudin, ta kalli Momy tace “nagode sosai Anty Rahma, Allah yasaka da alkhaairi”
Momy ba tace komaiba tajata jikinta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida taga ta daina kukan tasaki ranta, sannan suka tashi suka fara shirye-shiryen had’a Abincin dare
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Cikin bacci taji anajan gashin girarta, zafi taji, lokaci d’aya tabude idonta, dashi tafara yin tozali yana kwance agefenta yazuba mata ido, tace “kai meyasa kakejamin girata, Allah Zan fadawa Diddi”
“to sai bacci kike kitashi mana, tashi natayaki wasa”
Kafada ta maqale masa “bazanyi wasa dakai ba,saboda d’azu kaine kaqi rakani shago nasiyo omo”
Kansa ya nuna da hannunsa yace “nid’in? bana wanke miki kanki ba?”
Daria tasaka, gefen kumatunta duka biyun suka lotsa, ahankali ya d’ora hannunsa awajan, itama hannunta tasaka ta janye nasa hannun daga fuskarta tace “eh natuna, kamin wanka, to mun shirya, meyasa kai baka magana? Anty tace baka magana”
“inayi mana, gashi ina magana dake”
Gyara kwanciyar ta tayi Tajuyo tana fuskantarsa, kusancin yayi kusanci Kamar zata shige jikinsa, tace”meyasa to kakeyi Dani?”
” because You’re my friend “
Girgiza kanta tayi tace ” niban gane me kace ba”
“Zan fad’amiki”
“yaran Momy kun tashi daga baccin kenan” Dagowa sukai dukansu suka kalleta, Dasauri Nihla tace “yawwa Anty, me You’re my friend take nufi?”
“Nihla Anty, Anty, nahanaki cewa Antyn nan kinqi ji, to zamu bata dake, kutashi ku futo kuyi shirin sallah, magrib takusa,”
tana fadar haka tafice daga d’akin, itama Nihla tashi tayi tafice tabar Abba shi kad’ai
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da daddare dukansu suka baje a tsakar gidan akan tabarma, Nihla ta liqewa Usman tana ganin game a wayarsa, gama cin Abincin su kenan, sai lemuka dasuke ajiye agefe Wanda suka sha sukabar sauran
Baba ya kalli Momy yace “Amma hajiya ai zakuyi mana sati d’aya ko”
Momy tace “sati Ibrahim! Haba Mai hakuri, sati ai yayi yawa, jibi jibin nan zamu tafi insha Allah, kwana biyu zamuyi muku, saboda yara suna zuwa school, yanzu ma saida muka sanar a makaranta sannan muka Taho dasu”
Yace “to hajiya, ai hakanma kunyi kokari sosai, su Alhajin de duk suna lafiya ko?”
“lafiya kalau alhmdlh”
“to yaya wajan su hajiya Farida da yaran nata su Dida da Diyana?”
Wannan karan saida Momy tayi Murmushi, saboda tasan duk cikin mazawaje family baya shiri da kowa Kamar hajiya Farida, tace masa “suma suna nan kalau”
Yace “to madallah, Allah yasaka da alkhaairi Hajiya, Aisha duk ta nunamin abin arziqi”
Murmushi Momy tayi ba tace komaiba, suna nan zaune suna taba hira har dare yayi, suka nemi makwanci, Usman da Aliyu da farouq sukabi baba d’akinsa, Momy da Diddi da Abba da Nihla suka tafi dayan d’akin suma, Momy ce ta gyara musu shimfida daga nan taja Nihla jikinta suka kwanta, yanda tasata a gabanta Kamar wani zai qwace mata ita, har Diddi nayi musu daria