DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Wayarta tace tayi qara tana dubawa taga Abokinta ne yake kira Wato Abdallah qanin Anty Nadiya, tanayin picking ya sanar da’ita cewa Posting dinsu fa yafuto, taje taduba nata, shi anduba masa nasa yaga sun turashi yola

Tace “toooo yola!, tabdi nikam ko’ina suka kaini? Sai Allah”

Yace “kije kiduba naki kema, sai munyi waya”

Bata jira komai ba, ta shirya tsaf, taje kafe aka duba mata, Wanda yaduba nata yaciro posting latter din yabata, tana dubawa taga anyi posting dinta kano, cikeda mamaki tace “kano kuma?”
Kudinsa tabashi tadawo gida, a compound taga su Baba da ya Yusif da Alhaji Isma’iel Abban ya Yusif, tana gaishe su ta miqa musu takardar, kowa yagani, duk sunyi mata murna da aka turata jihar musulmai, Alhaji Isma’iel ya kalli Yusif yace “to Yusif ai sai kuje tasiyo abubuwan dazata buqata gobe tabi jirgi tatafi ko?”

Yace “to Abba insha Allah”

Sannan ya kalleta yanayi mata wani kallan luv yace “kishirya anjima sai Muje shopping din”

Da yamma kuwa sukaje shopping, tasiyo komai na buqata, tagama shirya kayan ta tsaf, tunda aka ambaci service akano taji tanayin murna badan komaiba, tasan zataga Ilham da Momy

Da daddare baba yazo har dakinta, tayi mamakin ganinsa a dakin Dan ba shigowa yake ba, Kallanta yayi yace “Nihlan Diddi, gobe kuma sai kano ko?”

Murmushi tayi tace “hakane Baba”

Yace “to banda shirme de, ki tsaya kiyi abinda yakaiki, idan kun gama zaman camp din idan kinga zaki iya cigaba dayin service din Acan saiki zauna, idan kuma bakyaso saiki nemi relacation kidawo nan”

Tace “to Baba, amma Baba ai gara na dawo nan din yafi, saboda nanne gida”

Yace “a a, can dinma ai gida ne, ga yayun mahaifiyar ki duk suna can, sai kije can kiyi zaman ki”

Tace “to Baba kakira su awaya kafada musu zanzo”

Yace “saboda ga gwamna ko shugaban qasa ko? Sai an sanar dasu zuwan ki, ????kema ai iyayen ki ne, kikirasu da kanki kifada musu, ni bazan saka baki akan zaman ki agidanba, kawai de bazan dauki abinda za’aci zarafin ‘yataba”

Murmushi tayi tace “to Baba insha Allah, zankirasu”

Kallanta yayi yaga tanata murna, yasan kuma bazai wuce ace murnar ganin Momy bace, Dan zuwa yanzu kam yasan ai ta cire Abba aranta, daga nan yatashi yayi mata sallama yatafi

Washe gari saida tayi sallar azahar sannan ta shirya cikin doguwar riga Mai adon stones ajiki, sannan tayi rollinga tasaka wani shegen glass a’idonta, sai zuba qamshi take, idan ka kalleta saika sake waigawa, tayi masifar yin kyau, farar fatarta yaqara futowa sosai sai shining jikinta yake

Ya Yusif ne yakai ta Airport sai firar soyaiya suke abinsu gwanin sha’awa, har lokacin tashinsu yayi, sukai sallama yace zai kawo mata ziyara idan yasamu dama, da haka tashige cikin jirgin akaro na farko atarihin Rayuwar ta, wayarta tadauko zata kira Momy, kawai saita fasa, gara tayi mata surprice kawai

Ko awa daya basuyi ba, jirginsu yayi landing, tana futowa daga Airport din mutane suke ta Kallanta, daga ita sai yar qaramar truly dinta tanaja, tayi mutuqar birge kowa, Mai taxi ta tare tashiga tafada masa Inda zai kaita, acikin motar ma kafa daya ta dora kan daya, tana daddana waya, har sukazo bakin get din family house din Mazawaje

Sallamarsa tayi, ta tsaya ta qarewa Babban get din gidan kallo, duk an sassauya abubuwa dayawa, yau gata a Mazawaje family akaro na biyu

Tura get din tayi tashiga, iliya Maigadi yana zaune yanajin radio, taga ya kalleta yayi shiru Kamar besanta ba, cikin mamaki tace “iliya d’anmai qarfi baka ganeni bane?”

Kallanta yasake yi, yaji sunansa radau abakinta yace “Wacece? Bangane kiba wallahi, baquwa mukayi ne?”

Murmushi tayi ta cire glass din idonta tace “iliya nice Nihla fa”

Cikin sauri yatashi tsaye yace “kai kai kai, wai Nihla kece? Aini jinake wata balarabiyar ce wallahi, a a a a, masha Allah, sannu da zuwa, sannu sannu, kice yau munada manyan baqi agidan namu, kawo jakar taki, kawo, kawo”

Nihla tayi Murmushi tace “iliya kenan,”

Sannan tabashi jakar, suka nufi part din Momy, saida yakai mata jakar har cikin falo sannan yajuyo yana qara yimata sannu da zuwa, Nihla ta zube akan sabun kujerun falon da aka sake tace “wash Allah nah, gajiya”

Sannan tadaga murya tace “Momy!!! To futo ‘yarki tazo”????

Kamar almara Momy Tajuyo Kamar muryar Nihla, amma sai taqi gaskatawa, mezai kawo Nihla kano yanzu? Kawai de kunnanta ne

Nihla tasake cewa “Momy!, koba kowane agidan?”

Dasauri Momy tafuto falon, taga Nihla kwance akan kujera ga jakar tanan agefe, qaraso wa tayi cikeda tsananin mamaki, Nihla na ganinta tatashi ta gudu taje ta rungumeta cikeda murna

Momy tadagota daga jikinta tana Kallanta tace ” Nihla ‘yata, yanzu Allah kece kika qara girma haka? Gaba daya kin sauya kamar ba Nihla ta tadaba”

Dariya tayi tace “Momy nice mana, wai meyasa kowa yake cewa na sauya ne? Momy girma naqara ne?”

“girman ma Nihla, kin qara kyau, Kamar balarabiya, mezakici adafa miki yanzu?”

Saida tayi farrrr da idonta sannan tace “Momy yanzu banajin yunwa, saide da daddare, but idan akwai cornflakes zansha kadan”

Momy ta lakace mata hanci, tace “Wato bakyason cin abinci Kamar da ko? Ni narasa ya’akayi ma kikai bul-bul dake masha Allah Babu wata rama Kamar da”

Dariya tayi, cikin ranta tace Anty Nadiya ce sirrin, afili kuwa sai tace “Momy bari nakai kayana daki”

Momy tace “a a Barshi, Adala zatazo takai miki, tashi Muje ki gaisa da sauran yan gidan”

Hannunta Nihla ta riqe Kamar wasu qawaye suka futo, kowanne part saida sukaje ta gaida kowa, kuma kowa sai nan-nan yake da’ita, kowa yayi murna da dawowar Nihla, saita zama wata abar sha’awa kowa Kallanta yake yanda ta sauya,Hajiya Farida maman su Diyana kuwa tana ganin Nihla taji tausayin Abba ya kamata ???? ????

Haka suka dawo part din Momy, Nihla ta dora kanta akan cinyar Momy tana bata labarin makaranta dakuma service din da aka turota

Suna wannan firar har la’asar tayi, Tatashi taje tayi wanka, tasaka riga da wando na jesy, (kayan ball) na mata, amma nata dogon wando ne Mai launin dark blue, Momy ce da kanta tahado mata cornflakes din, tace “to yata taso kisha, yauda kaina Zan baki”

Murmushi tayi tatashi, suka zauna a kafet din, Momy tafara bata, ita kuwa sai surutu take mata, Momy cikin ranta sai mamakin yanda Nihla ta sauya takeyi, kanta Babu dankwali hakan yasa dogon gashinta dayasha gyara kwanciya a bayanta

Adede lokacin yaturo falon nasu yashigo, yau kwanansa takwas baya qasar ma baki daya, saukarsa kenan

da dogon gashinta yafara tozali, kasancewar tabashi baya baiga fuskar ko Wacece ba, mamakin hakan yasa yaqame a tsaye abakin kofa, Wacece wannan Kamar ba ‘yar hausawa ba kuma Momy tana feeding dinta?

Momy ce ta lura dashi takalleshi cikin murmushi tace “a a Abba, shigo mana”

Jin an ambaci sunansa yasa bugun zuciyarta ya sauya, ahankali tajuya ta kalli bakin kofar itama, lokaci d’aya Idanunsu yahade dana juna, cikin abinda baifi second ashirin ba tagama qare masa kallo, yau ne karon farko daga taba ganinsa azahiri sanye cikin kakinsu na Pilot Mai launin fari da baqi banda pic dinsa data gani awayar Anty Nadiya sanye da kayan , sosai kayan sukayi bala’in karbar jikinsa, yaqara girma, yaqara yin kyau Kamar ba shiba yasake zama babba tamkar wani cikakken magidanci, kawarda idonta tayi,ta karbi spoon din hannun Momy ta cigaba dashan cornflakes din ta, shikuwa kasa dauke idonsa yayi akanta, shin anya kuwa ita dince de agabansa? Inda ace baiyi mata kyakykyawan saniba Babu abinda zai hana yakasa ganeta, but ya’akai takoma haka? Dogon gashinta yasake kalla Kamar ba gashin bahaushiya ba, ahankali yaqaraso cikin falon cikin takun izza

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button