DANGI DAYA HAUSA NOVEL
Gabanta yaje ya tsaya yana Kallanta, duk kuma saita rikice tarasa mezataci gaba dayi, ta kalleshi tace “Sannu da zuwa ya Fawaz”
“yawwa sannu da kwalliya Baby Dida “
Murmushi tayi, ahankali tafara kokarin tashi zata nufi wajan kayan ta, Miqewar da zatayi towel din ya kunce yayi qasa ????????♀️
Ganinta haka Babu komai yasa cikin sauri Fawaz ya runtse idonsa, bugun zuciyarsa yafara sauyawa, ita kuwa Dida tsugunna wa tayi ta rarumi towel dinta ta daura ????
Tayi tunanin zata riskeshi yana kare mata kallo amma abun mamaki tana kallansa taga idonsa a runtse, mamaki ya kamata, to kode ya Fawaz baida lafiya ne?
Miqewa tayi tsaye tace “ya Fawaz Zan shirya, kaje Zan futo ma da maganin”
Babu musu yace “to” sannan yafuto, Dida tabishi da kallan mamaki, mum tace mata masu shaye-shaye basa kula mata, to amma ita ai matar sa ce, menene zaisa ya runtse idonsa Kamar yaga abinda ba halal din saba?
Haka ta shirya tafuto falon tabashi maganin yasha, anan falon suka zauna suna kallo, amma Babu fira, maganar sai de kadan kadan ????, ita Dida tana tunanin hali irinna Fawaz, shikuma idan ya kalleta saiya tuna dazu da towel yafadi, dama haka wannan abin na qirjinsu yake? Dama bata tsugunna ba, meyasa ma ya runtse idonsa ne?
Ahankali yatashi ya kalleta yace “zanje daki nadan huta, anjima Zan futo”
Cikin ladabi tace masa “to”
Dakinsa yashige yafada kan gado, ya janyo fillo ya rungume yana tunanin Dida, gara yazo daki ya kwanta yanda zaifi jin dadin tunanin nata, ahankali yaji yanayin sa yana sauyawa, Tun yana jin dadin tunanin harya dawo yana jin mararsa tana masa ciwo kadan kadan, sai qara matse fillo yake a qirjinsa
Shiru shiru har bayan sallar ishsha’i Dida bataga Fawaz yafuto ba,dakinsa tabishi anan taganshi akan gado yahada uban gumi, yatakure kansa waje daya, Dasauri ta qarasa wajansa “Innalillahi, ya Fawaz, menene yake damunka? Meyasa baka kirani ba?”
Kasa magana yayi, sai runtse idonsa yake, Dida tasa hannu ajikinsa tana jijjigashi, “ya Fawaz, kafadamin meyake damunka? Zaka iya tashi Muje asbiti?”
Girgiza mata kai yayi, ahankali yakamo hannunta yajashi jikinsa, batayi aune ba taji yadora hannunta akan mararsa, gabanta yafadi, Dasauri tafara kokarin dauke hannunta, amma Fawaz yariqe hannun yana qara tura matashi can qasan mararsa, cikin sauri ta fizge hannunta tana fadin “nashiga uku na, tsaya ya Fawaz ina zuwa”????
Falo tafuto takira wayar likitan daya dora Fawaz din akan magani, cikin tashin hankali tace “doctor, ya Fawaz baida lafiya, cikin sa yana ciwo, kuma bazai iya tashi mutaho hospital ba, Dan Allah ko zaka temaka kazo ka dubashi?”
Doctor yayi jimmm, yasan de ciwon cikin namiji baya wuce qarfin sha’awa ne kawai, Fawaz Yana buqatar matar sa ne, ajiyar zuciya yayi yace” keba matar sa bace? Kibashi haqqin sa”
“doctor kamarya? Mekake nufi?”
“ina nufin mijinki Fawaz Yana buqatar mace atare dashi, Inda baida aure sainazo na kawo masa maganin dazaisha, amma yanada iyali, menene amfanin ki? Kibashi haqqin sa kawai Tun kafin mijinki yaje yakai kansa wajan wata, Allah yakiyaye hakan”
Gaban Dida sai faduwa yake, kai tsaye tace “gaskiya Doc bazan iyaba”
Yace “to shikkenan, ai zaki iya biyawa mijinki buqata ta wata hanyar, amma de Karki Barshi haka,ke mace ce, kinsan hanyar dazakibi kisamawa mijinki nutsuwa basai nafada miki ba, sai anjima”
Doc. Ya kashe wayarsa yabar Dida da waya akunne, tunani takeyi tayaya zata iya cire kunya tayiwa yaya Fawaz wani abu? To amma kuma Doc yace zai iya kai kansa wajan wasu matan, yanzu yaya zatayi? Diyana ce tafado mata, Dan haka ta dannawa ‘yar’uwar tata kira, a lokacin suna can suna bacci, Adam ya qwaqumeta ajikinsa, sama sama taji wayarta tana ringing, tameqa hannu ta dauka taga Dida ce me kiran, cikin sanyin murya tace “Dida ya’ akayi?
“Diyana kinga ya Fawaz ne baida lafiya, cikin shi yana masa ciwo sosai, bakiga yanda yake hada gumi ba, tona kira Doc. Sai yacemin wai matar sa yake buqata, kokuma wai namasa wata dabarar, narasa ya zanmasa Diyana, Kibashi shawara Dan Allah ya zanyi? Abinda nauyi Diyana “
Diyana tayi shiru tana tuno irin azabar da tasha ahannun Adam, tace ” karkiyi masa komai kirabu dashi yamutu “????????????♀️
Cikin sauri Dida tace” narabu dashi yamutu fa kikace Diyana, haqqin sa yana kaina ya za’ayi nabarshi ya mutu? “
Diyana tace” to Dida Karki bari yamutu, ke saiki tsaya ya kasheki ai “
Qit takashe wayarta tana masifa, yarinya ana nuna miki annabi kina runtse ido, nace kirabu dashi zaki fara min wa’azi wani haqqi haqqi ai sai kije, lokacin dazakiban labari Babu wani haqqi dazaki tuna
Adam kuwa yana jinta yayi shiru Kamar bacci yake, sai dariya yake qasa-qasa ????
Haka Dida takoma cikin dakin nasa tazauna agefen gadon tayi tagumi, tarasa shawarar wazata dauka, Doc. Kokuma abokiyar shawararta Diyana, tajuya ta kalli Fawaz taga gaba daya ya rikice mata
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda tadawo daga camp taci gaba da harkar gabanta agidan, kuma har zuwa wannan lokacin magana bata qara Hadata Da Abba ba, idan taganshi afalo ma bata futowa, idan tafuto kuwa ko gaida shi batayi take harkar gabanta, abin yana masa mugun ciwo, yarasa yaushe yarinyar nan takoyi rashin kunya
Yauda yamma taci kwalliya cikin riga irin readmade dinnan, Mai launin green, rigar tayi mata mugun kyau, kuma tayi daidai da jikinta shape din cikinta daya kwanta yafuto sosai, hakan yasa qirjinta Dagowa, daga qasan rigar kuma abaje take, sai farin mayafi data nad’a akanta, tafitar da gashinta waje
Falo tafuto hankalinta yana ka waya tana daddannawa,a lokacin Abba yana zaune da system agabansa yana serch wasu abubuwa, wando ne ajikinsa three quater, sai riga irin body hock dinnan, takama jikinsa rigar, hakan yasa muscle dinsa ????????bayyana, sarai taganshi azaune amma ta dauke kanta, tazo tawuce ta gabansa ta zauna awata kujera ta gefensa, harda dora kafa daya kan daya, tadauki remote tana sauya tasha, wayarta ce tayi qara ta duba taga Ilham ce, cikin murmushi tadauka “meciki”
Ilham tace “mekikeci nabaka na zuba, abinda bai zoba bai wuce ba”
Wani irin dariya tayi me daukan hankali tace “um um aide baizo dinba, ke kuwa yazo, yakike yagida”
“lafiya Nihla, kinqi kizo, kewai karkizo ki takura mana kuma wallahi Babu wata takura, ya Aslam dinma baicika zama ba wallahi”
“kwantar da hankalinki insha Allah zansa rana dukanku nazo muku”
Ilham tace “to shikkenan, bari naje Zan aiki direba kasuwa, wani sabon direba ya Aslam yakawomin waiko Zan buqaci wani abu, wallahi yacika shirme dayawa”
Murmushi Nihla tayi tace “Toda ke waye yafada miki direbobi basuda shirme? Ai kowanne irin direba dakike gani duk haka suke” ????????♀️????
System din gabansa ya janye yajuyo yana Kallanta, me yarinyar nan take nufi? Bade shi take fadawa magana ba, Wato kowanne direba mashirmaci ne, to Allah yasa tace harda Direban jirgi, wallahi dasai taga qarshen rashin kunya yau????
Momy ce tashigo falon, tayi Murmushi tayi matuqar jin dadin ganinsu atare , tayi tunanin masu zaman falon zaman arziqi suke, tace “a a, ashe duk kuna nan kuna kallo”
Abba Bece da ita komaiba yadauki computer dinsa da wayoyi yanaso yatashi daga wajan, Nihla ta kalli wani mujalla agefenta tabude taga pictures din kayan daki dasu kujeru masu mugun kyau, haka take bude shafi shafi tana gani, gaskiya kayan sunyi kyau sosai, sun birgeta, bangon farko takoma tagani, anan taga amsa A&A FURNITURES