DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Yau Tun safe tatashi da matsananciyar naquda, daqyar ta’iya kiran Aslam dayake wajan aiki, yana jin yanayin muryarta yasan ba kalau ba, haka yadawo gida suka tafi asbiti
Tayi doguwar naquda sai cikin dare ta haihu lafiya, tahaifi danta namiji Mai kamada ita sak
Tun asuba labari ya’isa family house cewa Ilham ta haihu, dasassafe kuwa asbitin yacika sosai da yan’uwa, Nihla kam tafi kowa murna, gata da ihlam haka suke zaune a dakin, sai wajan la’asar sannan suka dawo gida, amma Nihla sai dare tadawo agajiye, hajiya Na’ila bataga ta zamaba, tunda akai haihuwar tayi kane-kane akan komai, ko kara bata yiwa hajiya Abida ba, Wato Maman Ilham ????

Ita kuwa hajiya Abida abin ma bai wani dameta ba tunda ana kula da yarinyar ai shikkenan, ita dadi ma taji, tasan cewa hakan alama ce ta Ilham din tana zaune da sirikarta lafiya

Bayan kwana bakwai aka radawa yaro suna Abubakar Wato Abba, suna kiransa da lil Abba

Da yamma ta shirya tsaf cikin riga da siket na leshi, Mai launin dark blue da sirkin fari, qananun kalba ne akanta, da kanta ta tsara kwalliya taci daurin dankwali Mai kyau, ta tattare kalbar tata tadaureta abaya, wayarta ce take qara taqi dauka, su Dida ne suke kiranta Tun dazu, tasan kuma bazai wuce suce basu ganta ba

Saida ta shirya tsaf sannan tayafa mayafin ta Dan ma dedeci tafuto falo, hayaniyar su ya Usman take juyowa a dakin ya Abba, tace to wannan yaushe sukazo, gefenta ta kalla taga wata waya qirar iphone tayi Murmushi tadauka tace may be ta ya farouq ce, tana daukar wayar kai tsaye tatafi camera tadinga yin Selfie masu shegen kyau, sai Style take qarawa tana yin pictures din, saida tagama sannan ta ajiye wayar ta qwalawa Momy kira

Sai gata tafuto daga dakin ya Abba ita dasu ya Usman ashe ma tare suke, suna futowa farouq yace “kai kai kai, ina zakije haka Kamar Wanda zakije wajan gasar sarauniyar kyau?”

Murmushi tayi, tace “ya farouq gidan suna Zan tafi”

Ya Usman yace “gaskiya wannan wankan nawa ne”

Murmushi tayi batace komai ba, Aliyu kuwa baiyi mata magana ce kawai de yana murmushi cikin ransa yana yaba kyawun surar yarinyar

Shikuwa Gogan abakin kofar dakin nasa ya tsaya hannunsa zube cikin aljihun wandonsa, yana qare mata kallo Bece dasu komaiba, yatsani yaga tanayiwa mutane murmushi saboda yanda take yin mugun kyau, musanman ma yanda dimple dinta suke futowa
Fuskarsa adaure Babu alamun wasa yake kallanta, amma yakasa cewa uffan

Momy ta kalleta tace “masha Allah, yanmatan Momy kinyi kyau sosai, bari na gyara miki daurin dankwalin naki”

Nihla ta tsaya Momy kuwa ta qara gyara mata daurin, sannan tayi mata sallama tatafi

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Gidan suna yayi albarka sosai, Mazawaje family duk sunje, iyayenne mata kawai basujeba, saikuma ‘yan’uwan mahaifiyar ta suma duk sunje sosai, maijego tana shiga cikin kayaiyaki na alfarma itada Baby

Har dare yayi anata hidima sannan mutane suka Dan rarragu, duk wannan abun da ake jikin Dida asanyaye yake, sai bayan mutane sun watse ne da daddare Nihla take cewa “Dida meyake damunki ne Tun yamma kinyi shiru”

Tace “tunanin ya Fawaz nake, ina tsoron karyaqi shan ma ganinsa”

Diyana tace “Dida kina shagwaba ya Fawaz wallahi, koda yake soyaiya ce, rannan ma munyi waya da mum take cemin tabawa driver yakawo miki jakar ki tunda kintafi Babu sallama” ????

Murmushi tayi kawai

Ilham tace “kice anaji da yayan nawa, toki sakarwa dan’uwana jiki de yamore ehe”

Diyana tace “um, nikam danba qara, Tunna farko bansake yarda ba”

Nihla tace “waiku Dan Allah miye hakan, kawai saiku dinga yin wannan firar agabana, salon ku lalatani”

Dida tace “kwana nawane kema Nihla, ai Kamar yaune”

Diyana tace “ke gwauruwa waye zaizo yadauke ki ne? Kingani ya Adam zaizo, kuma Dida ma nasan ya Fawaz zaizo”

Tace “nikam driver, dama shiya kawoni”

Itama Diyanan tace “wai kina nufin ya Abba ba zaizo yadauke ki ba?”

“ya Abba fa kikace, ashe kuwa saide na kwana anan, keni fa ko magana bamayi, kowa harkarsa yake agidan nan infada miki”

Ilham tace “haba Nihla, ya Abban kine fa, kudena Dan Allah”

Itade Nihla shiru tayi tanajin su suna zancen su ta qyalesu, taga alama Ilham ta Manta cin mutuncin dayayi mata

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Fira suke sunata kwasar daria amma shi yana zaune akujera shi kadai ya zubawa wayarsa ido, farouq Tun dazu ya lura kwata-kwata hankalin Abba yanakan wayarsa, ko kallansu Babu kawai ya qurawa waya ido

Ahankali yatashi yayi kitchen Kamar gaske ????
Soyake yaga menene yadauke hankalinsa haka, daya dauko Ruwan da niyya yazo wucewa ta bayan Abba,karaf idonsa yasauka akan screen din wayar Abba, pictures din Nihla ne, kuma da kayan data fita dashi dazu da yamma ne, toya akai Abba yasamu pictures din? Yaushe yayi mata? Dama sun fara shiri shida itane harya fara yimata photo awaya?
Ganin Babu me bashi amsa yasa ya tsaya yana kallan Abba dayake kallan pictures din daya baya daya, idan yashiga cikin guda daya saiya dade yana kalla sannan zai sake zubawa nagaba ido

Momy data lura shurun nasa yayi yawa tace “Abba na lafiya de ko?”

Kafin Abba yayi magana farouq dayake bayansa a tsaye yace “lafiya Momy, yana ganin abinda yake rayuwa tare dashi ne acikin gidan”

Cikin sauri ya juya ya kalli farouq, Dasauri yasaka wayar aduhu, sannan yasakata cikin aljihun wandon jeans dinsa, Innalillah… Baiso farouq ya kamashi yana kallan pictures din yarinyar nanba, kada yayi tunanin wani abu, ahankali yamiqe tsaye yace “Babu komai Momy”

Farouq ya kwashe da daria ganin yanda qanin nasa yayi fuska Kamar bashi ba, yace “idan tayi tsami maji”

Momy kam bata gane komai ba, danhaka tashare su, haka sukaci gaba da firarsu sannan sukai mata sallama kowa yatafi gidansa

Shima Abba compound din gidan yafuto, Momy kuwa daki tashige tana waya da Daddy akan matsalar Abba da likita yafada mata, yace ta bari idan yadawo gida saisu yi masa magana

Yadade a compound din yana kallan get din gidan, Agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla kasancewar akwai yalwar hasken fitilu agidan yaga goma saura, zagaye yafarayi awajan hannunsa daya yana cikin aljihunsa, har zuwa wani lokaci kuma Yaqi komawa cikin part din nasu, Agogon yasake kalla afili yace

“why bata dawoba har yanzu?”

Gashinan anyi dayawa, dafatan zanga Comments, facebook readers ina godia sosai da sosai ????

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/5, 12:37 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

37&38

Babu me bashi amsa, haka yadinga zagaye wajan har saida ya hango maigadi yana bude get alamun itace suka dawo, sannan ya juya cikin sauri ya koma ciki

Ita kuwa Nihla bata lura dashi bama, ana sauke ta tashigo part din nasu, kai tsaye dakin Momy taje ta sanar da’ita dawowar ta sannan tatafi dakinta tayi wanka, tafara shirin bacci

Har shigowar ta falon yanajinta, sai a lokacin ya kashe wutar dakinsa shima ya kwanta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“Doctor magunguna na sun qare inaso kahada min wasu” cewar Fawaz

Doc yadubeshi yace “to Alhamdulillah gaskiya naga ana samun cigaba”

“hakane kam, but wani lokacin inajin raina yana baci haka kawai, kuma cikin raina inajin inason nasha qwayar ko kadanne”

Murmushi Doc yayi “hakane, dama dole zakaji haka, amma kaci gaba da hakuri, kana kai zuciyarka insha Allah zuwa nan gaba kadan zakaji tafita daga ranka ma gaba daya”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button