DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Yadaga mata kai, daga nan tafice daga dakin

Momy tace “meyake damun kane Abba na, naga lafiya kafita”

Ahankali yace “Momy kaina ke ciwo”

Tace “to Allah yasawaqe, bari ajima idan bakaji sauqi ba sai akira Doc”
Bece da ita komai, domin kuwa abinda yakeji yafi ciwon kan yawa, Inda ace ciwon kai ne Toda sauqi ????

Momy na fita Aslam yace “Abokina meyake faruwa ne? Meke damunka?”

Cikin damuwa yace “Aslam kayi Gaskiya, kafini gaskiya Aslam, ina sonta, Nikaina yanzu na tabbatar ina sonta” ya qarasa maganar tareda fashewa da kuka

Gaban Aslam yafadi, bade maganar datake ransa hakace take shirin kasancewa ba, kallan Abba yayi yace “Wacece?”

Kai tsaye yace “Nihla”

Aslam yayi shiru Tsawon second talatin,zaka dade kafin kaga Abba yana kuka Kamar haka, yasan cewa tabbas tunda haka ta faru toba qaramin so yakewa yarinyar ba, haka yasa hannu yayi tagumi hannu bibbiyu,
gaskiya Abba yadauko musu Babban aiki, kallansa yayi yace

“Gaskiya Abba akwai damuwa,ka janyo mana Babban aiki a gabanmu, maganar gaskiya itace kana ruwa tsundum kusada kada”

Cikin masifa Kamar bame kukaba yace “Dan Allah Aslam idan bazaka bani goyon bayaba to kamin shiru kawai, meyasa bazaka fahimci abinda nakeji bane?”

Cikin damuwa shima Aslam din yace “Abba aini nafi kowa fahimtar ka” ????

“dan Allah Aslam tashi kafita kabarni da abinda nakeji” yasa hannu ya goge hawayen idonsa

Sharhi please

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/5, 10:18 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

39&40

Aslam yatashi yafuto daga dakin jikinsa a sanyaye, domin kuwa yasan abokin nasa yana cikin damuwa yanzu, maganar aikin data kawoshi ma baiyi ba.

Fitar Aslam keda wuya Abba ya danna kansa cikin fillo yana hawaye, to Aslam ma dayake makusancin abokinsa yakasa fahimtarsa inaga sauran jama’ar gida? ????

Har dare yayi sosai Abba bai sake futowa daga dakinsa ba, saide Momy tana zuwa tana dubashi akai akai

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Karfe goma na safe ma agida tayi mata, babu part din da batajeba cikin family house din nasu, tana zuwa part dinsu Nihla taji shiru Kamar Babu kowa, kai tsaye dakin Nihla tashiga taganta kwance tana bacci fillo rungume a qirjinta

Batare data tasheta ba, ta’ajiye mata lil Abba agefenta, yaron kuwa idonsa akan fan din dakin dake juyawa Ahankali

Fita tayi daga dakin tashiga kitchen din tanaso ta hadawa kanta Tea Dan taga Momy da Nihla harkar gayu suke ji ita kuwa tana goyon yaro bazata iya wannan zaman ba

Cikin baccinta taji yaron yana wasa, bude idonta tayi ta kalleshi, shi kadai, sai tsotsar hannu yake, murmushi tayi tatashi zaune tareda daukar sa tace “Wato mamanka tazo shine ta ajiye min kai tagudu danka tashen a bacci”

Kissing dinsa tayi, suka futo falo, anan taga taga Ilham zaune tana shan Tea da uban Bread a gabanta, Momy tana zaune da alama itama yanzu tatashi

Qarasowa tayi ta ajiye yaron tace “ashe kinzo, yau kece agida kenan”

Kafin Ilham tace wani abu momy tace “nima yanzu na futo naganta”

Ilham tace “Momy Tun dazu ya Aslam ya kawomu yawuce wajan aiki, ina zuwa wajan umma nace ko Abincin ta ba zanci ba wajan Nihla Zan tafi, shine na tarar da ita tana bacci, nabar mata Yayanta a dakin na futo”

Momy tace “Ah kin kyauta wallahi, gashinan ya warware,”

Daukansa Momy tayi tace “Abba nah, mekakeci ne?”

Daga nan tayi cikin dakinta dashi tabarsu anan suna fira

Har yamma Ilham tana wajan Nihla suna ta firarsu, yaron ta kuwa yana hannun Momy saide idan yayi kuka takawo mata shi, yanzu ma nono tagama bashi Nihla ta karbe shi tana masa wasa, sai dariya yake

Tace “Ilham wannan yaron Kamar ku sai sake futowa yake”
Miqewa tsaye tayi tadauki towel dinsa ta goyashi taci gaba da magana “gashi sai dariya yake gwanin sha’awa wallahi ba Kamar me sunansa ba, kullum fuska adaure ko murmushi Babu” ????

Karaf maganar ta sauka a Kunnan Abba daya shigo cikin falon yanzu, Tun safe yaje company sai yanzu yadawo, Wato shine kullum fuska adaure, Ilham de taga shigowarsa, danhaka sai tayi shiru ????
Ita kuwa Nihla data bawa kofa baya ko’ajikinta, taga de Ilham din tayi mata shiru kawai kuma sai qifta mata ido take ????, amma bata gane komai ba, yaron taci gaba da jijjigawa a bayanta ko zaiyi bacci, amma memakon bacci ma saiya fara kuka

Ahankali ya qaraso cikin falon, cikin ladabi Ilham tace “ya Abba sannu da zuwa”

Saida yadan saki fuskarsa sannan yace “yawwa, ya Baby”

Tace “gashinan Alhamdulillah”

Shiru Nihla tayi, kode yaji maganar data fada ne, shiyasa Ilham take qifta mata idanu? ????

Abba kuwa bai sake cewa komai ba yanufi Nihla fuskarsa adaure ko alamun wasa Babu, muryar sa yarage cikin fada yace “bani yaron nan, saboda rashin hankali kina goyo”

Mamaki yakama Nihla, menene abin rashin hankali a goyo? Batare data ce masa komai ba tafara kokarin kunce yaron, saura kadan yaron ya qwace daga hannunta garin sauko dashi, aikuwa yakama gaban rigarta ya riqe, karon farko da kunya takama Nihla ganin ga ya Abba a tsaye, Sannan wannan yaro yakama riga yariqe har hakan yasa ana hango albarkatun qirjinta

Batayi auneba taji ya Abba yasaka hannunsa awajan ya cire hannun yaron, sannan ya juya zai tafi dashi

Ilham tana zaune tazama yar kallo, duk abinda ake akan idonta, saide bataji abinda ya Abba ya cewa Nihla ba, tayi Murmushi tace “lalle Nihla kin iya goyo, kema da yanzu danaki Babyn”

Abba yana kokarin shiga dakinsa yaji wannan maganar ta Ilham, Wato da ace anyi musu aure a wancan lokacin da yanzu itama da nata yaron, ko juyowa beyiba yashige cikin dakinsa

Nihla kuwa tana qame a tsaye, Ilham tace “kitaho ki zauna mana, kin daskare a tsaye, shiyasa nake ta qyafta miki ido, amma inaaaa gulma ta rufe miki ido bakisan yashigo ba sai zuba kike” ????

Nihla ta kalleta “niba wannan ne yasa na tsaya ba, bakiga abinda d’anki yamin bane?” tayi qwafa tadawo tazauna akujerar tana kumburi

Ilham tayi dariya tace “nagani mana, jiyake rigar mamansa yariqe, besan takwaransa ya budewa abubuwa yana ganiba” ????

“kuma basai ya tsaya nacire yaron nabashi ba, amma haka kawai saiya wani sakamin hannu a qirji”

Dariya Ilham tayi “kiyi hakuri, ganide ba tabawa bane, kuma gani yayi zaki yarda takwaransa, shiyasa yakawo muku temakon gaggawa” ????

Nihla tayi shiru batace komai ba, al’amarin Abba kullum qara tsamari yake, da yana zama agefenta yanzu kuma yafara kawo mata hannu, nan gaba kuma ai batasan mezai faruba

Ilham tace “wai Dan Allah meyake cemiki ne naji yayi qasa da murya yana magana”

“cemin yayi nabashi yaron, saboda rashin hankali ina goyo, menene abin rashin hankali agoyo”

Ilham tace “eto da gaskiyarsa, may be bayaso abubuwan sa suzube ne”

“mekike nufi Ilham?”

“Nihla kinsan goyo yanasa nonon wasu matan yazube, inaga shiyasa, inba hakaba ai bazai ce kina goyo ba”

Nihla tadafe kanta ????‍♀️ tace “Innalillahi…. Wallahi gayen nan yagama dani gaba daya”

Ilham tace “kema ai kinga ma dashi, Dan wallahi nide abinda na fahimta ko, ya Abba sonki yake, kigafa yanda yawani matsa gab dake Kamar zaisaku ajikinsa keda Babyn kawai saboda zai karbe shi, Nihla kiyi tunani mana”

“Ilham kenan, babu wata soyaiya, rannan ma sallama ya mana nida Momy yace yatafi zance”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button