DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Ta kalli Momy tace “Momy wannan kayan sunyi kyau sosai gaskiya, inane wannan A&A din?”
Momy tace “laaa campany yayunki nefa, Abba da Aslam ne suka bude, nayi tunanin ma kinsani ai”
Girgiza kanta tayi, tace “bansani ba”
Cikin ransa yace yawwa tunda batamin magana yanzu ai dole tatayani murnar bude campany…
Kafin ma yagama tunanin sa yaji tace “idan nasamu lokaci zanje nayiwa ya Aslam din murna” ????
Cikin ransa yace Aslam… It means banda Abba, cikin bacin rai yatashi fuuuuu yashige cikin dakinsa
Babu Wanda yalura da yanayin sa, saboda shi dama koda yaushe fuskarsa adaure take
Yana zuwa yafada kan gadon yana tunani cikin damuwa, tunda yarinyar nan tazo gidannan baitaba ji takira sunansa ko sau dayaba,yalura kallan arziki ma baya samu awajanta, to meyasa hakan? Meyasa?
Nan take ya tsinci kansa cikin damuwa a dalilin hakan
More Comments more typing, idan akai Comments dayawa nima inyi typing dayawa, idan akai Comments kadan nima inyi typing kadan, babu zafi ????????
Amnah El Yaqoub ✍️
[7/4, 12:34 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Masu buqatar sa daga farko sunemi wannan number 09039066577, kokuma kai tsaye suje page dina suyi like saisu karanta
35&36
Furzar da iska yayi daga bakinsa tareda yin ajiyar zuciya, toshi menene ma zai dame shi?wata zuciyar tace saboda yar’uwar ka ce, sannan kaida ita DANGI DAYA ne, ba haka take wa su ya Usman, meyasa shi take rabuwa dashi?
Koda yake, yasan ba komai ne yake damunta ba sai yarinta ????
Wataran idan tayi hankali zata dena, danhaka shi zai dinga yimata magana kawai
Washe gari dasafe yana kwance akan doguwar kujera wayarsa na hannunsa yana danne-danne, Momy kuwa tana gefe tana waya da Daddy dayayi tafiya, Nihla ce tafuto daga dakinta kai tsaye wajan Momy tanufa ta dora kanta akan cinyar Momy, binta yayi da kallo, lokaci yayifa dazai fara yiwa yarinyar nan magana, to amma ta wacce hanya? Shi dama can bawata magana sukeba, mezece mata yanzun?
Hakanan ya tsinci kansa cikin faduwar gaba, tome hakan yake nufi? Tsoron ta yakeji kokuma kwarjini take masa? ????
Daqyar yayi gyaran murya yadaga kansa yana Kallan gashinta dako dankwali Babu yace ” Am Zan samu coffee?”
Sarai tajishi amma saita shareshi, idan bazai kira sunanta ba yabari, babu wani coffee dazata hada
Momy ta kalleshi taga idonsa akan Nihla yake, da alamun da’ita yake kenan, kuma taga alama itama Nihlan taji tayi masa banza, kai wannan yara tarasa ya zatayi dasu, ta lura kowa jinkansa yake, yanzu shi bazai bude baki yace Nihla tashi kihadamin coffee ba, saide ya yi mata magana Kamar yana magana da wata daban ba qanwarsa ba
Ajiyar zuciya tayi tace “Nihla yayanki yana magana”
Cikin shagwaba tace “Momy Allah nina gaji”
Momy ta shafa gashin kanta tace “Nihla banason qiwa, maza tashi kije ki hada masa”
Daqyar tatashi tana bubbuga qafa tayi hanyar kitchen din tana gunguni “Allah ni nagaji…”
Yaja daga kwancen yagama qare mata kallo, ba qaramin birgeshi tayiba yanda take wannan shagwabar, shiyasa yace yarinta ce take damun yarinyar, kallan Momy yayi yace “Momy yanzu haka zakibar yarinyar nan tadinga yawo kanta Babu dankwali”
Momy tace “Abba kaima fa qanwar ka ce, kanada iko akanta, kayi mata magana mana”
Shiru yayi, besake magana ba, daga yin qorafi kuma sai ace shi yayi mata magana?
Nihla kuwa da niyya taqi futowa daga kitchen din dawuri, saida tagama Jan ajinta sannan tafuto da iya cup daya jal a hannunta, ko akan tire bata dora ba, takawo gabansa ta direshi batare datace komai ba, sannan takoma wajan Momy, Kallanta yayi yanda ta ajiye masa coffee din Babu ladabi aciki, aikuwa karaf idonsu yahadu dana juna, fuskar nan tasa ahade, lokaci daya kowa yadauke idonsa cikeda basarwa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau juma’ah, su ya Usman sun saba ko wacce juma’ah da an’idar da sallah gidan suke zuwa susha firarsu da yamma can saisu tafi
Yauma zaune suke afalo suna kallo amma hankalinsu baya kan kallon ma, kawai firar duniya sukeyi, koda yaushe Momy ta kallesu wani irin dadi takeji yanda Allah ya hade mata kan yaranta waje daya.
Bakinsa dauke da sallama yashigo falon, yau manyan kaya yasaka harda Babbar riga, kayan sunyi masa kyau sosai Kamar bashiba, kallo daya Nihla tayi masa ta dauke kanta, bata taba ganinsa cikin manyan kayan dasuka karbi jikinsa Kamar yau ba, koda yaushe saide qananun kaya, farouq ya kalleshi yace “saurayi mijin yanmata, baka gankaba Kamar sabon Ango”
Murmushi yayi, Wanda ya qarawa fuskarsa kyau sosai, qaraso wa cikin falon yayi, duk kujerun dake falon bai zauna akowacce ba, sai wadda Nihla take zaune dayake a 2seater take zaune
Yanda ya zauna akujerar dab da ita saika dauka matar sa ce, gabanta ne yafara luguden faduwa amma sai tayi fuska ta basar Kamar yanda yayi
Aliyu yace “farouq bakada damuwa, shiyasa ko d’an yayan ne da qanne suke fadawa yayunsu Abba baya fada ma, kacika tsokana wallahi”
Usman yadauki wayarsa Kamar yana dannawa amma saiya shige cikin camera ya cire flash din camerar yadauke su photo batareda kowa ya lura ba, pic din ya kalla sosai anan yaga tsantsar dacewar dasukayi, murmushi yayi yasaka wayarsa cikin aljihu yace “gaskiya farouq yafada, munada manya manyan biki a gabanmu nan gaba, Gana Abba Gana Nihla”
Sai a lokacin Abba yayi magana, “ya Usman biki kuma?”
Usman yace “emana, to tsayawa zamuyi muyita kallan ku”
Murmushi kawai yayi, baisan dalili ba haka nan yakejin dadin zamansu a kujera daya, jiyake Kamar suci gaba da kasancewa ahaka
Ruwan dake ajiye a table din gabansu yadauka ya tsiyaya a glass cup yanasha, hakanne yabawa Nihla damar matsawa gefe can qarshan kujerar, domin kuwa ba qaramin takura ta yayi ba
Wayartace tayi qara, Kamar hadin baki dagashi har ita suka kai dubansu kan wayar, yau ma cin karo yayi da irin sunan da yagani kwanaki Wato ❤my Yusif ❤
Wani irin haushi ne ya kamashi, Wanda shi kansa yarasa dalilin jin hakan,daga farouq har Usman da Aliyu Abba suka zubawa ido suna kallan yanayin sa
Nihla kuwa hamdala tayi cikin ranta, ta miqe zata shige daki domin amsa wayar, saida taje tsakiyar falon ta tsinci maganarsa Kamar almara “please kid’an kawomin lemo a kitchen”
Cak taja ta tsaya, ita batayi gaba ba, ita batayi baya ba, wallahi ranta yabaci, Dan me dukda datake zaune baice taje tadauko masa ba, saida yaga zata shiga daki ta amsa waya, tayi tunanin su ya Usman zasuce tarabu dashi taje tayi wayarta, amma saitaji shiru, tome suke nufi? Ita zasu hadewa kai subi bayan dan’uwansu? ????
Cikin taqaici tayi hanyar kitchen din,takawo masa lemon ta ajiye, Usman sai kallan fuskarta yake ko zaiga yanayin ta amma sai yaga fuskarta Babu yabo Babu fallasa, shi kokadan baiji haushin abinda Abban yayi ba, domin kuwa yagama gane dan’uwan nasa kishi yafara batare daya saniba, shikuma gaskiya bazaiso ace mace Kamar Nihla tasake kubce musu ba, musanman ma yanzu dakomai yaji ????
Bayan ta ajiye lemon ko kallansu batayi ba, tashige cikin dakinta, wayar ta wullar akan gadon tareda dafe kanta ????????♀️, me wannan mutumin yake nufi da ita ne?
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zaune suke suke afalon Diyana gaba dayansu, dukansu Kallanta suke tana basu labari, cikin damuwa taci gaba da cewa “idan na zauna afalo koda yaushe bashida wajan zama sai qarqashina, ga aiki, kullum saiya sakani aiki Dan masifa, narasa yaya zanyi, har gara wani lokacin Momy tana masa magana, amma wallahi rannan dasu ya Usman sukazo dukansu qyaleshi sukayi, kuma suna gani fa ankirani ne awaya “